Home Siyasa Atiku ya musanta labarin ya bar siyasa

Atiku ya musanta labarin ya bar siyasa

2
0

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da ke yawo cewa ya yanke shawarar janyewa daga harkokin siyasa.

Jaridar Daily ta ambato ofishin Atiku na Abuja, na zargin hannun gwamnatin Nijeriya a kirkirar labarin.

Ya ce, duk wani labari game da taron da ya yi da masu ruwa da tsaki na ADC, inda ake zargin ya yanke shawarar yin ritaya, ƙarya ce kawai kuma an tsara ta ne don ruɗani da ɓata ƙoƙarinsa na siyasa a kasar.

Atiku ya jaddada cewa irin wannan shawara za a sanar da ita ne ta ofishinsa kawai ba ta hanyoyin jita-jita ko kafafen sada zumunta ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here