An tura kudi asusun banki na Atiku Abubakar – Zargin madugun adawar Nijeriya
Dan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwa kan wasu kuɗaɗe da aka tura zuwa ɗaya daga cikin asusunsa na sirri ba tare da saninsa ko amincewarsa ba, yana mai zargin cewa an samu kutsen bayanan sirrin asusun bankinsa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta bayyana cewa wani mutum da Atiku bai sani ba ne ya tura kuɗin zuwa asusun, tare da rubuta bayanin “Contribution Electioneering Campaign” a matsayin dalilin tura kuɗin.
Jaridar Punch ta ruwato cewa Atiku ya ce shi da kwamitin yaƙin neman zaɓensa ba su taɓa neman wannan gudummawa ba, ba su ba da izini ba, kuma ba su san wanda ya tura kuɗin ba.




