Arzikin Tinubu Ya Kai $4Bn? Sai Dai Ya Ki Bayyanawa Duniya

Kungiyoyin CSO sun ce har yanzu ba wanda ya san dukiyar da Tinubu ya mallaka kuma hukumar da'ar ma'aikata ta yi gum da bakinta kan hakan. 

Arzikin Tinubu Ya Kai $4Bn? Sai Dai Ya Ki Bayyanawa Duniya

Masu ruwa da tsaki daga kungiyoyin ma'aikatan gwamnati (CSO), sun yi nuni da cewa bayyana dukiyar da ya mallaka wani nauyi ne da ya rataya kan Shugaba Bola Tinubu. 

Kungiyoyin CSO sun ce har yanzu ba wanda ya san dukiyar da Tinubu ya mallaka kuma hukumar da'ar ma'aikata ta yi gum da bakinta kan hakan. 
Jaridar Legit ta fahimci cewa marigayi Umaru Musa Yar'Adua da Muhammadu Buhari ne kawai suka sanar da dukiyar da suka mallaka. 
Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan sun ki bin wannan doka ta sanar da dukiyar da suka mallaka har suka sauka daga mulki. 
Yar'Adua ya bayyana cewa dukiyarsa ta kai Naira biliyan 856 da miliyan 452 da dubu dari 892, inda ya ke samun akalla Naira miliyan 18.7 duk shekara. Ya kuma bayyana cewa matarsa, Turai, na da dukiyar da ta kai darajar Naira miliyan 19, da suka hada da gidaje.
A shekarar 2015, tsohon shugaban kasa Buhari ya sanar da cewa ya mallaki dukiyar da ta kai darajar Naira miliyan 30, kuma suna a asusun bankinsa.