APC tana alfahari da kokarin Hon. Bamalum a karamar hukumar Bade - in ji Bukardima Lawan

APC tana alfahari da kokarin Hon. Bamalum a karamar hukumar Bade - in ji Bukardima Lawan

Daga Muhammad Maitela, Damaturu. 

Shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Bade, Hon. Bukardima Lawan, ya ce jam'iyyar ta na alfahari da kwazon tallafa wa masu karamin karfi da matashin dan siyasa kuma Mashawarci na Musamman ga Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, Hon. Isa Bamalum Bashir. 

Shugaban ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da tallafin atamfofi ga mata masu karamin karfi, wanda Hon. Isa Bamalum Bashir ya bayar a Makaranar Sakandiren Jeka-ka-dawo dake Gashu'a a jihar Yobe, ranar Jummu'a. 

Ya ce lokuta da dama Hon. Bashir ya na aiwatar tallafin ga mata musulmi da Kiristoci, a matsayin nashi gudummawa wajen taimakon al'umma.

"A daidai lokacin da muke shiri da yardar Allah zamu fita zaben Gwamna Mai Mala Buni karo na biyu, tare da yan majalisunmu, inda zamu tabbatar jama'a sun bayar da hadin kai don kai mu samu nasara."

Ya ce, "Ba wannan ne karon farko wanda Hon. Bamalum, yake gayyatar al'umma mu shaidi raba wa mata atamfofi, har da yan uwanmu Kiristoci."

"Kuma a iya sanina, wannan matashin raba atamfofi sama da 977 ga mata masu karamin karfi. Wanda a matsayin mu na shugabanin jam'iyyar APC, mun yaba kuma mun gamsu da wannan hidima da yake wa al'umma a karamar hukumar Bade da jihar Yobe baki daya." 

"Gwamna Buni irin wadannan ayyukan ne yake bukata sauran yan siyasa su kwaikwaya, kuma wannan sune matasan da yake jindadin kasancewa kusa dashi masu kwazo da burin ci gaba. Mun yaba masa sosai a matsayin sa na matashi, mai kishin al'ummarsa, Allah ya saka da alheri."

A nashi bangaren, Hon. Isa Bamalum ya bayyana godiya da goyon bayan da yake samu daga Gwamna Mai Mala Buni, inda ya ce kowane lokaci ya na umurtar su wajen yin ayyukan alheri da kyautata wa al'umma. 

"Sannan na kebanci wannan tallafin ga iyayenmu mata ne bisa la'akari da nayi, mafi yawan lokuta dasu ake gwagwarmaya a siyasa amma ba a faye kulasu ba, sannan da irin yadda sune suka fi shan wahalhalu kuma ba a cika tunawa dasu ba." 

"Sannan kuma mun raba turamen atamfofi 623 a baya, jiya kuma mun rabawa yan uwanmu Kiristoci 70 yau kuma 100 sannan yau za mu raba katin wasu atamfofi 100 ko sama da hakan, in Sha Allah." In ji shi.