APC ta yadda da cewa manufofin Tinubu sun ƙara jefa talaka a mawuyacin hali
Jam'iyyar APC mai mulki, ta amince cewa manufofin shugaban kasa Tinubu ne suka haifar da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa a kasar nan.
Sakataren yada labaran jam'iyyar na kasa, Barrister Felix Morka, ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya fitar inda yake mayar da martani ga tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar na yankin Arewa maso yamma, Salihu Mohammed Lukman.
Lukman, ya soki gwamnatin APC wajen gazawa ga 'yan Nijeriya, inda ya kara da cewa tsohon shugaban kasa Buhari da kuma shugaban kasa Tinubu sun gaza wajen cika alkawarin da suka dauka.
Sai dai a martanin da ya mayar, Morka cikin wata sanarwa a ranar Talata ya ce shugaba Tinubu na daukar matakai masu tsauri ne don hana kasar nan fadawa karayar tattalin arziki inda ya kara da cewa matakan sun haifar da matsin rayuwa.
"Ba makawa, wadannan matakan sun haifar da karin matsin tattalin arziki ga al'ummar mu", inji sanarwar.