Barista Sa'adatu Yanusa Muhammad tana neman jam'iyar APC ta tsayar da ita 'yar majalisar tarayya da za ta wakilci ƙananan hukumomin Dange Shuni da Tureta da Bodinga a majalisar tarayyar Nijeriya sai dai jam'iyar ta murƙushe 'yar takarar.
Barista tana da ƙarfi da damar lashe zaɓen, ganin haka ya sanya aka sauya waƙillai na gaskiya da za su yi zaɓen, abin da ya haifar da tsaiko a wurin gudanar da zaɓen.
Kamilu Umar Tureta daya daga cikin delegate a mazabarta ya ce zaɓarsa aka yi bisa ga amincewar mambobin jam'iyar ya cika duk wani sharaɗin da ake buƙata, har ya samu nasara sunansa na wurin uwar jam'iya.
"an kawo wasu da ake son a sauya mu da su wanda su ɗin ba waƙillai ba ne ana son kawai su yi zaɓe, sojojin haya in an sanya su an yi wa jam'iya hasarar kujerar," a cewar Kamilu.
Ya ce 'yan takara biyar ne don haka a basu damar su zaɓi wanda suke ra'ayi don yi wa ƙasa da jama'a aiki.
Hauwa'u Abubakar daya daga cikin daligate ta ce jigon jam'iyarsu a mazabarsu ta Dingyadi Badawa ne ya saka ta a cikin wakillan ba ta san yanda aka yi ba, amma za ta zabi wanda take ra'ayi.
Namiji da aka baiwa sunan mace a matsayin delegate ya ce ya sanya matarsa a madadinsa bayan da ya fahimci bai kamata a kira suanan macen ya karba ba.
Ya ce sanya shi kawai aka yi ba tare da yasan yanda abin yake ba.
Barista Sa'adat ta ce ta samu bayanin akwai korafe-korafe kan wakillan musamman sauya su da aka yi wanda hakan ya sabawa dokar jam'iyar APC, "bai kamata a yi zaben a haka ba don haka zamu yi abin da yakamata domin tsare hakkin jama'a da jam'iyya," a cewar Barista Yanusa.
Ta yi alwashin kwatowa mutane hakkinsu da ake kokarin hana su saboda son rai da kokarin kakaba dan takara da jama'a ba su ra'ayinsa.
Barista ta kauracewa zaben domin ba ta gamsu da shiga duk wani lamari da ya sabawa doka ba.
Yunkurin jin ta bakin jami'in kula da zaben ya citura.