APC Ta Kori Tsohon Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Kebbi     

APC Ta Kori Tsohon Shugaban Karamar Hukuma A Jihar Kebbi     
       

Daga Abbakar Aleeyu Anache

Jam'iyyar APC ta mazabar Ribah Machka a karamar hukumar Ribah ta jihar Kebbi ta kori Engr. Sale Danyaro Ribah daga Jam'iyyar bisa zargin yiwa jam'iyyar zagon kasa. 

Shugabannin Jam'iyyar APC na mazabar Ribah Machka wadanda suka sanar da korar  Sale Danyaro daga APC ga manema labarai a Kebbi sun bayyana korarsa daga Jam'iyya  hukuncin ya fara aiki ne daga 8/12/2022 ba bata lokaci.
Sun bayyana cewa 25 daga cikin 27 na shugabannin jam'iyyar APC a mazabar sun amince da korar tsohon shugaban karamar hukumar Ribah bisa aikata laifuka daban-daban da zagon kasa ga jam'iyyar. 
A cewar APC a mazabar Ribah Machka ta kori  Danyaro wanda jigo ne na jam'iyyar a Danko Wasagu kan ayyukan  zagon kasa ga jam'iya.