APC Ta Dage Babban Taronta Ta Sanya  Taron Zabar Shugabannin Yanki

APC Ta Dage Babban Taronta Ta Sanya  Taron Zabar Shugabannin Yanki

 

Jam'iya mai mulkin Nijeriya APC ta daga babban taronta da ta shirya gudanarwa  a ranar 26 ga Fabarairu 2022.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata takarda da shugabannin rikon jam'iyar suka aikawa hukumar zabe ta kasa.

Shugabannin sun ce  za su gudanar da zaben shugabannin yanki a 26 ga Maris,  babban taron kasa kuwa ba a sanar da rana ba.
Takardar wadda Shugaban riko na jam'iyar Gwamnan Yobe Mai Mala Buni da sakatarensa John James suka sanyawa  hannu sun bayyana dage babban taron sun yi hakan ne bisa dokar zabe ta 2010 wadda aka yi wa gyaran fuska.
A tsarin za a fara sayar da Fom na takara  a 2 zuwa 5 ga watan Maris sai zabe ya kasance 26 ga watan maris na 2022.