APC Ta Bayyana Dalilin Rashin Fitar Da Tsarin Shugabancin Majalisa Ta 10 

APC Ta Bayyana Dalilin Rashin Fitar Da Tsarin Shugabancin Majalisa Ta 10 

 

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Adamu ya bayyana dalilin da ya sanya har yanzu, jam'iyyar ba ta fitar da tsarin shugabancin majalisa ta 10 ba. 

Shugban jam'iyyar ya ce jam'iyyar ta kasa yin taro domin fitar da muƙaman, saboda zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, baya nan, cewar rahoton The Cable. 
Da ya ke magana da ƴan jarida ranar Laraba a birnin tarayya Abuja, jim kaɗan bayan taron kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam'iyyar (NWC), Adamu ya ce jam'iyyar a shirye ta ke ta tafi da kowa wajen yanke hukuncin ta. 
"Lokacin da za mu fitar da tsarin yankunan da shugabannin majalisar za su fito, ba mu kaɗai za mu yi ba. 
Tsarin za a yi shi ne tare da wanda yake da iko a ƙasar nan, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Sanata Bola Tinubu." 
"Mu na so ayi tare da shi, ya yi tafiya zuwa ƙasar waje bayan zaɓe, sannan duka satin da ya wuce ya dawo. Sai yana nan yakamata mu fitar da tsarin."
 Da ya ke magana a wajen, kakakin jam'iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce jam'iyyar ba sauri ta ke ba ta fitar da tsarin shugabancin majalisar, rahoton New Telegraph.