APC ta ƙaddamar da Kashim Shettima a matsayin mataimakin takarar Tinubu

APC ta ƙaddamar da Kashim Shettima a matsayin mataimakin takarar Tinubu

Jam’iyyar APC, ta bayyana tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima a matsayin dan takararta na mataimakin shugaban kasa a 2023.

An ƙaddamar da Shettima ne a wani taron da aka yi a Abuja a yau Laraba.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya zabi Shettima a matsayin abokin takararsa biyo bayan fitowar sa a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
 
Zaben Shettima na Tinubu ya ci gaba da haifar da cece-kuce a fadin Najeriya.
 
Galibin ‘yan Najeriya sun so dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya zabi Kirista a matsayin abokin takararsa, amma sai ya zauna da Musulmin Arewa.

Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamarwar, Shettima ya ce zaɓar Musulmi da Musulmi a matsayin ƴan takarar shugabancin ƙasa ba laifi bane saboda Nijeriya ƙasa ce ta al'umma ɗaya, duk da bambancin yare da addinai.

Ya ƙara da cewa a matsayin sa na mataimakin takara, zai yi iya ƙoƙarin sa don ganin a shawo kan matsalolin da ke damun ƙasar nan.