APC Na Gab Da Rasa Sanata da 'yan majalisar tarayya biyu a Sakkwato

 APC Na Gab Da Rasa Sanata da 'yan majalisar tarayya biyu a Sakkwato

 

Jam'iya mai mulki a jihar Sakkwato APC ta soma samun rashin jituwa tsakaninta da wasu mambobin ta in da ake zargin Sanata Ibrahim Lamido ya samu rashin fahimta a tsakaninsa da jam'iyar tasa a matakin jiha.

Jita-jitar ta yawaita a jihar Sakkwato cewa Sanatan zai sauya jam'iyar zuwa PDP tare da magoya bayansa gabanin zaɓen 2027, APC da PDP da Sanata Lamiɗo ba wanda ya ce komai kan jita-jitar da ake yaɗawa.
A ranar Jumu'a ne data gabata aka ɗaura auren Sanata Lamiɗo a masallacin Jumu'a na Sarkin Musulmi Maccido in da jagororin jam'iyar PDP a jiha suka halarta, a gefe ɗaya jagororin APC ba wanda ya taka ƙafarsa a wurin.
'Yan majalisar wakilai guda biyu na APC  Alhaji Sani Yakubu da Bello Isa Ambarura sun halarci wurin in da ake ganin zuwan su don alaƙalar su da Sanata ne ba don APC ba.
Masu nazari na ganin rashin halartar jagororin APC a ɗaurin auren yana nuna a fili akwai tsamin dangantaka tsakanin ɓangarorin biyu.
Managarciya ta yi yunkurin samun Sanata Lamido da jam'yar APC don samun karin bayani kan dambarwar sai dai lamarin ya ci tura.