APC A Zamfara Ta Zargi Mataimakin Gwamna Da Karɓar Belin 'Yan China Dake Tare Da Mahara

APC A Zamfara Ta Zargi Mataimakin Gwamna Da Karɓar Belin 'Yan China Dake Tare Da Mahara

Daga Hussaini Ibrahim,Gusau.

Jamiyyar APC a Jihar Zamfara,na Zargin Mataimakin gwamnan Jihar Zamfara, Barista Mahadi Aliyu Gusau da amsar Belin "Yan Kasar Chaina masu hakar Ma'adanai da ake a zargin suna da alaka da "Yan Bindiga a Zamfara.

Sakataren yada Labarai na Jamiyyar APC na Jihar Zamfara, Yusuf Idiris Guaau,ne ya bayyana haka alokacin da ya ke tattaunawa da manaima labarai a Hedikwatar ofishin da ke Gusau.

Yusuf Idiris ya bayyana cewa, Jamiyyar PDP ta kalubalanci gwamnatin Jihar Zamfara, karkashin jagorancin gwamna Matawalle akan matsalar tsaro,bayan Mataimakin gwamna Barista Mahadi Aliyu Gusau ne ya amshi belin 'yan Kasar Chaina wadanda aka kama suna harkar Ma'adanai kum ake zargin suna tare da "Yan Bindiga da ke kashe mutane da garkuwa da su.inji Yusuf Idiris Guaau.

" Yusuf Idiris Gusau ya kara da cewa, Shugaban Kasa Muhammad Buhari ne ya haramta hakar Ma'adanai a fadin Jihar ta Zamfara ,sai gashi an kama wadannan mutane suna hakar Ma'adanai sabo da Mahaifin Mataimakin gwamnan Janar Ali Gusau shike da kashi saba'in na guraran hakar Ma'adanai da ake a Zamfara .

Kalubalantar gwamna Matawalle akan tsaro da Jamiyyar PDP keyi wa gwamna Matawalle kaikai ne zai koma kan mashekiya inji Sakataren yada Labaran.

Jam'iyyar APC ta kuma Zargin Mataimakin gwamnan Barista Mahadi Aliyu da kwashe sama da Naira biliyan dari shida daga ciki asusun kudin Gwamnati.shima Mataimakin Shugaban Jam'iyyar PDP na jihar ,Furofesa Kabir Jabaka akan kwashe kudin naira miliyan dari uku da hamsin na hukumar zaka da wakafi a loakacin da ya ke Shugabantar hukumar.

Yusuf Idiris Guaau, ya Kuma tabbatar da cewa, gwamna Matawalle na iyaka kokarin sa na ganin samun nasara tsaro da cigaban Jihar,duk da zagon kasa da 'yan jamiyyar PDP ke masa.