APC a jihar Zamfara ta fada Cikin rudani
Jam’iya mai adawa a jihar Zamfara APC ta fada cikin rudanin rashin tabbas kan yanda tafiyar jam’iyar zai kasance in da mambobi da shugabanin suka fada cikin rikicin shugabanci da rashin makama tsawon sati biyu kenan ana cikin wannan dambarwar.
Rikicin ya fara ne a ranar Assabar data gabata in da shugabannin APC a mazabar Galadima cikin karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara suka bayyana korar shugaban jam'iya na jiha Alhaji Tukur Danfulnani saboda rashin kwarewa a shugabancin jam'iya da yake yi.
A hirar shugabannin ga manema labarai a Gusau sun ce sun yanke hukuncin ne domin a ceto jam'iya ga bakin mulkin Danfulani.
Mataimakin shugaba a mazabar da shugaban jam'iya ya fito Alhaji Garba Bello ya ce madadin shugabanni 16 daga cikin 27 sun sanya hannu tare da amincewar korar Tukur Danfulani a cikin jam'iyar su.
A cewar Alhaji Garba kashi 90 na shugabannin jam'iya ba su tare Danfulani hakan ya sa jam'iyar rabuwa gida biyu, ya yi kira ga uwar jam'iyyar ta kasa ta samar da shugabannin rikon kwarya a jihar.
Bayan wanan matsayar sakataren yada labarai na APC a jiha Yusuf Idris ya fitar da takarda ga manema labarai cewa maganar korar shugaban ba gaskiya ba ne wasu ne dake kiran kansu shugabannin mazabar Danfulani suka kitsa lamarin ba za su yi nasara ba mutane kar su kula shirmensu.
Ya ce jam'iyar su na sane da 'yan siyasar da ke kokarin kawo hatsaniya a jam'iyar a shirin su na kafa sabuwar jam'iyya don zaben 2027, hakan suka yi a Kano da wasu jihohi mummunar manufarsu ba za ta yi nasara ba.
Sakataren ya ce in wasu mambobin jam'iyar nada matsala da shugaba akwai hanyoyin da ake bi don warware komai a tsanake ba tare da rigima.
Kwana ɗaya da haka shugabanni takwas daga cikin 16 da suka kori shugaban suka zo hidikwatar jam'iya cewa sun janye sa hannun da suka yi kan cire Danfulani domin yaudarar su aka yi, su sun gamsu da mulkin shugaban jam'iya Danfulani.
Sakataren jam'iya Ibrahim Umar Dangaladima da ya karbi takardar goyon bayan da suka kawo ya ce wadanda ke son cire shugaban basu bi ka'ida ba, jam'iya nada dokokinta.
Ana cikin wannan dambarwar ranar Juma'a data gabata APC a matakin jiha ta bayar da sanarwar dakatar da dan majalisar tarayya da yake wakiltar kananan hukumomin Birnin Magaji da Kauran Namoda Honarabul Aminu Sani Jaji daga jam'iyar domin samun shi da yiwa APC zagon kasa da raba ta gida biyu da sanya 'ya'yan jam'iya ba su aminta da juna ba.
Sakataren yada labarai na APC Yusuf Idris ya karanta dakatarwa bayan shugabannin jam'iya sun karbi takardar koke da katarwar daga mazabar dan Majalisar.
A yayin wata zantawa ta wayar tarho da ɗaya daga cikin makusatan ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Ƙauran Namoda da Birnin Magaji, Hon. Aminu Sani Jaji, Hon. Abdulmunafi Usman, ya bayyana shugaban jam'iyyar APC na jihar Zamfara Tukur Umar Ɗanfulani a matsayin tsintacciyar mage wadda ba ta mage.
Hon. Abdulmunafi Usman yana magana ne dangane da korar da wasu ke yaɗawa cewa an yi wa mai gidansu Hon. Aminu Sani Jaji daga jam'iyyar APC, ya ƙara da cewar korarren shugaban jam'iyya ba zai iya jagorantar korar wani ɗan jam'iyyar ba.
Ya ƙara da cewar wasu tsiraru ne kawai marasa aikin yi da ke neman na tuwo aka yi amfani da su domin su ɓata wa mai gidan nasu suna.
Rudanin da jam'iyar ta shiga ne ake ta dakatar da muhimman mutane a cikinta abin da ake ganin duk jagororin jam'iya a jiha ba su dauki mataki lamarin zai wargaza APC a jihar duk da ana zargin yaran tsohon Gwamna Ahmad Yarima ne dana tsohon Gwamna Bello Matawalle ke rigimar neman shugabancin jam'iya a jiha.
managarciya