Annobar Korona Ta Kashe Ma'aikatan Lafiya Sama Da Dubu 100 Cikin Watanni 18

Annobar Korona Ta Kashe Ma'aikatan Lafiya Sama Da Dubu 100 Cikin Watanni 18

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

Hukumar lafiya ta duniya tace akalla jami'an kula da lafiya 115,500 suka mutu sakamakon harbuwa da cutar korona a cikin watanni 18, da suka gabata,

Wata sanarwar hadin gwuiwa da hukumar ta gabatar tare da kungiyar kwadago ta duniya ta bayyana cewa ma'aikatan lafiya na bukatar wuraren ayyukan yi dake da tsafta, wanda zai kare su daga fuskantar duk wani hadari, 

Daraktan dake kula da lafiyar wuraren aiki da kuma sauyin yanayi a hukumar lafiya, Maria Neira ta ce wuraren ayyukan yi kadan ne ke da matakan kariyar dake kare ma'aikatansun a wuraren da suke aiki,

Neira ta ce ma'aikatan lafiya sun gamu da matsaloli da dama da suka hada da cututtuka masu yaduwa da samun raunuka da cin zarafi da kuma rashin ingancin wuraren aiki,