Ana Jimamin Sace Dalibai a Kebbi, 'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Sokoto 

Ana Jimamin Sace Dalibai a Kebbi, 'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Sokoto 


’Yan bindiga dauke da makamai sun farmaki kauyen Tarah da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto. 'Yan bindigan wadanda suka kai harin a daren ranar Talata, sun yi garkuwa da mutum tara tare da jikkata wani mutum guda. 
Jaridar Leadership ta ce an kai harin ne kwanaki kaɗan bayan an mayar da ’yan sa-kai na kauyen Tarah zuwa Katsina. 
Dauke 'yan sa-kan ya bar kauyen ba tare da kariya ba a daidai lokacin da ake bukatar tsaro sosai. Majiyoyi sun ce matasan yankin sun yi gaggawar taruwa inda suka fuskanci maharan, wanda hakan ya hana aukuwar barna mai muni a kauyen, rahoton ya zo a Daily Post. 
A baya-bayan nan, sace mutane da kashe-kashen al’umma a Arewacin Sokoto sun zama ruwan dare, inda 'yan bindiga ke farmakar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba. Wadannan hare-hare na baya-bayan nan sun sake bayyana bukatar da ake da ita wajen samun tsari na haɗin gwiwa domin kare al’ummomin da ke cikin hadari. Lamarin ya kuma haifar da sabuwar damuwa game da yawaitar garkuwa da mutane da kuma kisa a jihar, musamman ganin cewa al’ummomi na ci gaba da fuskantar barazana duk da ayyukan tsaro da ake yi.