Ana caccakar gwamnatin Neja bayan umarnin  rufe gidan rediyon Badeggi FM

Ana caccakar gwamnatin Neja bayan umarnin  rufe gidan rediyon Badeggi FM

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayar da umarnin rufe gidan rediyon Badeggi FM da ke Minna tare da kwace lasisinsa da binciko bayanan mai gidan, bisa zargin yada shirye-shiryen da ke tayar da hankali.

Matakin ya janyo suka daga kungiyoyin fararen hula, Amnesty International, da ‘yan jarida, inda suka bayyana cewa hakan na nuna danniya da yunkurin danne ‘yancin fadar albarkacin baki.

Daraktan Badeggi FM, Abubakar Shuaib, ya bukaci gwamnati ta bi ka’ida ta hanyar kai kara zuwa Hukumar NBC maimakon amfani da jami’an tsaro don tsoratarwa.

Binciken ya nuna cewa ba wannan ne karon farko da kafafen watsa labarai ke fuskantar barazana a jihar ba.

Masu rajin kare hakkin bil’adama sun bukaci gwamnan da ya janye umarninsa, suna masu cewa hakan barazana ne ga ‘yancin kafafen yada labarai da dimokuradiyya.