ANA BARIN HALAL......Fita Ta 46

ANA BARIN HALAL......Fita Ta 46

ANA BARIN HALAL......Fita Ta 46 

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin ƘarfBurin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

Idan kana/kina sha’awar:

_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._

_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._

_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._

_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._

_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
*Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t

*Page 46*


*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE  ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559

**********
Ajiyan zuciya na samun nutsuwa na sauƙe,  a hankali nace mishi,  "mafarki ne nayi",  tashi tsaye yayi yace, "bakiyi addu'a ba ko? Ko kuma kina tunanin zan biyo bayanki ne"?
Girgiza kai nayi alaman a'a, sannan na gyara kwanciya na,  shiru yayi a tsaye yana kallo na, chan yace,  "beauty meyasa kike tsoro nane"?.
Buɗe ido nayi na dube shi, don lokaci ɗaya naji kaina yana wani sarawa, girgiza kai nayi alaman a'a,  ba tsoron shi nake ba,   "tou ki daure na kwana ɗaki ɗaya dake mana",  tura baki gaba nayi kaman zanyi kuka, ganin haka yasa ya jiya ya fice a ɗakin.

Washe gari wurin ƙarfe 3:50pm sai gasu yayah Ahmad da iyalensu A.G ya musu jagora har parlor,  ae bansan lokacin dana felfelo da gudu na rungume yayah muhammad ba, daɗi nakeji kaman nayi shekaru bamu tare, dukkan mu dariya muke yana rungume dani, yayah Ahmad na kallo yana gefen A.G, ae da sauri shima naje na rungume shi ina dariyan jin daɗin ganin su,  "chaɓ yau munaga wariyan launin fata, wato baki maraba da mu sai yayunki ko"?  Aunty B ta faɗa tana kama haɓa, kunya naji na rufe fuskana da hannun yayah Ahmad, shi da A.G sai dariyan abunda nayi sukeyi, haka naje na musu oyoyoyo dukkansu, duk da Aunty B ta wani kawai da kai, hannun areef na riƙo muka wuce kitchen, drinks na zuba saman tray na juyo zan fito sai ga A.G, shigowa yayi ya karɓi tray ɗin ya ajiye a gefe, buɗe hannun shi yayi yace, "zoki mun nawa oyoyoyo ɗin ko kuma mu kwana a kitchen ɗin nan,"  tsayawa nayi cike da mamakin shi, ganin bazai bani janya ba yasa na rufe idona naje na shige jikin shi, aiko rungume ni yayi a jikin shi sosai yana juyi dani a hankali, chan nace, "tou bari na kai musu ruwa plz A.Gn Beauty",
Sakeni yayi yana murmishi yace kawo A.Gn Eeshaa ya ɗauka, ke ki huta ko"?  Ban ja maganan ba na miƙa mishi, na koma na haɗa cake dasu chinchin na fito da su, kallona yayah muhammad yake cike da murmushi a fuskan shi, nima murmushin nayi na koma gefen shi na zauna,  bayan angaisa ne yayah muhammad ya sake mana nasiha sosai da ƙara mana shawarwari na rayuwa mai kashe jiki, daga nan yayah Ahmad yake cewa su tashi a wuce, turo baki nayi gaba ina "yayah tafiya kuma"?  Dafa kaina yayi yace "ke da nan da 2weeks zaku dawo Abujan? Sai kin gajji da gani ae, inaga kullum ma ina gidanki",  dariya matan suka mishi suma lallai kuwa A.G yasan ya auro ƴar gatan ƙanwa, shima dariyan yayi muka rakasu har mota, driver ne yake jiran su, hannu na riƙe dana yayah muhammad, ina kallon yayah Ahmad ina ƙara mishi godiyan motan daya bani, "albishir sisto"? Da sauri na kalle shi nace "goro kyakkyawan yayah na mai nasarori",  dariya sukayi har da A.G daya wani kafe ni da ido yana murmushi,  nasan bai taɓa karo da ganin dogon hira na bane,  "Yayanki ya biya muku makkah ku uku, ummie, Aunty B, ke,"  ƙara nayi na rungume yayah muhammad, dariya ya fara yace "bai miki ɗayan ba ae?  Shima ya biya mana ni da shi da jeedah shi, bana mu shidah zamu ƙetara insha Allahu," inji yayah muhammad da maganan shi ba mai tsawo bane sai takama, duk da shirun yayah Ahmad yafi shi magana, shi kaman A.G ne sai ta ɓaci kakanji su, hawaye na fara narasa waye zan kuma je gare shi, ganin haka yayah muhammad ya jawo A.G ya manna mishi ni yace,   "mu zamu wuce sai kayi aikin rarrashi, maganan makkan naji barrister yace ya nemi izinin ka ko"?
Murmushi A.G yayi yace,  "ranka ya daɗe ya gaya mun mungode Allah ya ƙara girma, ya mun gaggawa ne ae, naso ni nafara kaita, amma yanzun ma bai ɓaci ba tunda babban yayah ne, muma tare za'aje damu, nida M.G da wife ɗin shi",   "masha Allah abu yayi kyau sosai, Allah ya zaunar daku lafiya, zamu wuce sai kun iso",   haka mukayi sallama A.G na riƙe da hannu na har suka wuce, juyowa yayi ya kalle ne yana murmushi,  "hajiya Eeshan A.G",  juya ido nayi na mishi fari da su,  "Alhaji A.Gn Beauty" kiss ya kai mun kan lips ɗina yana murmushi, hannu na ya kamo muka shige gida.


Daren yau ma dai abunda ya faru haka ya faru, ranan kam da ƙyar numfashin shi ya daidaita, har naji tsoro nayi tunanin neman taimakon M.G ko zai kai shi asibiti, hanawa yayi ya shaƙi inhelan shi kawai, kuka sosai nayi ranan, don har hannu na nasaka na shaƙe wuyan shi, da ƙyar ya ƙwace kanshi a lokacin,   kwana biyu ya biyo bayan ranan bai sake gigin cewa zamu kwana ɗaki ɗaya ba, ni duk sai naji abun babu daɗi, amma ya na iya, tsoro nake ji sosai, kuma wannan ɗabi'un ban san ina yin su ba, lokacin kawai suke zuwa mun, kuma ko nayi ƙoƙarin na hana kaina yi abun sai yaci tura.


Sati ɗaya da yin auren mu da daddare bayan an idar da sallan ishaa sai ga M.G da Heedayyah sun zo, nidai har ranan period ɗina bai ɗauke ba, kuma ni 4dys nakeyi amma wannan karon tsabar tsoron da nakeji abu yaƙi tsayawa.

Da fara'a sosai na karɓe su bayan ya buɗe musu  ƙofa sun shigo parlon yazo ya mun magana,  rungume ni heedayah tayi tace,  "Aunty Aysha ina ta son leƙowa mu gaisa amma bai barni ba sai yau, gashi nasan yayah ba zai barki ki fito ba nasani,"  murmushi nayi bayan mun zauna na gayar da M.G, ya amsa yana ta murmushi, ya wani ƙara mun ƙiba a ido yayi haske,  sai wani fallin angonci yakeyi, kallon A.G nayi sai naga kaman ya mun baƙi ma, duk sai naji tausayin shi ya rufeni, gaisawa mukayi da heedayah sai tace " Aunty muje parlon ki mu gaisa da kyau",  ta faɗa yana wani riƙo hannu na,   "bana son gulma da faɗin abun da bai dace ba kinji ko Heedayah, don naga wani sabon falli kike ji dashi" muryan A.G ne ya doki kunnen mu, duk sai naji kunya ya kamani, don nagane mai yake faɗi, ita kuma zaro ido ta fara ta kasa cewa komai, sai M.G ne dayake dariya yace,  "jeki Giwata kuyi hiranku keda Auntynki," ya juyo kan A.G kuma yana "don Allah a daina firgita mun Giwata"  nidai ban ji mai A.G yace ba, hannunta na jawo muka wuce, don ya wani haɗa girar sama da ta ƙasa.

Muna zama na ɗauko mata drinks da ɗan abun taɓawa,  hannunta ta dafa a ƙirjinta tace,  "Aunty nifa hala baifi sai ɗaya ko biyu naga yayah A.G yana murmishi ba, dariya kam hala bantaɓa gani ba, amma tsawan shi yafi sau million yake mun, gara ma Adda Huda suna ɗan zama suyi hira, ballantana da aka fara sayyayyan auren ku kullum zakiji shi ƙus-ƙus da ita, dama shirun su iri ɗaya ne, nikan haushi na yakeji tun farko saboda yawan magana na, na ɗauka yanzu tunda na girma har da miji zai sarara mun tunda abokin shine, ashe abu kam bazai chanju ba, dafah fita zanyi da gudu da naji tsawan shi, tou ganin Giwa na yana wurin ne fah na ɗan kama kai",  dariya ta bani wanda har yasa na ɗan dara, wato dai halin su ne yazo ɗaya da M.G shiyasa Allah ya haɗa su,  "yana murmushi da dariya mana heedayah",  na faɗa ina dubanta, ya mutsa fuska tayi ta ɗauki coke ta buɗe ta ɗan kurɓi kaɗan ta ajiye, "Aunty yanzu yana iya ce miki I Luv u kuwa"?  Dariya sosai maganan ta ya bani,  ina kallon ta yadda tayi wani tagumi ta ƙura mun ido,  nace mata " bai miki kama da wanda zai faɗan bane ko"?  Ya mutsa fuska tayi tana lumshe ido ciki irin nashi, don na lura dukkan su ukun suna da wannan ɗabi'an, kuma dukkan su suna kama, amma yafi kama da ita sosai, haline shida Huda yafi zuwa iri ɗaya, amma ita Huda tana da fara'a, don kuna haɗa ido zata maka murmushi, amma babu surutu sosai,  "Aunty ae kam bai mun kama ba, nasan dai kam zaki na shan doka da umurni, ko ba'a miki tsawa ba kam zaki sha aika, da umirni, ke kam sai dai kiji ko kiga ana cewa wasu I Luv U",  ta faɗa tana riƙe haɓa, nidai murmushi nayi na sake wannan maganan na tambayeta yayh mummy? Tana lafiya ta gaya mun, inda tace mun idan ana gobe zamu tafi chan zataje ta wuni ae, shine nace zan tambayi A.G nima sai muje tare, amma bazan wuni ba zanje na ƙarasa a gida, kallo na tayi tace,  "Aunty kema A.Gn kenan kike gaya mishi? Aiko gara ki sama mishi wani special suna wanda zaiji ya banbanta shi da wanda ya saba ji",
Juya ido nayi nace,  "kinsan shi special ne, sunan shi ma special ne, bawai ina so kunnen kowa ya ji bane",  dariya ta kwashe da shi tana tafa hannu,  "Adda kawai ki faɗa babu kunya, bakiga shi ko agaban mummy da daddy Eeshan shi ko beauty yake faɗa ba? Ranan fah har daddy ya manta yace mishi ina yaje ya daɗe ko yana wurin beauty ne"? Kowa sai da yayi dariyan daddy, shine rana na biyu da naga murmushin shi, kinga kema ako ina yakamata kada kiji kunya, bakiga Giwana ko gaban waye ba Giwa yake ƙirana ba"?  Muryan A.G naji yana ƙiran ta tafito su tafi, baki ta turo gaba bayan ta amsa tace,  "yanzu fah shine zai kore mu don a barshi ya hole da amaryan shi bawai Giwana bane zaice mu tafi, kawai bazai bar mutum ya ɗan yi hira ba",  ta faɗa tana miƙewa tsaye, nidai murmushi nakeyi ina gyara gyalen jikina,  "Aunty yaushe zaki shigo kiga nawa gidan"? Ta faɗa tana fita da sauri jin ya sake zabga mata ƙira, na bayanta nabi da sauri ina murmushi,  a parlor muka same su suna tsaye suna magana, M.G ne ya dube ni fuska cike da fara'a yace,  "tou amaryar babban yayah mun gaishe ku munga wuri yayi kyau, muna sa idon ganin ku muma",  ya faɗa yana miƙawa A.G hannu,  hararan shi yayi suka fice waje, bayan su muka bi muka raka su har bakin namu Gate ɗin, bayan sun fita ne ya rufo Gate ɗin ya juyo inda nake tsaye ina jiran shi, kallona kawai yayi ya wuce ciki, a baya na bishi amma duk sai naji babu daɗi da yayi gaba ya barni.

Parlon shi nima ma zauna ganin ya zauma yana rage volume ɗin T.Vn,  "yaushe zaki gama wannan abun?"  ɗago kai nayi na kalle shi, ganin yayi magana amma kuma idon shi yana kan T.V,  shiru nayi bance komai ba, har ya gajji ya juyo ya kalle ni, sunkuyar da kai ƙasa nayi nace,  "na ban sani ba, 3dys yake yi ko 4dys, amma wannan naga har yanzu",  shiru yayi yana kallona, chan yace,  "saboda kin sakawa ranki tsoro ne Eesha ta, dom Allah ke yanzu heedayah basu baki sha'awa ba? Yakamata ki saki jikin ki dani, nifa ba dodo bane, and kuma bazan taɓa cutar da ke ba beauty, kinsan yadda na damu da ke kuwa? Kin san yadda abun nan yake hanani bacci da chin abinci kuwa? Don Allah ki daure ki cire tsoron, ni bazan miki komai ba sai abunda kika amince, nidai naga kin sake dani kin daina waƴan nan ihun da dukan da kikeyi kawai".

Hawaye na share na haushin kaina da nake ji, saboda Allah meye amfanin abunda nakeyi, ni wallahi wannan period ɗin da bai ɗauke bane ma yafi bani haushi, don insha Allahu idan ya ɗauke ko mutuwa zanyi zan bashi kaina,  "kayi haƙuri A.G nah insha Allahu idan ya tafi zan daina jin tsoron, kuma zan dawo ɗakinka",
"why not tun yanzun ki dawo mu saba kafin ya tafi? Na miki alƙawarin bazan taɓa miki wani abu da bako so ba ko da babu yardar ki a kai kinji beauty nah",  ya faɗa yana dawowa gefe na ya zauna, hannun shi duka biyu ya saka ya riƙo nawa cikin nashi, hawayena suƙa zubo mun a fuskana, bana komai ba sai najin ciwom sabon halina da nakeyi yanzu, ina jiran naji wannan chanjin yanayin halin nawa yazo mun amma sai naji shiru, shima ina ankare da shi, ganin shiru baiga ina wasu idun ba ya saka ya matso jikina sosai, Allah sarki A.G jikin shi wani rawa yakeyi kaman zan ƙwace mishi ne,  Rungume ni yayi sosai ajikin shi, nidai ban hama shi ba, haka ya ringa zuba mun kisses kaman zan cinye ni, har zaman kujeran ya gagare mu muka faɗo ƙasan carpet ɗin dukkan mu, har a haka yana rungume dani bai sake ni, ido kaɗan na buɗe jin hawayen shi da yake taɓa mun fuskana, tausayi sosai ya bani, gashi banji wannan tsoron ba amma kuma ina jini,  laluɓeni ya fara yi babu nutsuwa a tare da shi, sai wayan shi tafara ringing, a hankali ya buɗe odon shi ya diba mai ƙiran,  ido ya zubawa wayan bai ɗauka ba bai kuma kashe ba, ganin shirun da yayi ya ƙurawa wayan ido yasaka na miƙe da ƙyar na wuce nawa side ɗin don nayi wanka na chanja pad ɗina da nakeji duk ya ɓaci, ido ya bini da shi har na kusa wucewa tukun naji yace,  "M.G ne, ko me yake so bayan yanzu suka bar gidan"? Juyowa nayi na kalleshi, duk kunyar shi lulluɓe dani nace ,   "tou ka ɗauka mana, ko akwai abunda ya manta ne",  na faɗa ina kallon shi, ga hawaƴe kuma kan fuskan shi,  "ok, zaki dawo yanzu ko na biyu ki"?  Murmushi na mishi murya a hankali nace,  "wanka zanyi, zan dawo insha Allahu".
Shima murmushin yayi ya ɗaha mun giran shi duka biyu, sannan ya ƙira M.G, nidai wucewa nayi ina jin yana masifan "wallahi bazan buɗe ƙofa ba, ƙaton bamza yarinya ƙarama tana juya ka kaman waina, sai da safe ta aiko a ɗauka mata, tun da har yanzu sakara ce tana jefar da abu a unguwa",  nidai dariya nayi a zuciyata nace,  "shi ae juya shi akeyi, kao kuma kuka ma ake saka ka, gara shi yasan daɗin abunda yasa ake juya shi, kai hanya kawai ka ɗan kama amma aka saka ka kuka, ranan da ka ƙarasa kam ina ga sai maƙota sun taru rarrashi",  na faɗa ina shigewa toilet, wanka nayi da ruwan mai zafi sosai, bayan na fito na shirya cikin wani three quater da riga armless fari sol, cotton ne mai kyaun gaske, gashi na nasaka a wani hula mai net mai kyau na bacci,  bayan nagama kintsawa na ɗauki chwemgum na jefa a bakina, hijab har ƙasa na ɗauka na ɗaura akan kayan na fice,  parlon shi na shigo naga baya ciki, a zuciyata nace ya shige ɗakin shi don yayi wanka, hanyar ɗakin na miƙa, buɗe ɗakin nayi na shiga, baya ciki sai dai ina jin ƙaran shi a toilet yana wanka, ɗakin yayo sanyi A.C akunne ga ƙamshi daya kama ɗakin sosai, chan kan kujeran dressing mirrow na je na zauna ina jiran fitowan shi, ban daɗe ba kuwa ya fito ɗaure da wani farin towel a jikin shi, sai ƙamshin shower gel da yayi wanka yakeyi, kallona yakeyi fuskan shi ɗauke da murmushi, ganin haka na sunkuyar da kaina ƙasa ina wasa da yatsuna.

Kai jama'a typing ɗinnan ya isa haka, yunwa nakeji, su jikalle su ruƙayyah, fatin mama 
Aunty falila
ae ya isa haka ko? A jira mai kowa mai komai ya kai mu gobe kuma l


*AUNTY NICE*