ANA BARIN HALAL...:Fita Ta 40
ANA BARIN HALAL...:
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin ƘarfeBurin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
Idan kana/kina sha’awar:
_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._
_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._
_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._
_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._
_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
*Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t
*Page 40*
*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559
********
Kwanciya nayi saman gado tukun na ɗauki wayan, shiru dukkan mu mukayi babu wanda yace uffan, har kusan mintuna biyar, "hmmm yarinyar nan wato sai na sauƙe abunda yake mun yawo a kaina na tanka tukun ki amsa mun ko"? A.G ya faɗa bayan shirun da mukayi na wasu lokaci, murmushi nayi nace, "tou ae kai ke nema, kaga bansan me zaka ce ba kada na maka shishshigi", "kedai kika sani, yayah meye labari"? Duk yadda naso shareshi bai yadda ba, haka yayita jana da hira har zuwa wani lokaci tukun mukayi sallama, ya kuma sake jaddada mun kada na ɗauki wayan Aliyu, nidai da tou kawai na bishi, sallama mukayi nidai nayi shirin bacci.
Yadda yayi alƙawari kuwa da yamman yazo, parlon hajiya ummah na kaishi, bayan sun gaisa ta shige ciki ta bar mu nida shi, gaishe shi nayi sannan na tashi na fice domin ɗauko Sabeer.
Tunda na shigo rungume da Sabeer ya ƙura mana ido, da ƙyar naja ƙafa na zuwa gaban shi, hannu biyu ya saka ya karɓi Sabeer, shiru yayi mai ɗan tsawo yana kallon fuskan sabeer, kaman wanda yake ƙididdige abubuwan fuskan shi ya daɗe a haka, sai chan ya ɗago ya kalle ni, "masha Allah, Allah ya rayashi da imani, Allah ya jiƙan mahaifiyar shi yasa tayi shahadah",
"Ameen ya rabbi", na faɗa ina duban shi yadda ya riƙe babyn.
Ɗago kai yayi ya kalle ni yamun murmushi, "girls nake so ki haifa mun masu kama da ke, two, or three, idan kina son boy tou mai kama dani amma ya tafi ana uku" dariya nayi mai ɗan sauti kaɗan, ina kallon shi yadda ya wani ci serious, "tou idan kuma duka boys ne fah"? Na faɗa ina mishi dariyan zaro idon da yayi waje, gaba ɗaya girman su sua bayyana, "a gidan M.G insha Allahu za'a haifa mishi boys, nikan girls nake so, boy ɗayan ma nafasa, sabeer ya wadatar, idan kin matsa kuma sai M.G ya bamu ɗaya a nasu muƙara",
Fuska a ɗaure ya faɗa, daga gani kuma iya gaskiyan shi ne, murmushi nayi na girgiza kaina, "idan ya baka boy ɗaya zaka bashi naka girl ɗaya ne"?
Harara na yayi "haba Eesha, yara ukun ne zamu bawa wani? Tsaya kiji iya maganan gaskiya, ni ko hutu ƴata baxata je ko ina ba ballantana nayi kyautan su".
Kallon shi nayi cike da mamakin son kanshi, "amma kai kuma zaka ɗauki ɗan wasu? Tou idan ummie ko mummy sukace a basu ɗaɗɗaya fah"? "wayyo beauty ki rufa mun asiri kada ki haɗa abunda bazai yiwuba, yara biyu ko ukune kike zancen mu bayar da su? ko hutu baza suje musu ba ballantana kyauta, ni zan kula da ƴaƴana idan bazaki iya ba", dariya maganan shi ya bani, ga mamakin maganan da yakeyi, duk da dai shi maganan shi murya a ƙasa take amma dai yana iya mu hira, wanda duniya ta shaidah dagani sai M.G ake ganin yayi dogon hira da su, M.G kamma wataran baya amsa mishi, amma ni a rayuwar shi sai ya iya good 2hrs yana mun hira, some times nice ma ke nuna gajiyawa, kallo kuma a rayuwar shi har mamakin baya iya gajjiya da kallona nakeyi, "tou mu haifi 5, ɗaya mu bawa mummy, ɗaya wa ummie, sai mu rie 2girls 1boy, mu haɗa da Sabeer sun zama 4 mue dasu".
Harara na yayi yace, "ke Eesha nifa ko goma kika haifah bazamu bawa kowa ba, yauwa gari ki sani, ke ummie tayi kyautan kine ko ni mummy mai tsananin ƙulafucin ƴaƴa ta bayar da nine? Muma mu zamu riƙe namu, kuma 3 ne insha Allahu".
Dariya nayi kawai na bar mishi zancen a haka, "wawan nan ya sake ƙiranki kuwa"? Naji muryan shi yana tambaya na, kai na girgiza mishi alaman a'a, "jiya nagayawa ummie yadda mukayi da shi, kuma tace zata samu yayah muhammad akan maganan, duk yadda sukayi zata gaya mun".
Ajiyan zuciya ya sauƙe, "Allah ya sakawa ummie da alkhairi, gaskiya naji daɗin shawaran da ummie ta bayar, mungode Allah ya saka da alkhairi",
Babu daɗewa yace na ƙira hafsy a waya, shigowan hafsy na ɗan harareta ƙasa-ƙasa ganin kallon da take mun tana ɗan iskan smilling, "yauwa hafsy zuki sha da yaro nan sai ki dawo,"
Miƙa mata sabeer yayi ya ɗaura mata 50k a kanshi, "kisaya mishi madara da pampers ko? Murmishi tayi ta fita da sabeer, kallon shi nayi bance komai ba, har hafsy ta dawo naga ya miƙe yace mata suje waje, gwalo ta mun da tazo fita.
Basu wani daɗe ba ya shigo, zama yayi ya ɗan ƙura mun ido, kunya naji nayi ƙasa da murya nace, "mungode Allah ya ƙara buɗi", shirun da naji yayi ne yasaka na ɗago ido na kalle shi, abun ko da nayi tunani ne ya faru, idon shi ne dai a zube a kaina, "idan uba yayiwa ɗan shi abu sai a mishi godiya"? Naji muryan shi yana faɗa, ɗago da kai na nayi ina duban shi kaina a ɗan langaɓe, "nidai nagode Yayah A.G, Allah ya ƙara buɗi", "bana son yayan nan, a bani wani sunan special, yayah ae Ahmad ne da M.G.
Bai wani daɗe ba ya mun sallama, rakashi waje nayi har jikin mota, bayan ya tafine na wuce wurin ummin mu, a ɗaki najiyo muryan su, har chan na samesu, ina shiga kuwa hafsy tayi charaff tace, "yauwa Adda gara da kika shigo, dama har haƙurina ya kusa ƙarewa, kaman zan leƙa waje nace ki dawo, ga tsaraban da nake ta ɗoki an kawo, buɗe mugani, ummie ta hanani buɗewa", ta faɗa tana wani washe baki, ummie na hararan ta "amma dai hafsy ke kam ko wa ke aka kawo kayan nan sai a hankali", murmushi hafsy tayi tana jawo babban jakan da yake kusa da ita, tana dariya tace, "ummie ae abun Adda na mu ne, yanzu hala ƙaramin jakan ma nawa tsaraban ne, bari mu fara na ma'in ɗin muga meye da meye a ciki"?
Buɗewa tayi nidai ido kawai na ƙurawa bag ɗin, dogin riguna ne kusan kala biyar, masu kyaun gaske, sai jean skirt kusan kala uku da riguna masu kyau, sai holland guda biyu super guda biyu, lace guda biyu masu kyaun gaske, sai gayyan takalma designers masu kyau da wasu handbag masu kyau na yayi, sai turaruka da dai cusmetics sosai, idona na ƙura akan wani agogo mai kyaun gaske, ƙasan kayan kuma kaya ne kusan set 10 na Sabeer da takalmin babys guda uku masu kyau "tou ni khadijah, duk wannan tsaraba ne? Shi dayake da haɗa kayan aure a gaban shi ya kawo wani tsaraba mai yawa haka"? Ummie ta faɗa, na buɗe baki zanyi magana sai naji ƙaran shigan txt a wayana, Aliyu ne ya turo mun txt, tsaki nayi ko karantawa banyi ba na goge, ido na mayar kan ɗayan jakan da hafsy ta buɗe Leda na asama an rubuta ummie, ɗaukowa tayi ta buɗe, turmin zani ne holland guda ɗaya sai turare guda biyu, miƙawa ummie tayi tana dariya tace, "ummi gana ki tsaraban, sannan ta ɗauko leda na biyu, English ne a ciki sai wani flat takalmi mai ɗan laushi an rubuta Hajiya ummah ajiki, ajiye shi tayi a gefe ta ɗauko wani da aka saka shadda 10yrd fari da turare guda biyu a ciki, an saka Abba, dariya hafsy ta ƙyalƙyale da shi da ta ɗauko ledan gaba jiki na rawa ta buɗe saboda ganin sunanta akai, lace ne mai kyau a ciki, sai tarkacen, bags, shoe, cusmetics kala-kala a ciki, ga wani riga da skirt mai shegen kyau a ciki nata ma har da wani agogo mai kyau a ciki, rungume ledan tayi tana "Yaya A.G Allah ya baka Adda duniya da lahira, Allah yasa a aljannah a rabon kace", "Ameen ya rabbi" ummie ta faɗa tana kallonta da farin ciki, "hankalinki ya kwanta ko"? Ummie tace mata, tana wani jaririn dariya tace, "ae ummi bakiji yadda kayan nan suka sakani farin cikiba, gaskiya Yayah A.G duniya ne".
Harara ummie ta mata "tou maza rufe komai sai Abba ya gani tukunnah", ummie ta faɗa tana miƙewa zata fita, "ummie kada fa Abba yace no", hafsy ta faɗa, "bazai faɗa ba auta, amma abinda ya kamata kenan ayi", ummie na fita mutuniyata ta matso kusa dani, "Adda gaskiya kinyi dace da Ɗan gaske, don wallahi mutumin nan duniya ne, kiga wasu arnakun laces masu zafi? Wannan kam hala ma ya haɗa kayan shi achan, kuma ya tambayeki size ɗin takalman mune Addah"? Hafsy ta faɗa tana jin wani farin ciki domin ya nuna a fuskanta, nafi kowa sanin hafsy da son abun duniya, gashi dai akowani lokaci daga Abba har yayun mu cikin hidima suke mana, amma ita bata gajjiya da abun duniya, murmushi nayi na miƙe don jin an fara ƙiran sallan magrib, "nifa tun farkon tafiyan shi sister shi Heedayan nan ta tambaye ni size ɗin takalmi na dasu bra, ni na ɗauka ma mummyn su ce ta sakata, sai ana sauran kwanaki ya dawo ya mun wayo, don sai yanzu nagane, ya tambayeni nida ke wayafi tsayi nace kin ɗan fini kaɗan, shine yake ce mun kenan zaki fini tsayin ƙafa, ban fahimta ba nace mishi a'a size ɗaya mue sawa 39, kuma fah sai da yace kice hajiya ummah ma bazata wuce 39 ba nace mishi 38 take sakawa, ashe wayo yamun", dariya hafsy ta ƙyalƙyale da shi tace, "kai kaji ɗan bariki" harara na juyo na mata cikin wasa, "ae mijin nawa ne ɗan bariki? Ba laifin ki bane na bar shi ne har ya miki tsaraba", da sauri na shige toilet jin dariyan da hafsy ta sheƙe da shi, ima jiyota tana, "ashe fah kema Adda idan kin samu wuri duniya ce ke"? Ina toilet ni kaɗe ina smilling, wai nice ke ƙiran A.G da mijina ko kunya bana jin, haka nayi alwalan na fito na ɗaure fuska don kada ta kawo mun rashin mutunci, hannu ta saka ta rufe bakinta ta wuce toilet ɗin itama.
Abba bai wani yi faɗa sosai ba , kawai dai yace kayan sunyi yawa ne, ummie na taya shi, ƙiran wayan A.G yayi ya saka a speaker, ina jin muryan A.G na sunkuyar da kaina, godiya Abba ya mishi ya kuma mishi faɗan shi dayaje karatu kuma ga hidima a gaban shi ya kashe kuɗi haka? Shidai A.G godiya yake tayiwa Abba kaman wa shi akayiwa kyautar, daga jin voice ɗinshi risinawa yakeyi,haka ummi ma ta karɓa tayi godiya ta kuma ce ya gaida mummyn shi, itama godiya yayi ta mata, haka Abba ya sallame ni bayan ya tambayeni babu komai ko? Anan ne ummie ta ɗauko mishi maganan Aliyu da takurawan da yayi mana, ai kuwa Abba inda ya shiga bata nan yake fita ba, ɗaukan waya yayi ya ƙira yayah muhammad, ya umurce shi daya nemi Aliyu yaja kunnen shi, ya tabbatar mishi shifa bai manta riƙon da yayiwa habiba ba, sannan kuma ya gaya mishi ya tsayar wa ƴar shi da ranan aure, kada ya shiga hurumin da bana shi ba.
Ummi da kanta ta kaiwa hajiya ummah kayanta, ranan kuwa A.G yasha yabo a wurinta, har da cewa ba'a taɓa saya mata takalmi mai kyaun wannan ba tunda tazo duniya, ita dai ummie murmushi kawai bata tanka ba, sai da hajiya ummah ta gama murnan ta tukun tayi ƙasa da muryah tace, "tou kayan shi jaririn wa matsafiyar za'a kai ? Kada fah taje tayi wani surkullen ta ɓata maganan auren"? Murmushi ummie tayi tace, " babu abunda ta isa tayi akai hajiya, insha Allahu babu abunda zatayi yayi tasiri, za'a kaimata yau ɗinnan".
Haɓa hajiya ta riƙe tana ya mutsa fuska tace, "tou duk yadda kuka gani, amma nidai da za'a bi shawara na da kada a kaimata, amma yanzu idan an kai babu bayanin matsayin shi, kawai abokin Ahmadu ne",
"hajiya ae yanzu da maganan Aliyu ya taso tasan da maganar aure, amma dai bata san waye ba, don ko lokacin rasuwar habiba, yayansu ne ya haɗashi da ita awayan shi suka gaisa, inaga ae rasuwan nan ya rikitata bazata yi wani abun ba", ummie ta faɗa tana miƙewa, ya mutsa guska hajiya tayi tace, "a naki zucuyar imanin ba, don Hauwan da nasani ko mutuwa tayi ta dawo taga abun mugunta zata aikata, saidai Allah ya tsare".
*********
1month da dawowan A.G aka ska ranan auren mu, 3month mai zuwa, rana ɗaya dana M.G, zokiga rawan kai a wurin M.G, sai wani tsare-tsare yakeyi, sai da yagama A.G ya gwale shi, buɗan kai da reception kawai A.G ya amince zaiyi, haushi kaman zai kashe M.G, daga baya ne ma da A.G yaga ya tayar da hankalinshi ya yadda da maganan hawan da za'ayi, sai lokacin M.G ya ɗan sake, idan bani ba babu wanda ya isa ya ce ga ɗokin da A.G yakeyi, amma ni yakasa ɓoye mun farin cikin shi, photonan gidajen da zamu zauna bauchi da Abuja yake ta nuna mun, ya matsa wanne yafi mun kyau, babu yadda na iya dole na nuna mishi na bauchin yafi mun kyau, kallo na yayi yace, "Abuja yafi tsaruwa, kawai don baida girmane, shi 2bedroom ne, na bauchi kuma unguwa guda ne, side ɗin shi da ban nawa daban, 3bedroom ne nawa, ga parlor babbah, gidan yana kallon na M.G.
Abuja kuma A haɗe suke Gate ɗaya.
*AUNTY NICE*
managarciya