ANA BARIN HALAL....:Fita Ta 34
ANA BARIN HALAL....
*Page 34*
*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559
**********
Murmushi kawai yayi bai sake cewa komai ba, har na gajji da jiran naji me zai ce amma sai naga yayi shiru, duka hannayen shi yana kan stearing motan, idon shi na kallon gaban motan, "bari na bar ki kishigs gida, saboda bai dace na tsayar da ke a mota ba, insha Allah gobe zan shigo idan kina free, don jibi zamu wuce Abuja", juyowa yayi yana kallona, ko jira yake yaji mai zance? Ni kuma sai nayi shiru ban ce uffan ba, ƙoƙarin buɗe ƙofan nakeyi sai najiyo muryan shi yana cewa, "3weeks zanyi na koma, sai bayan six month zan gama insha Allahu, tsarabanki gobe zan shigo miki da shi insha Allahu,"
Buɗe motan nayi na fito waje, hannu na riƙe da handbag ɗina, fuska a ɗan ɗaure nace, "sai da safe mungode," banjira jin mai zaice ba nayi gaba zuwa side ɗin ummie nah don na mata saida safe, ina shiga na samu babu kowa a parlor, ɗakin ummie na wuce, ta fito daga toilet alaman alwala ta ɗauro, gaban mirron ta na ƙarasa inda naga ledan namanta akai, kallona tayi tace, "hafsy tace mun yayan ku A.G ne ya saya mana ko?" ɗaga kai na mata alaman hakane batare da nace uffan ba, "tou angode Allah ya musu albarka" a zuciyana na amsa sannan na mata saida safe, ko ta kan su hafsy ban bi ba, don nasan ina zuwa zasu ɓata mun lokaci.
A ɗaki na samu su zainab sun baza nama a plet kowa tana figan nata, gefe ɗaya kuma sun ajiye mun nawa a leda, hiran su suke tayi na sha'anin bikin da muka gama, nidai abunda yake damuna ya dameni, nayi mamakin M.G daya na sauƙe su ya wuce abunshi, don ina ganin ko cikin gate ɗin gidan bai shigo ba, daga waje ya ajiye su, ni bai isa ya mun shariya ba, don ko wallahi wurinta yazo, Allah ya bashi sa'a, haka na ci naman ba wai don ina jin daɗin shi ba, gaba ɗaya na rasa me yake damuna ne kawai, haka muna gamawa kowa tayi shirin kwanciya.
Washe gari duk shaƙiyancin su hafsy ban kula su ba, don ina ankare da su agaban ummie suke zabga rashin mutuncin su suna dariya, har suka saka hankalin ummi dawowa kanmu, alama kuma kaman ta fara zargin wani abu ne daga yana yin dariyan su, 50k ya tura musu na shawarma, kuma yadda ya bayar haka na saka musu 25k ma kowa, ganin hakan ne suka fara tiƙa dariya kaman wasu tumakai, nidai ban kula su ba na juya na bar ɗakin.
Hadiza ne da ta fito daga side ɗin su habiba take ce mana yau kam sun haɗu har sun gaisa, nan habiban take ɗan tsakura mata abunda yake faruwa, wai haka kawai Aliyu zai burkice mata yace shi bai taɓa son ta ba, kuma shi ni yake so amma don su cuce shi suka aura mishi ita, shi bai san ma yayah akayi ya rabo da ni ya koma mata ba, daga nan kuma idan ta tanka akan ae abunda yayi Ayshaa shi yayita, ae duk ɗaya ne yayi haƙuri itace ƙaddaran shi, ae kuwa nan zai kama dukan ta yana ƙiranta da mummunan ƙaddara dai, tana gayawa hadiza tana kuka, akan ita wallahi mamie ne ta matsa akan maganan, ita dai tasan yana burgeta amma ita ma batasan yayah akayi wannan al'amari ya faru ba, tayi -tayi ta kaucewa abun amma ta kasa, kuma mamie tace zata tsine mata idan ta bari abun ya fasu, hadiza tana gaya mana cike da tausayin habiba, "hmm kunsan babu abun da mushirikiyar uwarta bazata yi ba, yanzu haka ma ita ta maida hankalin habiba kai, gashi asirin ya karye aure baije ko ina ba, sai tsaraban ciki", zainab ta faɗa tana ya mutsa fuska.
Bayan sallan azahar zainab ta wuce unguwar su, hadiza kuma tace sai gobe da safe insha Allahu.
Ana sallan ishaa wuraren 8:00 sai ga ƙiran A.G, ina ɗauka naji yace , "ina waje", raina ne naji duk ya ɓaci, babu yadda na iya na fito parlor na gayawa hajiya ummah A.G yazo yana waje, bakinta kaman zai tsage tsabar fara'a tace naje na shigo da shi mana, haka na fita babu ko ɗan powder a fuskana, na daiyi wanka bayan magrib saboda bana sallah, dogon rigan material na saka, amma dai ina ƙamshi na gaske, gyalen material ɗin kawai na yafa na fita, yana tsaye a jikin motan hannun shi riƙe da wayan shi yana dannawa, ina isowa turaren shi mai suna *BVLGARI* yana tashi a jikin shi, designer ne mai ƙamshin gaske, yana sanye da blue jean, da red ɗin polo, yayi wani haske yayi kyau a idon masu ganin kyaun shi, sallama na mishi murya chan ƙasa -ƙasa, ban yadda mun haɗa ido ba lokacin da ya kallo ni, shiru yayi baice mun komai ba, naga muna ta ɓata lokaci a tsaye, sai na daure na ɗago kaina nace, "mu shiga parlon ummah" bai ce uffan ba sai ido da ya zuba mun, juyawa nayi na nufi hanyan parlon, ina jin shi ya rufe motan ya biyo baya na, a parlon muka samu hajiya ummah zaune ta ƙurawa T.V ido kaman gaske tana ganewa, don kuwa labarai ne ake yi a channel ɗin CNN, zama yayi yana gaisheta cike da sakewa a fuskan shi, itama da fara'arta take amsawa, sannan ta tambaye shi "ina M.G?" murmushi a fuskan shi yace, "M.G yaje neman aure, ya tafi hira", ya bata amsa yana ɗaukan remote ya rage vulome ɗin da madam ummah ta wani ƙure, dariya tayi na jin daɗi, "kaii kai kai abu yayi kyau, a gari yake neman auren kenan"? Ta tambaye shi, "ƙanwata autar mu yake nema, sunan ta Heedayah".
"kace ƴar gida za'ayi kenan? A ashe muktari yayi maka wayo, shi kam a gida ya samo, kaima ae yakamata ka nemo, sai a haɗa ku tare asha biki, don abun zai fi armashi", murmushi yayi ya ɗago kai ya dubeni, sanan yace, "ke baki iya kawo wa baƙo ruwa ba ko? Haka za'aje gidan ki"? Turo baki nayi na miƙe nayi hanyar kitchen ɗin, ina jin hajiya ummah nacewa, ae banida wayo ne ko kaɗan, wannan mijinta ae zai sha fama, sai dai Allah ya bata nagari kuma ɗan gida.
Maida kallon shi yayi kan hajiya ummah yace, "hajiya ae ni yakamata kibawa ita, kinga nima nasamo ƴar gida irin na M.G, sai ayi tuwona mai na ko", ya faɗa yana bina da kallo fitowa na daga kitchen, hararan shi nayi ina mamakin wayon mutumin nan, wato so yake ya ɗaureni kenan ko?.
Cike da murna hajiya ummah tace, "idan nice wallahi na baka, kuma nayi imani daga iyayenta har yayunta babu mai hanaka, kai dai gata nan sai ka nemi haɗin kanta, mudai fatan mu ɗa addu'an mu Allah ya haɗa kanku, Allah yasa ace gara da akayi, bari na baku wuri kuɗan zanta, Allah yayi albarka abu yayi kyau", haka ta miƙe tayi ɗaki tana bani sallahun idan mungama na kashe mata T.V kada ya zuƙe kuɗin Usmanun ta.
Murmushi yayi yadawo da kallon shi kaina bayan ta ƙarasa shigewa ɗakinta.
Nidai ban yadda na ɗago da kaina na kalle shi ba, amma a jikina naji shi yana kallona, chan kuma naji muryan shi, "naso M.G mutaho tare ae, amma yaƙi, wai shima zai gyara zaman shi ne a wurin yarinyar nan, gashi ni sai naga kinƙi sakewa da ni", ɗago kai nayi na kalle shi, a zuciyana nace kaji mun mutumin nan, wai M.G yaƙi rako shi, wato hiran ma M.G ne zai mishi, tou zaman auren fah? Ƙara ɗaure fuskana nayi, don so kawai nakeyi naji yace zai tafi, amma mutumin ki kam sai ya gyara zama, "ina su hadiza da zainab, ko suna ɗakine?" ɗago kai nayi na kalle shi a fakaice, sannan nace, "zainab ta tafi gida ɗazu, hadiza kuma sai gobe insha Allahu, tana ciki tana waya ne", na faɗa da ƙyar kaman an mun dole, shiru ya sakeyi daga nan baice komai ba, amma kuma idon shi yana kaina, nidai wasa kawai nake da gyale na, ina ji kaman nace mishi sai da safe, haba me za'ayi da mutum shiru, ni shiru shima shiru ae abun baiyi ba, gaskiya M.G bai kyauta mun ba, bayan nagama sakawa raina shi zaice yana sona, amma sai naji wani daban, kuma tsaban banida muhimmanci a fuskan shi nace kada ya nemi sister A.G shine yayi kunnen uwar shegu yaje ya nema, nima daga yau na cire shi a raina, bazan sake tunanin shi bama, nima zan dage da addu'a Allah ya fito mun da wanda nake so, don wannan kam sallaman shi zanyi, ɗago da kai nayi ina kallon shi jin yana mun sallama akan zai tafi gida, da jin daɗi na amsa mishi da "nagode sai da safe" na faɗa ina miƙewa, ganin shima ya miƙe tsaye zai fita, har jikin mota na rakashi, tsayawa yayi kaɗan yana kallona, "me zancewa mummy"? Ɗago kai nayi da hanzari don jin abunda ya ke faɗi, "ka gaisheta" na samu bakina da faɗi, murmushi yayi mai ɗan sauti sannan yace, "inji waye zance mata"? hararan shi nayi a fakaice ina mutsul -mutsul da baki, kafin nace wani abu sai naga an buɗe gate, zuciyata ne naji ya yanke lokaci ɗaya, domin motan Abba ne ya shigo, daga ni har A.G bin motan mukayi da kallo har sukayi parking, ganin haka A.G ya dubeni da murmushi a fuskanshi, "bari ni naje na gaida surukina yasan ni waye yanzu a wurin shi, ki jirani" ya faɗa yana karasawa inda Abba yake fitowa daga motan, kaman an dasani a wurin kuma nakasa tafiya, ina ganin Abba ya miƙa mishi hannu fuska cike da fara'a, amma A.G yaƙi miƙa nashi ya duƙa yana gaida Abba, kafaɗan shi Abba ya ɗan buga yana amsa gaisuwan shi, idon Abba kuma akaina da nake tsaye jikin motan A.G, ganin haka ya saka na ƙarasa inda suke tsayen, hannu Abba ya miƙo mun na ƙarasa jikinshi, "sisto yayah akayi? Ina sauran ƴan'uwankin?" na'amsa mishi da suna ciki, sannan yace ya muka bar A.G a waje bamu shiga ciki da shi ba, ina ganin A.G yana wani sauƙe smilling, sannan yace, "Abba ta shigar da ni parlon hajiya ae, yanzu na fito ne zan kuma gida, saboda Daddy ya shigo gari ina so mu gaisa da shi", cike da farin ciki sukayi sallama da Abba nah, nidai duk a hargitse nake jin kaina, Abba na wucewa na mishi sallama, shidai murmushi yakeyi ya wuce motan shi.
**********
Washe gari da wuri hadiza ta kama hanyan Tafawa ɓalewa, sai naji duk gidan babu daɗi, ga ummitah ma ta tafi gidansu tun jiya, hafsy kuma tayi gidan Aunty Rakiya, haka na wuni tare da ummie nah, da la'asaar na shiga side ɗin Mamah don mu gaisa, abun mamaki ina fitowa sai muka haɗu da habiba da raliya zasu fita, daga gani kuma habiba babu lafiya ne, don duk fuskanta ya wani hau, wani zuciyan yace na tsaya mu gaisa, wani zuciyan kuma yace kedai wuce babu ruwanki, ina kallon ta muna haɗa ido tayi mun murmushi, nima sai na maida mata na wuce, duk sai naji ta bani tausayi, gaskiya Aliyu bai kyauta mata ba, da ƙaramin shekarunta ya maida ta bazawara.
Ana sallan ishaa na lallaɓa na koma ɗakin Hajiya ummah, don nasan A.G zai zo, kuma bana son ummi ta fahimci komai, haka ko akayi ana idaar da sallah kuwa sai ga wayan shi, tsaki na ɗan ja a hankali bayan na ɗauka yace mun yana waje, kallon hajiya ummah nayi nace, "Hajiya A.G zai shigo" murmushi ta fara tace, "kice dai yaro ya ƙyasa ƴar kyakkyawar jikata, dama raina ya kwanta da shi wallahi, don kullum addu'a nake ko shi ko mai fara'an nan Allah ya baki ɗaya, ashe wannan mai yana yin basaraken ne rabo, aiko bari na wuce ɗaki kafin ya shigo, kada yace tsohuwar banza kullum tana gaban television", tana faɗa kuwa ta wuce ɗakinta, nidai kaɗa kaina kawai nayi nafita.
Gaisuwa mukayi sai kowa yayi shiru, ganin bazai ce komai ba sai kallona,kawai sai na tashi na shige kitchen na kawo mishi ruwa, ina zama ya tambaye ni ina hajiya su gaisa, kallon ƙofan ɗakinta nayi nace, "yau bata jin son fitowane nake ga, ko kuma ma ta kwanta", ina faɗa ya dube ni yace, "ko kuma baki so mu gaisa ba, don jiya na lura bakiji daɗin gaisawan da nayi da Abba ba", baki na buɗe ina kallon shi cike da mamaki, sai kuma na turo baki gaba saboda irin kallon da naga yake mun, "mummy tace idan nazo na haɗaku ku gaisa, zan iya ƙiranta yanzu"? naji muryan shi.
Da sauri na buɗe baki ina kallon shi, "nikan bazan iya ba kunya nakeji", kallo na yayi sai kuma yace, "kedai baki son ɗanta shiyasa baki son gaisheta, don ma kada ta saka ranta akanki, bari na ƙira sai nagaya mata ba zaku gaisa ba",
nidai ido na zuba mishi har ya ƙira suka fara magana da shi, sannan ya tashi ya miƙo mun wayan naji yana cewa, "tou first love ga princess ɗin", baki a buɗe na ɗago kaina, amma sai naga ya miƙo mun phone ɗin, da sauri na karɓa nasaka a kunne, muryanta naji cike da farin cike tace, "my doug yayah kike? Yh mutanen gida"? Ni dai sake miƙa mata gaisuwa nayi cike da rusunawa kaman ina gaban ta, wani sakewa dani tayi tana tambayana karatu, sannan kawai naji tana tambayana, A.G bai ɓata miki ko"? Nidai ɗan murmushi kawai nayi ban iya nace komai ba sai ɗaga ido nayi ina kallon shi, giran shi duka biyu ya ɗaga mun, hakan yasaka na mai da kallona ƙasa, chan kuma naji Heedayah ta amshi wayan cike da karaɗi take gaishe ni, har tana ce mun ae M.G yace zai kawota ta gaishe ni, nidai murmushi kawai nakeyi har muka gama gaiswa dasu ya karɓi wayan shi, idon shi na kaina yace mun, "ina son mummy sosai, hope zaki tayani sonta da bata kulawa na musamman"? Kallon shi kawai nayi na sunkuyar da kaina, a zuciyata nace, kama jira kaima a baka kulawan tukun kafin ka nema mawani, haka dai hiran ya ƙare, sallama ya mun zai tafi, yauma har mota na rakashi, anan ya buɗe motqn ya fito mun da tsaraba, bai sauƙe ba parlor ya wuce dasu ya ajiye, sannan ya dawo mukayi sallama, godiya na mkshi ya harare ni na wasa ya shige motan shi ya tafi, ina dawowa parlon na samu hajjaju ta fito, haka ta buɗe kayan tana ta saka albarka, ni dai ban kalli me takeyi ba, sai da naji tace gobe zata nunawa iyayena tukun na juyo na kalleta, baki a buɗe nace, "waya aike ki ki gaya musu"? Harara na tayi ta rufe kayan tace sai ki ɗinke bakina ko ki ɗaure ƙafana.
*AUNTY NICE*
managarciya