ANA BARIN HALAL.......:Fita Ta 24
ANA BARIN HALAL...
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*PAGE* 24
*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559
**********
Washe gari muka koma bauchi cike da tsaraban mu da su Aunty j da Aunty B suka bamu, gefe ɗaya ga wani shooping na ban mamaki da M.G ya kawo mun, su fatima ma nasu daban,.
Muna komawa da 1week muka koma sch, kuma a wannan lokacin maryam tayi sabon saurayi likita ne mai suna Dr Abdoul, yana aiki a T.H, sunje da mamanta ne bata da lafiya Allah ya haɗa su, haɗuwan su da Dr ya fara kwancewa maryam lissafi da soyayyah, gashi lokacin ma zainab ma ta haɗu da wani ma'aikacin banki mai suna Abdoulmaleek, ɗan gayu ne shima sosai, hadiza tana nan da suraj ɗin ta, haka fatima ma tana nan tare da kabir ɗan maiduguri, da yake duk munyi addn ɗinsu a cikin group ɗin mu, sai ya kasance 9:00 na dare sai mun haɗe a group ɗin ana zuba chafter, yanzu dai ya kasance nice ƙwalli ɗaya banida ma shinshini, don yau mun haɗe an saka zainab a gaba da tsokana, duk da rashin maganan ta da baƙin halinta yau sai da tanka har da dariyan ta, domin sunan da mukaje tana gayawa Abdoul ɗinta wai handsome, duk tsiya muka fara mata anata voice note ana shan dariya, da taga abun ya mata yawa sai ta mayar da chaftern ta kaina, "tou ke ayshaa har yanzu baki samo mana naki gwanin bane? Ko rawan ido irin na yaran GRA kikeyi ne"?
Jammy ce ta bata amsa dacewa, "wan irin rawan ido kuma? ae kinsan da badan wani dalili ba da yanzu besty na gidan auren ta, gwaninta special ne zai zo, duk da teemah ta ɗan tsegunta mun wani lafiyayyen soyayyah da akeyi a ɓoye", ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya, sticker na zaro ido teemah ta turo, irin yyh akayi jammy ta tona mata asiri, nan kuwa zainab tafara tambayan waye?, haka mukai ta sharhin mu har 10:00 tayi, daga nan maryam tace zatayi waya da luv, hadiza kam dama bata daɗe ba ta mana sallaman cwit yayi ƙira, haka dai ta ɗaɗɗaya aka watse, sai ni da jammy ne ƙarshen sauƙa, bayan munyi sallama na koma na kwanta nayi shiru ina tunanin habiba, yanzu wasa gaske duk wani alaƙa da muka taso a ciki da ita ya rushe? Duk irin wannan yanayin idan ya faru ita nake tunani, gashi duk wata alaƙa dake tsakanin mu mamie ta bunne shi, ganin tunanin zai mun yawa sai na tashi na fito parlor nayiwa ummie nah sallama na wuce side ɗin hajiya ummah, ina shiga parlor na samu yayah ishaq da ummitah zaune a parlon suna hira, hjy ummah kuma tana fitowa da ga ɗakinta kenan, gani kuwa ta wani kalloni tana ya mutsa fuska, "jirgin danƙaro an ƙaraso ne"? Ko kulata banyi ba na wuce kan dinning ɗinta ina haɗa tea, "tou baiwar Allah idan kinji haushi yau naji ance ga wani yazo wurinki hira mana, kuma da baki so na faɗa kin wani haɗa fuska kinje kina ɗiba mun kayan shayin da ɗana ya saya mun don gadara ko? Tou daɗinta na nan gidan ɗana ne halak malak ba na wani ba, ballantana anuna mun iko", ta na gama faɗa kuwa hafsy ta juya kanta tana cewa, "kaji mun mata wai gidan ɗanta? Tou ae munfi iko da gadara akan gidan da komai na gidan, mufa nan gidan mahaifin mune",
Hararanta hajiya ummah tayi, baki agaba tace, "kaji marar hankali, tou ke idan an barki sai ki ɗauka ke wata abarce a wurin shi? Tou ae shi usman daba don farin cikina ba don ƙaniyar ku da duk ya maida ku zaman tafawa ɓalewa, duk kuje ku saje da su hadiza", dariya dukkan mu mukayi, yayah ishaq ya miƙe yana dariya yace, "ni wallahi surutunki ma ya ishe ni, duk kin takura ni kin hanani ƙarasa I Luv u na, bari na tafi ma na bar miki gidan, gidan da ba malam umaru bane yayi amma ake damun mutane da gadara", kafin ya ƙarasa hanyan fita hajiya ummah ta jefe shi da kofin hannunta, "ɗan banza mai wargajejen baki kaman na ubanshi, ae abunda malam yayi har ka mutu bazaka iya ba, har wani gida ne Usman yayi na nunawa a duniya wanda malam bai yi shi ba? Ja'iri ni irin gatan da malam ya nuna mun ni da ƴaƴana ae ƙaryan Usman yayi shi, har kuna wani ɗagawa gaku ƴaƴan wani ko"?
Dariya muke mata gaba ɗayan mu, don dama ƙarshen faɗan kullum haka yake komawa, ana taɓo mijinta zata koma kare shi, dariya yayah ishaq yayi ya fice yana ƙara mata ɓacin rai da, "wargajejen bakina fah na mamana na ɗauko, don baba na yafi kyau", da gudu ya ƙara sa fita saboda ya ƙara ƙular da ita, tsayuwa tayi ta rasa abun da yake mata daɗi, nida hafsy kuma sai dariya muke, bata kula mu ba ta wuce ta kashe T.V ta, sannan ta kalli hafsy ido a ɗaure tace, " maza tashi ki tafi inda kike kwana sokuwa mai nacewa soyayyan ɗa namiji, bakida zuciyar karatu irin na ƴar'uwar ki sai zuciyar son ƙaton banza mai babban baki, tashi ki fita marasa kunya", ta faɗa tana nunawa hafsy hanyar waje, dariya hafsy tayi ta gyara zama tace, "anan min zan kwana, babu mai fitar dani a duk inda yayi mun a gidan nan, idan mutum ya matsa kuma na ƙira Abba yanzu yaji irin sakayyar soyayyan da yayiwa mahaifiyar shi take mishi nata, bata son ƴaƴan shi, bata son su raɓeta",
"amma dai Allah wadaran munafuki mai haddasa fitina tsakanin ɗa da uwa, ni yaushe naƙi ƴaƴan usmanu? Yoo ko gadona ƴaƴan usman sukace na sauƙa su kwanta ae sai na sauƙa, ballantana ɗan banza cikin wani ɗaki na daban? Tou a hirr ɗinki kika ƙirashi kika tayar mishi da hankali", tana faɗa ta juya zuwa ɗakin kwanciyar ta tana ta mita, mudai dariya mukeyi nida hafsy, don babu abunda yake rufe bakinta irin ace za'a gayawa Abba bata son mu, Allah sarki hajiya Ummah.
**********
Kwanci tashi babu wuya a wurin ubangiji, yau wata shida da aure su habiba da yayah Ahmad, sannan yau ranan laraba 06/06/ 0000 muka tashi da labarin habiba ba lafiya wai tayi misscarrige, haka mamien ta da raliya sukayi ta sintirin zuwa asibiti, da yake Abba yana gari babu yadda muka iya, ana sallan magrib yace duk mu shiryah muje asibiti mu dubata, da yake a Ni'imah clinic take, ana sallah muka fito, da ummie, mamah da hafsy driver yaja mu sai asibitin, muna isa kowa saiga Aliyu zai shiga, bayan sun gaisa da su ummie muma muka gaishe shi, duk idon shi yana kaina ya amsa mana gaisuwan, bin bayan shi mukayi har ɗakin da habiba take kwance, muna shiga muka sameta a zaune maminta na bata tea tana sha, ganin ma tare sai mamie ta wani haɗa rai kaman taga mai ɗaukan ranta, ko kunyan idon Aliyu bataji ba ta wani kawar da kanta ta cigaba da bawa habiba tea ɗin, har gaban gadon mukaje dukkan mu muka gaisheta, ko ganin idon su ummie ne sai ta ɗago ta amsa mana fuskanta ɗauke da murmushi, amma kana ganinta kasan ta sha jinya, tayi baƙi ta rame, ni har raman ta ma da baƙin ya ban tsoro, kaman ba habiba ƴar gayu ba duk tazama kaman wata ƴar ƙauye, gefe ɗaya kuma kan carpet hajiya umma ne zaune tare da raliya, wanda kallo ɗaya ta mana ta cigaba da danna wayan ta, gefe ɗaya muka koma muka tsaya nida hafsy, domin mun gaida mamie ko kallon mu batayi ba, gara ma su ummie ta amsa gaisuwan su fuska a ɗaure, chan kuwa najiyo hajiya ummah tana tambayan Aliyu ina mummyn shi, "nikan Aliyu ita mahaifiyar taka kam bata gari ne? Naga har yanzu banga idon ta ba ko wani daga gidan ku? Ko dai baka gaya musu bane kana jin kunya irin na ƴan fari? Tou ae yanzu anci gaba ko haihuwa ne ae za'a faɗa ballantana ɓari, ɓari ma irin wannan da Allah ya kiyaye ba'a rasa rai ba", murmushi Aliyu yayi baice komai ba, sai mamie ce tayi magana ranta a ɓace, "hajiya ae ta ƙira taji yayah jikin, kuma tace tana tafe wani abune yasha kanta, amma kuma ae bai kamata ayita magana ba, naga wanda ya zama mishi dolen ae yana tsaye akan komai", ta faɗa tana ƙara ɗaure fuskan shi, mitsi-mitsi da ido hajiya ummah tayi tana kallon mamie, "ni kikan Hauwa neyasa bakijin kunyan shera ƙarya ne? Ina nan ɗazu da la'asaar muke jajanta rashin zuwan ta da rashin ƙiran wayan da batayi ba? Shima Aliyun wani sintiri ya tsaya yakeyi akai? Ina tunda yazo ya ajiye ta yace zaije office bai dawo ba sai wurin ƙarfe biyar, hidiman komai inace Abbanta ne a tsaye akai shida ɗanshi Umaru? Ga Aliyun nan ae a tsaye shi kam bazai zabga uban ƙaryan nan ba, tun da yazo a tsatsatsayen sai yanzu ya dawo, ko coolern abinci ɗaya banga ya shigo da shi ba, kuma hakkin sune bana Usmanu ba, dubi habiba inda ta lalace tafita hayyacin ta, haka aka basu ita? Kawai ƙatuwar mata baki son a faɗi gaskiya".
Hajiya ummah ta faɗa tana miƙewa tsaye, shidai Aliyu shiru yayi yana wani murmushi chan ƙasa-ƙasa, idon shi akan habiba da taketa sharan hawaye, babu daɗewa yayi waje abinshi, "sai a haƙuri dai za'a dinga yi, yanzu ta lafiyan ta kawai za'ayi ummah ba wai ta abinda sukayi ba, idan basu zo bama ae mu munzo, kuma Alhmdllh tunda mahaifinta na tsaye akai ae yafi akan ace babu kowa", ummi ta faɗa tana matsa jikin gadon domin rarrashin habiba da ta fara ƙara sautin kukanta, tsaki hajiya ummah tayi tana kallon mamah tace, "baiwar Allah ku tashi mu tafi, ae gaisuwan ya isa haka, na Allah da annabi kam ae munyi shi, kinga ae da yasan basu da gaskiya daga shi har iyayen shi da ƴan'uwan shi ae kinga fita yayi, yoo ba dole ya fita ba, yaga na banza ya samu, an tula mishi uban dukiya ankai gidan shi ya dawo yana cin uban ta la'ada waje, gashi ya lafta mata uban cikin da bai shiga mahaifah ba yabar mahaifinta da ɗawainiya, shi ko a kwalar rigan shi, ina zai damu daman yadda ake so, tunda junin mutane chushen mata ce ae kaɗan kuka fara gani, dama matan chushe ina take daraja".
Kuka mamie ta fashe da shi, cikin ɓacen rai take magana, " hajiya naga dai da habiba da ayshaa duk ɗaya suke a wurinki, amma kullum sai ki nuna ayshaa sune ƴaƴa nawa kuma ba ƴaƴa bane, idan mijinta da ƴan'uwanta basu zo ba ae bai kamata ki tallata ta a duniya ba, ae sai ki rufa mata asiri, tunda kowa yasan kowani aure da irin jarabawan shi, ae gara dai wanda tayi akan wadda batayi ba, ayshaan ko mashin shini tana da shine? Ae itace abun magana ba habiba da mijinta yake tsaye akanta ba, ina ruwana da uwar shi idan bata so? Shina ae kowa yasan ba banza bane an shiga an fita an raba tsakanine kawai, amma ni ae nagode Allah da naga nawa ƴar a ɗakin aure, ga ƙaramar ma tana shirin tafiya, wasu fah? Saidai suga a nayi".
"A hir ɗinki hauwa, wallahi a hir ɗinki da jinin usmanu, insha Allahu Aysha da hafsy sai kin ɗauki ƴaƴan su da jikokin su, kuma insha Allahu auren sai ya rufa miki asiri, ki rubuta ki ajiye koda bayan rai na ne, kuma na ƙara jin bakin ki ima magana kina yi wallahi zakiga matakin da zan ɗauka, don ko shi wanda ya ajiyeki sai na juya mishi baya kiga idan auren naki zai yiwau, shashasha marar tarbiya, duk kinbi kin ɓata tarbiyan yaranki, nan rumi-rumi yara sun taso tare amma mugun halinki da banzan nonoki sai da kika ɓata tsakanin su, kikasa ƴarki tayi ƙwacen mijin auren ƴar'uwarta, da yaki Allah ba azzalumin bawan shi bane sai Allah ya baku nasara domin ya kare Ayshaa don tasha nono mai kyau da tsafta, zuciyarta bata gurɓace ba irin na ƴarki da tasha mummunan zuciya nata ya gurɓace, insha Allah miji ɗangaske ayshaa zata samu ba mai dukan mace ba, inba tozarci da wulaƙanta kai ba ina duka ya mata har aka samu cikin ya bar mahaifan, ko dama bai shiga ba, tsabar babu Allah a zuciyar ki kuma kina mummunan fata a wasu? Kijira kiga yayah naki zasu ƙare tukun", hajiya tana ƙarasa faɗi tayi hanyan fita waje, hafsy da ke bin raliya da harara ban san me ya haɗu suba tom & jerry naga tabi bayan ummah, ita ma raliyan na binsu da harara, ita dai mamie kuka ta cigaba da yi tana guna-guni ƙasa -ƙasa, tsaki mamah tayi ta dubi habiba tace, "Allah ya baki lafiya, idan kinga dama ki gyara halayenki tun baki makaro ba, idan kuma baki gajji da wahala ba ki cigaba da biyewa uwarki, ita kuma ta cigaba da ɗoraki a hanyar da bata dace ba, inace yau wata shida da yin auren ki? Amma duk lokacin da kika shigo gidan kin fi ƙarfin ki shiga ɗakin kowa ki gaishe shi saidai idan kin haɗu damu a waje ki gaisa damu, kuma nayi imani da Allah su yayunki da sukayi hidima dake a auren ki baki taɓa zuwa gidan kowa ko ƙirasu ki gaishe su ba, tou wallahi kikabi ta haikar uwarki abun bazai miki daɗi ba gaba, domin mu duk nan mutuwa zamuyi mu barku tare, yayunki sune iyayenki, shi kuma aure haƙuri akeyi, kiyi biyayyah wa mijinki da iyayen shi, idan kika bi ta uwarki zaki sha wahala", tana gama faɗi ta juyo ta kalli mamie da ke kallonta da harara, itama hararan mamin tayi tace, "idan ke mai shirya ce Allah ya shirye ki, kuma magana da kika maidawa ummah ki tabbatar Alhaji yaji, idan kin dawo sai kiyi mishi bayanin wani dama kika samu da tana magana kinayi, mahaukaciya futsararriya".
"Tou uwar gami karki bari ƙuda ya riga ki, ni dai insha Allahu nafi ƙarfin mace, tsakanina da Alhaji kuma sai Allah, duk munafurcin mutum kuma ae ko dan haihuwa Alhaji zai zauna dani", juyowa mamah tayi ta dubeta tana murmushi, "ae da haihuwa irin taki gara da Allah ya bar ni ba haihuwan, don idan bazan iya tarbiyantar da ƴaƴan ba gara na xauna haka, kuma wani kalma na rashin ɗa'a ya sake fitowa a bakinki zuwa gare ni, tou wallahi zan manta a asibiti muke na nuna miki ni ɗin *ZAINABU* ce kinsan bana ɗaukan wargi, kuka habiba ta fashe da shi tana, "wayyo Allah nikan na shiga uku, don Allah mama kuyi haƙuri, mamie don Allah ki daina jawowa ana rashin zaman lafiya, da wanne zanji ne kam"? Ta faɗa tana ƙara ɓarkewa da kuka, lokaci guda naji hawaye ya zomun, don wallahi ni shaida ce habiba bata so taga ana wannan tashin hankalin, kuma gashi ni tunda naji dukanta Aliyu yayi sai naji hankali na yayi mugun tashi, gaba ɗaya tausayinta ya rufe ni, juyawa nayi na fita a ɗakin duk jikina a sanyaye, gashi nasan maganan da habiba tayi dole ne sai mamie taci ubanta idan mun tafi, duk da dai nasan yanzu bazata doketa ba, muna fita mukaga Aliyu tsaye a jikin motan shi yana waya, ganin fitowan mu ya kashe wayan ya taho har inda motan yake, ƙofan gaba inda hajiya ummah ta shiga ya riƙe murfin motan, fuskan shi ɗauke da murmushi yake mana sallama, tsaki hajiya ummah taja lokacin da motan ta fara tafiya, cike da ɓacin rai tace, "ni wallahi na raina wayon Aliyu nan, idan akace maka zai iya saka hannu ya daki mace, macen ma irin habiba sokuwa ae sai abun ya baka mamaki, ta wani gefen ne kawai bazan yi mamaki ba, idan na tuna nonon uwarta da yake yawo a jikinta, amma abun takaicin ɗaya ne ace jinina kuma jinin usman ta zama boran miji da uwar miji?"
"hajiya ae ba jininki abun ya bi ba, jinin uwarta ne yake yawo a jikinta, itama uwar da badon ta Allah ya taimaketa ba darajan ƴaƴa ae da boran ce a gidan namu"..... ae bata gama rufe baki ba ummah tace "ae boran ce kuwa a gidan usman, tou wa tafi daraja a cikin ku? Idan ba duban yarah ba da tsoron Allah irin nawa ae da tunin usman ya sallameta, tou tsoron riƙon ƴaƴan fitina kawai nake jiye muku, don jifa kam har dana dodon ningawa za'a na muku, idan ba masifa ba irin na hauwa saurayin ƴar uwarta kisaka ta janye shi? Don wannan al'amari kam a yawon asirinta ta samu sa'a, amma taga ranan asiri ae, don Alhaji yace mun tana ta masifah ɗazu, wai ashe tunda akayi auren babu wani ɗan'uwan shi da yaje gidan ta, ita ma ko taje gidan iyayen na shi surkuwar ta mata tsakani da ɗakinta, idan taga dama ta fito su gaisa idan bata so ba kuma har su bar gidan bata fitowa, shima Aliyun kullum gorin ta cuce shi ba ita yake so ba amma mashiryiciyan uwarta ta asirce suka juya mishi hankali zuwa kanta yakeyi, rayuwar fah Alhaji yace mun babu daɗi, don ko kuɗin makaranta uban ne ya cigaba da biya, don uwar yaron tace yaronta bazai wahala a banza ba, yanzu ma wai auren ƴar ƙanwarta ake nema mishi, shine maka sudin dokan, sunje jiya gidan maman nashi, itama yarinyar ashe tazo, suna zaune suna hira da Aliyun a parlon maman shi sai marar kunyar ƙanwar tata ta gansu, kin san ba tarbiya take da shi ba, ashe da zasu tafi taje har ɗakin da yarinyar take ta zazzageta, ita kuma yarinya mai tarbiya ce bata tanka ta ba, sai da suka tafi ta gayawa maman Aliyun, ita kuwa uwa ta ƙira tace yaja kunnen ƙanwar matar shi, kuma kada ya sake shigo mata dasu gidanta, ae kuwa inda ya shiga bata nan yake fita ba, yace dole raliyan ta bar gidan a daren, ina ga ita kuma ƴar uwar ku taƙi ne, shi ko zuciya ya ɗebe shi yayi ta bugunta har abun yazo da tsautsayi,"
Dariya mamah tayi babu wani shakkah a ranta tace, "hakki ne kawai hajiya, ae kaɗan ta gani, ae idaɓ junin mutum hassada ne ya ringa ganin abun da baya so, duk wanda yace ruwan wani bazai tafasa ba tou insha Allahu nashi ko ɗumi bazai yi ba, ta cigaba dai kada ta daina".
Ita dai ummie bata ce komai ba sai jinjina magana da take tayi, nima duk sai naji hankali na ya tashi, a haka muka iso gida gaba ɗaya kowa ranshi babu daɗi, muna isa kuwa ummi da mamah da hajiya ummah suka wuce parlon Abba, ni da hafsy dai side ɗin ummin mu muka wuce, muna shiga hafsy ta wani zabga mun harara, "ke wai Adda tausayin su kike jine? Wallahi gara ma ki daina don bakiji me banzan raliyan nan ta faɗa bane akanki", "bance ki gaya mun ba tunda banji ba, kuma ke hafsy ko babu zuciyar imani ajikin ki ae zaki tausayawa habiba, ae ba raliya da mamie zaki duba ba, ita zaki duba", na faɗa ina neman wurin zama a parlon, tsaki tayi itama ta nemi wurin zama ta zauna, "nikan Adda bana tausayinta, don banga abun tausayi ba, lokacin da taci amanar ki ita ta tuna da tausayin kene? Ina wani falli ma takeyi ta ƙwace miki miji? Ni wallahi ya mun daidai, dama mai siffana sheɗanun nan ya laftawa dukan da sai bakinta ya kumbura yayi, amma itama ana tafe, nata laftan yana zuwa", ta karasa faɗa tana kwashewa da dariya, nidai ido kawai na zuba mata, tana dariya tace , " bari manyan mu ya shigo musha dariya" yayah umar take nufi, nidai ko maida mata amsa banyi ba, don haushi ta bani kawai na ɗauki remote ina kunna T.V.
Gaskiya yau kan dai nayi ƙoƙarin typing ko? Gaskiya haka ya isa, ina laifin shi?
wannan page ɗin naki ne Fatie yawale, don ke nayi typing mai tsayi, ki huta ki isar mun saƙon gaisuwa zuwa ga Baba da Bobby
*AUNTY NICE*
managarciya