ANA BARIN HALAL..: Fita Ta Tara

ANA BARIN HALAL..: Fita Ta Tara

'ANA BARIN HALAL..: 

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

*PAGE* 9


Tunda jammy ta sauƙa na ji komai ya fita mun a kai, sai kawai na kashe Datan na tsurawa wayan ido kaman ina hangen wani abu, kaman wanda aka tunatar dani wani abu ko aka umurce ni, sai kawai hannu na ya tafi kan number Yayah Aliyu nayi dialing number shi, duk jikina kuma yana rawa, kaman bazai ɗauka ba har ya kusa yankewa sai ya ɗaga.
"Hello" naji ya faɗa bayan ya ɗauki wayan, amma sai na samu kaina da kasa cewa komai nayi shiru, chan sai naji ya ƙira sunana, "Ayshaa! akwai wani damuwa ne"? Ji nayi ido na duk sun ciko da hawaye, ban bari sun zubo ba kuma ban amsa tambayan da yayi mun, shima shirun yayi na zuwa wani lokaci, chan kuma yace "idan babu wani damuwa zan kwanta, don kaina ciwo yake mun",  nan ma shiru nayi, har zuwa wani lokaci kuma sai na kashe wayan gabaki ɗaya, naji wani irin ƙunci da ciwo a zuciyata, wato har baya son magana dani kenan ko? Na tambayi kaina da kaina, ban ce komai ba sai na maida kaina na kwanta nayi shiru, duk wani farin ciki na neme shi na rasa.


*WASHE GARI*
Da yamma wuraren ƙarfe biyar na yammah 5:00pm, ƴan gidan su Aliyu suka zo, lokacin ni kuma ina ɗakin ummie nah ina kwance, don wani irin ciwon kai ne ke damu na, kuma ganin yanayi na sai ummi ta bani paracetamol na sha na kwanta, a wannnan lokacin kuma ummi suna tare da mamah a parlon ta bayan sun tabbatar duk wani abu da za'a buƙata ya kammmalah wuri ɗaya, haka chan side ɗin mamie ma tana tare da ƙanwarta da ƙawaerta da suka taso tare, kuma habiba tana chan side ɗin don tun jiya da ta tafi bata dawo wurin mu ba, a haka baƙin suka zo, Abba da su yayah mojd da ƴan'uwan Abba ne suka tarye su, baƙi ne su huɗu a mota ɗaya, don haka naji hafsy ta shigo tana gayawa su ummi akan baƙin su huɗu ne, duk sai naji faɗuwar gaba ya mun yawa, har wani zazzaɓi ne naji yana son kamani a lokacin, sannan naji wani siririn hawaye wanda bansan da shi ba yabi ta gefen kunne na ya wuce.

Bayan shigan su mamah ta saka masu aiki da hafsy suka shige da abincin baƙin da akayi, snacks ne dasu kayan drinks, sai nono da fura da aka dama musu mai kyaun gaske yasha kwaƙwa aciki aka kai musu, bayan sun dawo bai wani fi 30mnt ba Yayah Ahmad ya shigo ya samu ummi yace su zo ita da mamah da ni, jikina na rawa na miƙe na ɗauki hijab ɗina nabi bayan su ummi, parlon cike yake da huhun goro kusan guda goma sai katun-katun nasu biscuit da su chewngum dasu alawa, suma ko wanne ya kai katun goma ɗin, a haka na raɓe a gefen ummi na na zauna, chan gefen Abba na kuma hajiya ummah ne zaune ta wani kima ɗauri kaman ranan ne za'a ɗaura auren, bamu daɗe da zama ba sai ga mamie sun shigo ita da habiba da ta sha wasu sabbin kaya kaman amaryah, nidai kallo ɗaya na musu na maida kaina ƙasa don wani kallon da mamie ta mun saida naji zuciyata ta yanke, don kallo ne mai ɗauke da alaman dariyan mugunta ko kuma tula maka haushi.


Shiru parlon yayi babu wanda yace komai sai Abba daya tsurawa ƙasa ido yayi shiru, duk fuskan shi a dagule da ɓacin rai, ɗago kai yayi ya zura mun ido, kaman baxai yi magana ba chan kuma sai ya numfasa da ƙarfi ya furta "Alhamdulillahi ala kulli halin, komai daga ubangiji yake mai kyau da marar kyau, Allah mungode maka", "Allah abun godiya mutum abun tsoro, ehhh mutum abun tsoro mana, ni ae tunda uwata ta kawo ni duniya ban taɓa chin karo da labcecen abun tsoro ba irin wannan, kai duniyar nan abun tsoro ne, mutum ma abun tsoro ne irin wannan mata da ƴaƴan ta labta-labta nan", hajiya ummah ta faɗa tana nuna mamie da habiba, mudai bakin mu shiru nida ummi, sai mamah ne ta kasa daurewa ta dubi ƙanin Abban mu da shima yayi tagumi tace, "Alhaji ƙarami me yake faruwa ne? Kaddai sun fasa ne? Naga duk kan ku babu daɗin gani",
" da fasawan sukayi ae dayafi sauƙi akan wannan irin lafcecen cin amanar da ƴar'uwarta ta mata da shi sokon saurayin Aliyu, ni yau naji abun da ya girmi shekaru na," umma h ta faɗa tana kama haɓa, chan kaman wanda tayi tunani ta sake cewa, "ni dama irin yadda nake sauraren hiran da yaran nan sukeyi da shi saurayin sai da na zargi haka, amma kuma bance komai ba gudun kada ace ni nake haddasa fitina, amma ko zuwan Rakiya wancan satin sai da na ɗan ƙyanƙasa mata amma firr tace mun haka baxai faru ba, sai naja baki na kawai na tsuke, don Aysha da habiba duk ɗayane  a wurina, ban taɓa nuna banbanci ba Allah yana gani, amma yanzu kam sai ta Allah", ta faɗa tana hararan habiba da ta sunkuyar da kanta ƙasa kaman wata munafuka, Bappan mu ne yace "hajiya ae duk babu abun da zai gagara, ae da yadda da amincewar ayshaan hakan duk ya faru, kuma a wurin mu duk ɗayane suke, kawai dai a saka musu albarka" Bappah ya faɗa yana gyara zaman shi.
"mukan saboda Allah a mana bayanin me yake faruwa mana, duk kunsa cikina ya ɗuri ruwa" cewar mamah.

"Khadijah" Abba ya ƙira sunan ummie na, a hankali ta amsa da "na'am Abban su",
"Ɗazu bayan ƴan gaisuwa da tambayan auren Ayshaa sun zo sai zance ya chanja, don bayan gaishe-gaishe da akayi sai aka sako zancen abun da ya tara mu, amma abun mamaki sai naji zance ya chanja kuma suna bani haƙuri da cewan ba maganan neman auren Ayshaa suka zo ba kaman yadda muka zata, wai sunzo ne akan habiba, saboda Aliyu da habiba sun fahimci juna kuma da yardar Ayshaa, da naƙi amincewa sai da nasaka muhammadu ya ƙira mun Aliyun, handsfree aka saka kowa yanaji, sai ji nayi yace sun kasa daidaitawa da ita Ayshaan ne, wanda daga baya tace saboda zumunci ya nemi ƴar'uwar ta habiba, jin haka yasa mukayi sallama, ban neme kuba saboda nasan tsakanin Ayshaa da habiba za'a ƙullah abun da yafi haka, kuma nasan saboda tana tsoron tunkarar mu zasu iya yin wannan dabaran, duba da haka yasa na amince mu ka koma tsayar musu da rana nan da wata 2, wato december first week idan Allah ya kaimu, amma duk da haka na taraku ne don naji ta bakin kowa a cikin su, meye dalili meye kuma hujkan su"? 

Ajiyan zuciya kawai ummie ta ajiye idon ta a kaina, "babu wani hujjah da dalili sai dai son zuciya kawai da ake kitsawa yaran nan, amma gaskiya magana ni bn taɓa ganin irin wannan ba, anzo neman auren ƙanwa kawai sai a ɓuge dana yayarta"? Mamah ta faɗa tana wani hararan mamie.
"zainab don Allah bana son tashin hankali, ina ce Ayshaa da habiba kam duk abu ɗaya ne?" Abba ya faɗa ranshi a ɓace, tura baki gaba mamah tayi gaba, ƙasa-ƙasa tace "abu biyu dai".
Abba bai sake bi takan mamah ba ya maida hankalin shi kan ummie nah, murmushi ummi tayi tace, "Abban su ae abun da yayi Ayshaa shi yayi habiba, kuma abun daka hanga nima shi na hanga, zai yiwu Ayshaa ta ji nauyin ta gaya mana bata son Aliyu ne shiyasa suka yanke shawaran su ita da ƴar'uwarta, kuma hakan ae yayi dai-dai, don sun fitar da mu kunyan mahaifiyar yaron, nidai nawa addu'a ne, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a garesu baki ɗaya, ayshaa Allah ya kawo mata rabonta, habiba kuma Allah yasa ace gara da akayi", ummi tana faɗin haka taja bakinta tayi shiru.

"Ƙofar shiga aljannar ki da ban Khadija, wannan sanyi zuciya da halinkin wanda ko an cutar da ke baki nunawa saboda haƙurinki, Allah ya haskaka rayuwarki da ta yaranki, Allah yasa albarka a zuriyar ki, insha Allahu kuma khairan, miji kam na Ayshaa idan ya tashi zuwa duniya ne, Allah ya kawowa Ayshaa chanji na alkhairi",  hajiya ummah ta faɗa, shima ƙasa-ƙasa mamie tace, "ba ameen ba," da sauri na juya na kalle ta, don daga ni har ummie na da yayah Ahmad da muke kusa da ita munji, harara ta wurga mun, da sauri na maida kaina ƙasa, bayan naga yadda habiba take ta haɗa zufah duk a furgice ta ke zaune.

"Alhamdulillahi, nagode Allah daya bani ke khadijah cikin iyale na", Abba ya faɗa yana duban habiba, "Habiba yayah nene gaskiyar maganan Aliyun"?.

"Abbah" habiba ta ƙira sunan shi, sai kuma tayi shiru kan ta a ƙasa, "ina jinki ƴan biyu nah" da sauri ɗaga kai na dubi habiba, wanda ita ma ni ta ɗago tana kallo, gaba ɗaya sai naji wani tausayinta saboda yadda duk na ganta a wani firgice, ga idon ta ya ciko da ƙwallah, da sauri ta mayar da kanta ƙasa, "Abba watarana muna zaune a side ɗin ummah nida ayshaa, sai tace ta nema na mata alfarma, ita dai bata son Aliyu kuma tayi-tayi taji tana son shi amma ta kasa, gashi tana jin nauyin ƙawar mu jamilah da kuma mummyn su, don Allah na taimaka mata na amshe shi ya zama nice zai aura, don sun gama magana da shi kuma ya fahimce ta, nidai naƙi amince mata har tayi fushi da ni ta daina kula ni, danaga abun zai kawo mana saɓani sai na sake neman ta mukayi zama, nan ta sake mun bayanin sun gama magana da Aliyun kawai amincewa na take jira, tou Abbah ganin bana so saɓani ya sake shiga tsakanin mu sai na amince, nan kuma tace mun bata son kowa ya sani ko mamie ce, har sai ranan da za'a zo gaisuwan wato yau, shiyasa mukayi shiru, itama mamien na ɓoye mata sai yau taji, don ce mata nayi wani ne ɗan katagum, kuma baya zama anan yana saudi, wannan shine gaskiyan maganan Abbah", ta ƙarasa faɗa idon ta yana zubar da hawaye, nidai tunda ta fara magana na shiga al'ajabi, don a duk zamana da habiba ban santa da ƙaryah ba, kuma daga ji wannan magana tsara mata akayi, kuma nayi imani da Allah ba asiri mamie ta mata ta burkita tunanin ta ba, don tun farko habiba ran ta yaso Aliyu, saboda haka ƙofa kaɗan za'a buɗe mata ta zurma, kawai *Aunty nice* naji tsoron ɗan adam a ranan ta bakin hajiya ummah, kuma nayi mamakin ashe duk ƙaunar mu da habiba namiji zai iya shiga tsakanin ƙaunar mu? Don ni ina jin ko yayah namiji yake bazai ɗauke hankali na ba, har na haɗa so da ƴar'uwata, ae *ANA BARIN HALAL*... don kunya, ko da naji son wani wanda ƙawata take jin so ko ƴar'uwata inaga zan iya yakice shi a raina,  ya kicewa kuma na har abada, amma meyasa ƴar'uwata da nakeyi wa wani irin so ta mun haka, meyasa habiba ta yanke yadda da amincin da yake tsakanin mu na tundaga tashin mu? 
Kallo na Abba yayi, sannan yace "haka akayi Ayshaa ta"?


*AUNTY NICE*