ANA BARIN HALAL.: Fita Ta Biyu
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Don Allah a mun uzuri na chanja sunan book ɗin daga *AMINAN JUNA* zuwa *ANA BARIN HALAL*..... danayi, saboda wani dalili, nagode.
*PAGE* 2
Alhaji Usman Umar shine sunan mahaifin mu, Bafulatanine haifaffen garin *TAFAWA ƁALEWA* da yake garin bauchi, mahaifina cikakken ɗan boko ne kuma ɗan kasuwa ne, wanda yake da matan aure guda uku.
Uwargida Hajiya Khadija itace mahaifiyar mu, itama bafulatana ce, wanda sun fito gari ɗaya da mahaifina, wanda takeda yara guda biyar, Babban ɗanta mai suna Mohd, sai mai bi mishi Ahmad, na ukun su Umar, wanda yaci sunan kakan mu, daga kanshi sai da ta shekara takwai tukun Allah ya bata ni Ayshaa, a lokacin ta cire rai da sake wani haihuwan, sai Allah ya kawo ni, bayan shekara biyu kuma Allah ya bata ƙanwata Hafsat, wanda itace autar mu.
Hajiya Zainab itace matar mahaifin mu ta biyu, ita kuma bafulatanar toro ce, ita kuma Allah bai taɓa bata haihuwa ba, amma tana riƙon ƴar ɗan'uwanta mai suna Adda, takwarar tace amma ana ce mata Adda, ita kuma zata kai sa'ar Yayah Umar.
Hajiya Halima itace matar mahaifin mu ta uku, ita kuma ƴar garin *DARAZO* ne, na jihar bauchi, Hajiya Halima yaranta biyu ne duka mata, babbar sunanta Habibah ita sa'o'i muke da ita, amma ta bani wata uku, sai mai bi mata Raliya ita kuma sa'o'i suke da Hafsat, wacce dayawa muke cemata Hafsy.
Mahaifiyar mu muna ƙiranta Ummi, macece mai haƙuri da kawar da kai akomai, duk abunka da wuya kaji faɗa ko tashin hankali a wurinta, shiyasa abubuwa dayawa zaka ga kaman ana ƙwaranta sbd haƙurinta, acikin ƴaƴanta Yayah mohd da Yaya Ahmad da ni muka ɗauko halinta sak, inda Yayah Umar da Hafsy kuma bansan inda suka ɗauko zafin rai ba, don ko shi mahaifin mu zafin shi ba irin nasu ba, duk da shima mutum ne mai zafi da tsauri, amma ya kanyi wasa da dariya da iyalanshi, amma Yayah Umar kam zan iya cewa hatta matan gidan ma shakkan sa suke ji, ita kuma Hafsy kwata-kwata haƙuri ne bata da shi, ga tsaurin ido da rashin tsoro, don ita hatta Yayah Umar ya mata abu zata yi gaba ta ɗan taɓa gunaguni.
Hajiya Zainab kuma mukan ƙirata da Mama, ita kuma macece mai ɗan fushi, itama bata da faɗa amma abu kaɗan zai tunzurata ta yi fushi, gashi itama bata ɗaukan raini ko kaɗan, shiyasa duk rashin mutuncin Mami, wato Hajiya Halima ta kan ɗan ragar mata, don ita bata ɗaukan rashin mutunci ko kaɗan, don ko Baban mune ya mata abu atake zaka ga fuskanta ya canja, kuma zata fito ta gaya maka gaskiya, macece da bata yadda da wai wata ta fita ba a wurin mijinta, ko dan ganin ita bata haihu ba, tou bai taɓa sakawa taji ita koma baya bace, kuma ɗan kowa nata ne, saidai ita bata cika son taga yara suna raɓanta ba, dayawan lokaci idan jikokinta na wurin Adda sunzo zaka ga tana yawan kora su waje wasa, dayake Adda tayi aure har tana da yara uku, na farinta twins ne, sai yanzu da take goyon namiji.
Mamie kuma wato Hajiya Halima mafaɗaciyace na nunawa a gari, domin ita kullum garin Allah ya waye sai ta nemi faɗa, ba mijinba ba matan ba, ba kuma yaran gidan ba, duk da Yayah mohd da Yayah Ahmad sun girma, amma bata bar su ba, Yaya Umar ne kawai zai shigo gidan kaji ta ɓata shiru, har zuwa yanzu da muka fara zama ƴan mata fitinan ya dawo kammu.
Habiba itama muna kusan yanayi da ita, itama ko kaɗan bata da fitina, idan ka ganta zaka ɗauka Ummin muce ta haifeta, gata ita ma tayi farin mahaifinmu, ga ruwanta na fulani, bazaka taɓa cewa Mamie bace ta haifeta, babu garin Allan da zai waye baka ji faɗan su da Mamie ba, saboda Habiba ita tana da sanyin jiki aiki kaɗan zaka ga ta ɗauki lokaci, wanda hakan zakaji muryan Mamie kaman zata ta yar da gidan don faɗa.
Raliya kuma wayo ne kaman zai kashe ta, kuma ita ta hannun daman Mamie ce, sannan duk wani rahoto ita ke kaiwa Mamie, babu abinda takeso irin taga ana tashin hankali, nan zaka ganta tana fara'a, kaman wata shaiɗan, shiyasa wataran tana shigowa wurin mu, zakiga Ummi tana mata nasiha, kaman gaske zata rusuna, amma bata wani lokacin zata koma halinta, ita da Hafsy ko kaɗan basu zama inuwa ɗaya da Yaya Umar, suma sanin halinsu baida kyau suna ganin yazo hutu zasu rage shigowa parlon Ummi,
Raliya munafurci da neman tsokana, hafsy rashin kunya, gashi kullum suna tare, amma baki mintuna kaɗan zakji sun kacame da dambe, akansu kullum sai Mamie ta shigo tayiwa Ummin mu rashin kunya da rashin mutunci.
Gidan mu gida ne mai girman gaske a G.R.A, Sakashim road, kina shigowa gidan filine mai girman gaske, wanda idan nace zai ɗauki mota guda ishirin tou banyi ƙarya ba, don idan ana hidiman biki a sake akeyin komai, duk wani programm a wurin ake yin shi, gidan sama ne side ɗin Baban mu, a side ɗin shi kuma idan kin sauƙo ƙasa akwai wani dogon korido, wanda zai kaiki side ɗin ko wacce mace a cikin su, wanda tanan wurin kowa take shigowa side ɗin Baban mu.
Ta waje kuma agefen dama flat ne guda mai ɗauke da parlor da ɗakunan bacci guda uku, wanda anan ne ɗakun su Yaya mohd yake kafin yayi aure, wanda yanzu daga Yaya Ahmad ne sai Yaya Umar.
Gefen hagu kuma shima kaman na su Yayah Ahmad yake, shima parlo ne da ɗakunan bacci guda uku, shi kuma Kakar mu ce Hajiya Ummah ce a zaune a wurin, amma bata daɗe da dawowa wurin ba, don da tana garin jos ne tana aure, rasuwan mijinta wanda bayan rasuwar kakanmu ta aure shi, bata haihu a garin jos ba, shiyasa yana rasuwa Baban mu ya dawo da ita gidan shi, tunda yanzu *TAFAWA ƁALEWAN* Baffanun mune guda biyu a gidan, wanda suke uba ɗaya da mahaifin mu, shima gidan Baban mu ya gama gyara shi, idan kinje zakiji kaman a bauchi kike, domin bai rasa komai na jin daɗin rayuwa ba.
Baban mu su uku ne a wurin mahaifiyar su, shine Babban cikin su kuma shine namiji a cikin su, sai mai bi mishi ita ce mai sunana, tun tana ƙarama Allah ya mata rasuwa, sai ta ukun su Aunty Rakiya, Mijinta babban mai kuɗine, wanda ya riƙe manyan muƙamai, da suna zaune a lagos ne, amma zuwa yanzu yayi ritire ya dawo bch da zama, inda suka ƙera babban gida a Fadaman mada, Aunty Rakiya akwai kaman ceceniyar hali tsakanin ta da Yaya Umar, gashi dama ɗan gidan tane, domin ɗanta na 2 Ishaq abokin shine, itama babbar ƴarta mace ce, Nana Asma'u, itama ta daɗe da aure a yanzu, sai dai itama ɗanta guda ɗaya dal,
Aunty asma'u ma'aikaciyace a CBN, tana zaune a garin Abuja.
Aunty Rakiya mutumiyar Ummin mu ce sosai, domin ita duk wannan aure-auren da Baban mu yayi takaici ta ke ji, domin ita macece mai tsananin kishi, ko kaɗan babu fuska a wurinta idan tazo gidan mu, ko wacce mace kuma Allah yasa suna shakkan ta, domin ita ɗin favourite ɗin Baban mu ne da kuma Hajiya Umma.
A gidan mu akwai parlo guda ɗaya mai girman gaske, wanda yake saman site ɗin Baban mu, parlo ne mai ɗauke da dining section mai girma, shima yana ɗauke da dining table mai girma, mai ɗaukan mutane 12, sannan doka ne a wajen Bban mu duk lokacin cin abincin dare dole ne a haɗu a wannan wajen, aci abinci tare kuma ayi hira tare, wanda rana ɗaɗɗayane mamie baza tayi faɗa da mutane a wajen ba, ƙarshe mama tashi take suyi barambaram ta bar wurin, shi kuma Yaya Umar duk ranan da yazama yana gidan mu tou tabbas idan ranshi ya ɓaci da faɗan su ƙarshe akan Raliya da Hafsy yake sauƙewa, daga nan kuma ya bar wurin ya koma side din Hajiya Ummah, akasarin lokuta shi da Yayah ishaq sun fi zama a side ɗin kakarmu.
Mamie bayan masifah ita macece mai yawon asiri, wanda kowa na gidan yasan da wannan ɗabi'an nata, amma Baban mu kuma baya yarda, don shi yace bai yadda da asiri ba, shiyasa take tsula tsiyar ta yadda taga dama, gashi ko kaɗan Aunty Rakiya basu shiri, inda Allah yayi taimako kuma tsoro da shakkan Aunty Rakiya ta keji.
Yaya mohd muna tsananin shiri da shi, domin komai nashi ni yake nema, muna jss 3 nida Habiba aka fara maganan auren shi da wata budurwar shi ƴar maiduguri, ƙanwar abokin shine, tazo service bch sai ta zauna a gidan mu, sunan ta Bintu, gaskiya zan iya cewa na daɗe banga mace mai kyau da tsarinta ba, gata ƴar gayu na nuwa, naji daɗi da farin ciki danaji Yayah na danafi so zai auri Aunty Bintu, a site ɗin Ummin mu ta zauna, gashi tana bala'in kyautata mana, kullum da safe idan tana shirin fita inda take service bana gajjiya da ganinta, ga wani ƙamshinta kaman nayi yaya nakeji.
"Aunty nice ranan dana fara ganin ki naji kaman da Aunty Bintu na haɗu, saboda ƙamshin kanuri da naji kinayi, sai naji kema ina ƙaunar ki kwatan kwacin yadda naso ta" Ayshaa ta faɗa tana kallo na, nima cikin ƙara walwala fara'ar fuskata nace, "Aysha kina koɗani dayawa fa, yanzu matan *MUYI NISHAƊI* idan sunji ki sai su ɗauka haka nake fa da ƙamshi, har naje mrs Al'ameen Da takwararki Aisha jewal, da maman fodio sukawo mun ziyarar bazata" na faɗa ina ƙara murmushin fuskata.
Itama Aysha cike da fara'a a fuskarta tace, '"gaskiya ne ae Aunty nice, nidai haka kawai kina burgeni kuma ƙamshin ki yayi daɗi, dole ma ki haɗani da wacce kike sayan turarenki a wurinta, duk da dai Aunty Bintu bata rageni da turare ba har yanzu.
lokacin da maganan auren Yayah mohd da Aunty Bintu ya taso gadan-gadan, lokacin tagama Service har ta koma Maiduguri, Ummin mu ta wakilta Adda ƴar gaban Mama da wata ƙanwar Ummin mu wacce ake ce mata Goggo, itama anan bauchi take aure, suka wuce lagos domin acan Aunty Rakiya take aure lokacin, acan suka haɗu aka haɗo kayan aure na garari, kinsan auren ƴan maiduguri da ƙaryan kaya dai Aunty nice?
Girgiza kaina nayi alaman hakane,ina ƙara saurarenta, domin ni gaskiya bana gajjiya da kallon Ayshaan nan, don ni mace mai yanga burgeni takeyi sosai, ido na zura mata ina sauraranta.
Kaman tasan abinda yake raina, sai ta sake juya kyawawan idon ta cike da rausaya ta kalleni tana ƙara gyara zaman ta, "kina ji ko Aunty Nice, lokacin da suka dawo daga haɗa kayan auren ranan anyi tashin hankali agidan mu da Mamie, domin dama tana cike da bala'in tafiya da Adda da akayi lagos ɗinnan, tana jin haushi ba'aje da ita ba, ganin kayan kuma ta tada wani bala'in kan wai ana so duk kuɗin Baba ya ƙare, don ita bata yadda Yaya bane ya haɗa wannan uban kayan, ta manta Yaya Mohd a NNPC yake aiki, kuma mutumin nan yakai 5years yana aiki a wurin, gashi darajan Baban mu yasamu wuri mai maiƙo, Yaya Ahmad Barrister ne, shima yana Abuja da zama, Yaya Umar ne kawai ɗalibi, don shi kam da saura.
*AUNTY NICE*
managarciya