ANA BARIN HALAL...: Fita Ta 27

ANA BARIN HALAL...: Fita Ta 27

ANA BARIN HALAL...: 

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE

*PAGE* 27

**********
Numfashin shi naji alaman ba daidai ba, daga dukkan alamu abun yana kusa ne, sai naji hankalina kuma ya tashi, har bansan lokacin da bakina ya furta,  "yayah baka da lafiya ne"?  "kin damu ne da kisan lafiya na"? A.G ya mayar mata da amsa, runtse ido na nayi saboda yadda zuciyana naji ya yanke, daga jin yadda muryan shi yake fita babu lafiya, "sorry yayah A.Gn mu ka daina faɗa da fushi kaga baka da lafiya, kuma ni.....kuma shikenan dai yaya jikin"? Na tambaye shi, "kin taɓa ganin nayi fushi da ke? Na tafi banida lafiya anma bakiyi tunanin ƙiran kiji yaya nake ba, hakan kuma bai saka nayi fushi ba, ki tsoraci ganin fushina kawai, sannan meye kuma....kuman da kike son faɗi"?  Ya ƙarasa yana ɗan tari da jan numfashin shi a hankali,  " babu kawai zance tou kadawo mana tunda baka da lafiya, kuma ae kaima baka ƙirani ba",
"idan na dawo me zan miki? Akwai wani dalili ne da zai saka na ƙiraki? Ko ance miki kowa nake ƙirane"?  Tura baki nayi gaba kaman yana kallo na, murya chan ƙasa -ƙasa nace, "tou nima kowa ne nake magana da shi"?  "me kikace? Wato kin raina ni ko? Nine kowan ko"? Buɗe ido nayi ina zaro su don banyi tsammanin zaiji abinda nace ba, amma sai nayi diris nakasa bada amsa saboda yadda naga idon M.G ya koma, kaman wani marar lafiya, amma ganin na buɗe ido sai ya jefe ni da wani murmushi wanda bai wuce lips ɗin shi ba, da sauri na miƙa mishi wayan, yana ƙara murmushin fuskan shi ya karɓi wayan yakai kunnen shi yace,  "Friend yaya ƙarfin jikin? Amma yau kam ina ganin zasu sallameka ae ko? Don naji daddy yace zuwa friday zai dawo".
Hankali na ne naji ya sake tashi, wato a kwance a asibiti ma kenan yake? Wayyo Allah dama ban miƙa wayan ba, hannu bibbiyu na saka nayi tagumi ina kallon M.G da suke ta magana, zuwa chan naji yayi masa sallama ya ajiye wayan, kaman a sama na jiyo muryan shi yace.

"Tafiyan A.G wani abu ne da ya daɗe yana muƙurƙusa na, idan kinga na shiga gidan kakanun shi wato gidan Alhaji Inuwa tou sai ranan jumma'a, shima ba ko yaushe ba, domin yadda rayuwa ya ƙara juyawa goggon mu, Aysha goggo tasha wahalan rayuwa na kula da mu, kuma bazaki taɓa ganin gazawanta akan komai ba, goggo kitso ya janye a wurinta, yanzu ƙarfin sana'anta surfe ne da dakan hannu sai kuma masan da takeyi da safe, kuma babu lalaci ko kunya zamu fitar da tallen masan nida Hassan da hussain, da kuma kananzir ɗin inna ƴan'biyu, wanda yanzu itace zaune a ɗakin innan mu.

**********
Shekara na takwas yayah auwal ya gama school ɗin, wanda baya zuwa hutu sai ƙarshen shekara, domin yayah auwal ana hutu yake tsayawa da wani mutum ɗan bauchi mazaunin chan lagos, yana taimaka miki shi da zaman shagon shi, a haka yayah yake ɗan tara abun buƙatun shi na karatu, wanda kuma bayan wasu ƴan watanni ya kan turowa goggo da wani abu, lokacin da ya dawo gida yayi wani fari tass da shi, idan ka ganshi sai ka ɗauka balarabe ne ko wani bature tsabar farin shi, yayah sanie kuma yana level 2 a A.T.B.U, yayah Rabi'u this year ya rubuta weac da neco, amma shi hankalin shi gaba ɗaya akan ball ne, don ma yayah auwal ya gaya mishi dole fah sai yayi karatu, twins kuma suna S.S 1, ni kuma ina aji huɗu na primary, haka mukai ta murnan dawowan yayah auwal, babban abun farin cikin kuma yau shinkafa da miya goggo ta dafa mana, gashi har nama aka saka, nidai murna nan shinkafan yafi mun murnan dawowan yayan mu ma,"  A.G yana zuwa nan sai da muka kalli juna mukayi dariya, domin wani nishaɗi yake ji idan yana maganan shinkafan nan, nima kuma abun daɗi da dariya yake sakani, domin idan ka dube shi a yanzu yadda Allah ya dafa mishi baxaka taɓa tunanin ya shiga wani mawuyacin rayuwa ba.
 

**********
"Rayuwa ta cigaba da tafiya har nagama primary, baki tambayeni wa yake biyan kuɗin makarantar su yayah ba? Don ni dai har zuwa lokacin Aunty Rashida (mummy) ke biyan nawa, kuma idan an ɗauki lokaci tana mana aika, daga baya ma Daddy ya haɗa har da twins yana biya mana, karatun yayah auwal goggo ce ta sayar da wani gonan ta na gado, kuma yayah bai tsaya a neman kuɗi ba, son sai daga baya yake gayawa goggo har wanki da guga yayi a lagos kuma ya samu, so shi ya cigaba da biyan kuɗin shi, sai abun da yafi ƙarfin shi wannan ɗan'unguwan mu da yazama mishi uban ɗaki ya taimaka, yana gama service ɗinshi kuma ya tattara ya koma chan lagos ɗin, domin ya tsaya mishi ya samu koyarwa a wata private school, yayah sanie kuma da yayah rabi'u wannan bappan namu ne ya taimaka musu, sai kuma abunda goggo ta kalata, yayah rabi'u result ɗin shi baiyi wani kyau ba, saboda bai maida hankali ba, ba kuma babu kan bane, tsantsan ƙwallo kawai da yasaka a ranshi, saboda haka *BACAS* ya je yayi diploma ɗin shi a *PUBLIC ADMIN* yana gamawa kuma ya samu ɗaurin gindin fara buga wasan ƙwallo a team na wikki, kuma Alhamdulillah ya shiga a sa'a, don babu daɗewa sunan shi Rabi'u ya ɓace, sai dai kiji ana cewa *JOHN ZAKI* kuma babu laifi duk gidan mu babu sama da shi a son walwala, duk wani abun da yasa mo goggo ne, sai kuma ni ɗan lelen shi, don a lokacin asiri na yafara rufuwa da kayan gwanjon da yake tsinto mun, ga takalma har kala uku nake da su alokacin masu kyau, ina son ƙwallon a raina amma fir Goggo ta fige mun, kullum john zaki ya shigo na ringa tsalle ina mishi waƙan ƴan ball kenan, tou anan zakiga fushin goggo, rarumo abu takeyi ta jefeni, "ae wallahi yadda Rabiu ya ƙeƙashe yaje ƙwallo kai kam ƙaryar ka, don da wuri zan taroka",   shidai dariya kawai zaiyi kiji yana,  "sai goggon mu"  hararan shi takeyi ta shareshi, idan su twins suna nan su kama dariya suna cewa,  "ana yafito mata na goro kuma zakaji tace, "tou Allah yayi albarka Rabiu", dariya kowa yakeyi har goggon, don yadda suka iya kwaikwayon muryan mutane.

Bana mantawa lokacin da zamu gama primary, wani abokina da muke zaune sit ɗaya da shi Sulaiman, zasu koma kaduna da zama, dama baban shi banker ne, ya rubuta mun number wayan su, da yake landline ne lokacin, akan idan sun tafi zamuyi waya, shirme irin na yarinta, nasan fah unguwar mu gaba ɗaya gida biyu ne kawai masu wayan, daga gidan *Alƙali Abdullahi* sai gidan *Alhaji inuwa* gidan Alh inuwa kuma sun tafi umarah lokacin, kuma naji ance daga chan zasu wuce England su duba A.G da baiji daɗi ba, don ni naraka Goggo yiwa kakar A.G sallama, anan take gayawa goggo A.G asthman shi yana yawan damun shi, don lokacin wai har oxcygen aka saka mishi, duk da yarinta na damuna amma sai na shiga halin damuwa, gashi mun daɗe bamu gaisa ba, don an hana mu gaisawa, A.G duk ranan da ya gaisa dani iyayen shi sunce ya kan ɗauki tsawon lokaci yana fushi da kowa, makarantar ma ƙin zuwa yakeyi, idan an matsa kuma yayi ta kuka kenan, gaba ɗaya sukan kasa gane kanshi, gashi dai Allah ya ƙara basu haihuwan yara biyu amma duka mata ne, sun koma da 1year aka haifi *HUDA* wato A.G ya bata shekara shida kenan, sai bayan three years kuma aka haifi *HEEDAYAH* amma duk da haka son A.G daban ne a zuciyar iyayen shi, gashi kuma shi kaɗai ne mai ciwon asthmah ɗin, sai *HUDA* da ita tana da yawan mura amma ita bata da shi, sai dai ana kiyayewa sosai, bayan mun dawo ne nima nasamu kaina a damuwa da tunanin rashin lafiyan A.G, saboda haka na ɗauki paper da biro naje ɗakin yayah sanie, zama nayi a gefen shi nace "zan rubuta letter wa friend, idan nayi mistake ka gyara mun kaji yayah",   murmushi yayi ya dafa kaina yace,  "babu mistake ɗin ma da xakayi ae kai nasan gwani me mai brain",  daɗi naji sosai na hau rubutu, gaisuwa na mishi da tambayan yayah jikin shi? Sannan na bashi labarin abokina sulaiman, na kuma tambaye shi yaushe zasu dawo ƙasan"?
Gyara kaɗan yayah ya mun, da farin ciki na wuce gidan su A.G na kai letter na akan akai mishi, itama kakarshi da farin ciki ta karɓa, ta kuma mun alƙawarin zata kai mishi insha Allahu, daɗi naji na dawo gida.

Lokacin da muka rabo da abokina sulaiman, sai nayita tunanin ina zan samu waya na ƙirashi? Babu ɓata lokaci na tuna da gidan Alƙali, banyi shawara da kowa ba na wuce direct gidan, don na taɓa jin yayah hassan da yayah hussain suna labarin wayan a tsakar gida yake, kuma ana barin mutane suna ƙira da shi, don sun taɓa raka wani abokin su yayi waya da yayanshi da yake Abuja, tuna haka ya sakani tafiya gidan kai tsaye, cikin sa'a kuma ina isa saiga ƴar'gidan mai suna Ummatiti, domin lokacin ita ɗin budurwa ce, ganin ita tana da sauƙin kai don bata da hayani da faɗa irin na yaran gidan, ba kamar ƙanwarta waleedah ba, da sauri naje inda take shirin shiga gidan na rusuna nace, "ina wuni Aunty ummatiti"   da hanzari ta juyo ta kalle ni fuskanta ɗauke da murmushi tace, "ƙanina yau kaine da kanka kake gaishe ni? Yau ka kawo mana ziyara ne? Lallai girma ya fara zuwa",   tana faɗa hannunta riƙe da ni, nidai ban kawo kalmar ƙanina da ta faɗa da wani muhimmanci ba, kawai dai na ɗauka don ta girme ni ne.
Ina murmushi na nace, "nazo ki taimaka ki ƙira mun abokina mana Aunty",  na faɗa ina miƙa mata takardar da yake ɗauƙe da number shi, murmushi tayi ta miƙa hannu ta karɓi takardar, tana riƙe dani muka fara shiga cikin gidan,  "haba ƙanina kai da gidan ku sai ka nemi izini na? Kaima fah mai yiwa wani alfarma ne",  nidai sai daɗi nakeji muka shige gidan, lokacin babu kowa a tsakar gidan mai cike da interlocks, tsakar gidan mai girman gaske, yana ɗauke da wani varender mai kyau, wanda zai sadaka da babban parlon iyalen gidan, ana a gefe akwai wani friedge dogo da aka ɗaura telephone ɗin akai, babu kowa sai masifaffiyar mai tuwon gidan sun nan, muna shiga ta fito daga kitchen fuskan ta ɗauke da fara'a tace,  "lale maraba da uwar masu gida, uwar ɗakina kin dawo kenan"? Murmushi Aunty ummatiti tayi tana saƙo da wayan ƙasa,  "eh Babah na dawo, gashi yau na haɗu da autan mu wai yazo zaiyi waya, shine fah ya tsaya a waje yana neman alfarma, bayan shima mai yiwa wasu aƙfarman ne",  ta faɗa tana saka numbobin akan wayan, nidai daɗi kaman zan yi tsalle, ɗagowa tayi ta kalle ni tace, "ƙanina ina ga ana kan layi ne, amma zo kaga yadda ake yi, ni zan shiga na chanja kayane, idan baka gama da wuri ba zan fito mu sake gaisawa, sai na kaika ka gaida mamana," murmushi nayi domin wani daɗi nakeji idan tace mun ƙaninta nan, duk da bawai wani kyau take da shi ba, don baƙace sai dai doguwa ce kamar mahaifin mu, amma banga ta yi kyau kaman shi ba, sai dai akwai jininshi a tare da ita, so baza ace bata da kyau ba, don akwai ido da dogon hanci, sai dai baƙar fatan kawai.
Tana juyawa ban wani ɗau lokaci mai tsawo ba na gwada saka numbobin yadda ta gwada mun, ae kuwa sai naji wani ƙuwwwwt, ƙuwwwwttt, alamar yafara ringin, banji ɗaukan wayan ba sai naji wani abu mai azaban zafi na ɗaukan hankali a gadon baya na, da ƙara abun da fita a hankali na duk alaokaci guda naji shi, kuma ban ƙara jin komai ba ko fahimtan komai ba sai zuwa wani lokaci da naganni kwance a ɗakin goggo na, goggo da innah ƴan'biyu da dukkan yayuna, banda yayah auwal da baya nan duk suna tsaye akaina, gefe ɗaya kuma ga Umar mai chemist a tsugune akaina yan gyara mun drip, kaman ma yana chanja wani ne, don maga kaman sabo ake ɗaurawa, tashi naso yi amma sai naji wani azaban zafi a bayana, bansan lokacin da nace,    "wash Allah"
Da sauri goggo ta riƙe ni idon ta na zuban hawaye tace, "mukhtari na sannu ko, ka tashi?.... Mekake so?"  ta faɗa hawaye yana ƙara bin fuskanta, gefe ɗaya kuma Rabiu ne ya riƙoni jikin shi yana mun sannu.
Mai da ido na nayi na rufe ina jin wani mummunan azaba a jiki na, ga wani nauyi da naji kaina yayi mun, ga hannu na ɗaya da naji kaman ba ajikina yake ba dom azaban azaba, a hankali na sake buɗe idona nace, "goggo na ciwo nakeji, me ya same ni ne"?   Kuka Goggo ta fashe da shi gaba ɗaya ta rungume ni a jikinta, muryanta da jikinta gaba ɗaya suna rawa,   "haba mukhtari na, meyasa ga cikin malam Garba, kaƙi ka fito a cikin wanda bai san daraja da girman ka ba? Wanda me aikin boyi - boyi ma agidan shi tafi daraja da girma? Wannan abu yana mun ciwo ni Fatima, wannan abun yana firgita ni,  Allah ka raya mun mukhtari na, Allah ka ɗauka ka shi ɗaukakan da kake yiwa bayin ka nagari makusan tanka, Allah kayiwa mukhtari ni tanadi na alkahiri duniya da lahira, Allah ka ciyar da su a jikinka yadda basu ƙaunar ka Allah ka ƙaunace shi",  ta ƙarasa tana fashewa da kuka, chan kuma naji muryan Bappan mu yana cewa,  "ashha Alƙali basu kyauta ba, yau har an ƙure wannan baiwar Allah mai haƙuri, gaskiya basu kyauta ba Allah ya saka maka mukhtari, Allah ya fitar maka da hakkinka akan duk wanda yake da hannu aciki, don wannan kam ba halin Alƙali bane, yaran wasu ma ya riƙe, yaran nashi ma nawa ne? Amma duk gidan cike yake da yaran ƴan'uwa, ashsha abu bai yi daɗi ba",  ya faɗa yana matsawa jikin ƙofa, inna dai sai kuka take tayi Allah kaɗai yasan me yake sakata kuka, nima sai lokacin na fara kuka don ganin ƴan'uwa na da goggo na suna ta kukan, wanda ni har lokacin ban san me ya faru da ni ba, don sai daga baya goggo ke hiran da yayah auwal da yazo tukun na sani, kin san waye ya mun haka"? 
 Girgiza kai nayi alaman a'a, fuskana cike da tausayin shi har da goggon shi da ƴan'uwan shi,
Murmushi yayi ya sunkuyar da kanshi ƙasa yayi shiru na wani lokaci.

Nima Aunty nice shirun zanyi na wani lokaci, domin na ɗan huta, kuyi haƙuri da wannan don Allah, insha Allah labarin zai tafi yadda kuke so babu delay, sai day friday zan dinga hutawa insha Allahu.
*GIDAN KWAMUSHE* tou ga naku kyautan page ɗin, ku nemo dizzu ta kucincina muku, kowa ta samu, don ranan da Allah yasa nayi paid book, ku bar mun shi kada ku kwamushe 

*AUNTY NICE