ANA BARIN HALAL..: Fita Ta 10

ANA BARIN HALAL..: Fita Ta 10

ANA BARIN HALAL..: 

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*


*PAGE* 10


Ɗago kai nayi na dubi habiba, wanda har zuwa lokacin jikinta rawa yakeyi, maida kaina ƙasa nayi na saka hannun cikin na ummie nah na riƙe, ina ji itama ta damƙe a hannu na tana sauƙe ajiyan zuciya, muryah ƙasa - ƙasa na amsawa Abba da, "hakane Abbah, duk abinda ta faɗa haka ne ya faru" da rawar muryah na ƙarasa maganan, dai dai nan kuma Bappan mu ya amsa da, "Allah ya muku albarka, kema ayshaa Allah ya baki miji nagari, don baza ace kinyi wauta ba, amma gaskiyar batu kam akwai wautan a al'amarin, don dai komai ya wuce ne ae, ina laifin kiyi shawara da mahaifiyar ki kafin ki zartar da komai? Don dai duk ɗaya ne kawai, Allah ya kyauta", ajiyan zuciya Abbah ya sauƙe ya maida hankalin shi kan mu gaba ɗaya,bayan yayi mana dogon addu'a ya sallame mu, amma muna miƙewa mamah ma ta miƙe da sauri tabi bayan mu, tana ita bazata iya wannan zaman kayan takaicin ba, don idan ta cigaba da zama rai zai ɓaci, ina kallon yayah mohd ya bini da kallo, yayah Ahmad kuma ya dawo kusa da ummi ya zauna.


Muna fitowa habiba ta riƙo hannu na muryah ƙasa- ƙasa tace, "sisto nagode da kika rufa mun asiri, wlh duk wannan abun ya faru ne bada son zuciyata ba, amma insha Allahu zan miki bayanin da zaki fahimta, yanzu dai nagode"' , tana gama faɗa ta sake hannu na ta wuce side ɗinsu da sauri saboda hango raliya da ta fito daga babban kitchen ɗin dayake wurin, nidai bin ta da kallo kawai nayi ban iya nace mata komai ba, Mtssss, tsakin raliya naji dabdani, da sauri na bar kallon inda habiba ta wuce nayi, na maida kallo na inda raliya take nayi, itan ma bance mata komai ba sai ido dana zuba mata,  matsowa kusa dani tayi tana wani murguɗa baki, "mutum dai yaji kunya duk kyaun da yake gadara amma ya zama mai baƙin jini, baƙin jini kuma yanzu mutum ya fara, sai dai yaga ni wal ta gaban sh" tana rufe baki hafsy na kai mata mari a bakinta, "bakinki ya sari shegen guntun kashinki, insha Allah aniyar ku ta biku, ae kune masu abun kunyar da har babu kunya babu tsoron Allah kuka iya cin amana ƴar'uwarku, ae kuwa kune masu abin kunya, sannan da kike maganan baƙin jini, shin akwai wanda ya  kaiku baƙin jini? Kun kasa raminku sai dai ku ƙwace na wasu? Abun kunya ae ya tabbata akanku zuriyar matsafah".. tana rufe baki kuwa suka kancame da dambe, kowa duka take kaiwa ƴar'uwarta, nidai jan hafsy nake ina roƙon su dasu bar wannan shirmen, da sauri yayah mohd ya fito shi da yayah Ahmad, tsawa ya daka musu daga bakin ƙofan da yake tsaye, da sauri suka saki junan su suna huci kaman wasu zakaru,
"ku wuce kubawa mutane wuri sokayen banza da wofi, ku gaba ɗaya rayuwar ku baku da hankali, kullum sai faɗa baku son zaman lafiya"?
Nidai ganin yayah mohd ya fara faɗa wanda ba kasafai zaka ganshi yana yi ba, nayi wuff na wuce ɗakin mu, ina shiga na wuce chan ɗakin ummie na, kwanciya nayi na faɗa tunanin yadda al'amura suka juye, yanzu abun da habiba ta mun akwai adalci kuwa? Shin zan iya yafe mata har mu sake komawa kaman da? Shin idan tayi auren zan iya zuwa gidanta? Duk irin waƴan nan habiba batayi tunanin faruwar su ba, kawai hankalinta kwance taji ta so abun da yake sona? Tashi nayi na zauna, wayata na jawo nayi blocking number Aliyu na kuma goge number, bayan na share duk wasu massege ɗin shi, sannan na tafi whatsapp na sake blocking ɗin shi na kuma goge massege ɗin shi, don dama a yawancin lokuta bani ke reply ba habiba ce, shiru nayi ina tunanin yadda rayuwa zata miƙe tsakanina da habiba kawai nakeyi, a haka naji shigowan ummie nah, hannunta riƙe da na hafsy da taketa huci, bayan ta kuma yayah mohd da yayah Ahmad ne.

Wuri suka samu dukkan su suka zauna, ummi zama tayi akan gadon tana riƙo hannu na, yayah mohd ma a gefenta ya zauna yana riƙo hannun hafsy, shi kuma yayah Ahmad kujeran dake ɗakin 3sitter ya zauna akai shima idon shi akaina, wani abu naji da ban taɓa ji ba na rauni a lokacin da yayah mohd yace mun, "Ayshaa akwai gaskiya a maganan da kuka faɗa ke da habiba a wurin Abbah? Don gaskiya ni nakasa gasgata maganan, don nasan babu yadda za'ayi ku iya tunanin shiryah haka a tsakanin ku ba tare da kinyi shawara da ummie ba, don kwanaki B<ntu ta fara mun wani zancen da bangane ba sai na da katar da ita, amma yanzu ina son sanin gaskiyan maganan"?
Faɗawa jikin ummie na kawai nayi ina jin duk dauriya na ya ƙare, ina jin babu abinda nake so irin nayi kuka, kukan ne nake tunanin zai saka na samu sauƙi, domin ni dai bawai shaƙuwa nayi da Aliyu ba ballantana nace ina son shi da hankali na zai tashi ba, amma abunda habiba ta mun shiyake bani tsoro da sakani cikin damuwa, yanzu da ace ina son shi haka zata rufe ido babu kunya babu tsoro ta so shi? Kenan habiba zata iya son mijin da nake aure ma idan yayi mata tayi, kuka nakeyi sosai ummie tana rarrashina.

"kiyi haƙuri ayshaan ummie, komai insha Allahu zai wuce, kuma mijinki special zai zo", cewar yaya Ahmad, wanda tashi yayi zai fita don shi wani iri ne da baya son ganin abun da zai tayar mana da hankali, bayi da dauriyan yayah mohd, kuma shi sanyin shi da haƙurin shi dama yafi na kowa, yana miƙewa yace, "ummie don Allah ku kwantar mata da hankali, ni zanje gidan Aunty Rakiya mu gaisa, zan koma leƙa wurin su M.G ɗa A.G, don munyi waya suna gari,"  zuciyata ce naji lokaci ɗaya ta yanke saboda jin sunan fararen abokan shi masu kama da larabawan nan daya ambata, bansan lokacin dana ɗago da ido na ina kallon shi ba, matsowa yayi kusa dani yace, "ko akwai abinda kike so ne na sayo miki"?

Hannu na miƙa mishi ya riƙe, muryah na yana rawa nace, "yayah ni waya nake so ka chanja mun", murmushi yayi yace "angama my sister, zaki ga waya mai kyau insha Allahu", ya faɗa yana mun murmushi, a haka na sake mishi hannu ya juya ya fita, "wariyar launin fata, gaskiya kowa yafi son Addah Ayshaa akaina a gidan nan, yanzu fah kuka akasamu inayi amma babu wanda ya damu dani, amma ita kowa hankalinshi yana kanta, yaushe ma aka saya musu wayan amma don nuna so da sakalci har wani za'a sake mata wani, nidai bana son natan da za'a chanja mata nima sabo za'a saya mun ba kunce ba", hafsy ta faɗa tana turo baki gaba tana harara na, "tashi ki fita uwar rashin kunya, dama akwai wanda yace miki za'a saya miki waya ne yanzu? Fita kije ki ɗaura mun abinci" ummie ta faɗa tana nuna mata hanyar waje, haka ta miƙe tana Addah idan nagama don Allah ki bani akwalar wayar ki nayi game, nidai miƙa mata wayan nayi ban dube ta ba, ta juyo ummi ta wafce wayan tana, "rabu da ita sai ta gama aikin, idan kin bata wayan Game zata tsaya yi har abincin ya ƙone ko kuma tayi dare,
Bayan fitan tane yayah mohd ya dawo da duban shi kaina, ganin haka na bashi amsa da "wallahi yayah ni bansan duk abunda tace ba, kawai dai na bita a hakane don kar hankali Abbah ya tashi, kuma naga babu amfani tunda yaƙini ya koma mata na ƙaryata, don ni dai bazan sake kula shi ba tunda ya koma mata, akan ayi biyu babu gara itan suyi", na ƙarasa hawaye yana bin fuskana, riƙe hannu ummie tayi ta jawoni jikinta tana, "kiyi haƙuri insha Allahu zakiga alkhairin haƙurin da kikayi, ki barta da shi Allah zai kawo miki naki rabon, amma don Allah yanzu bana son wannan sakewa ki bar saurayi da ƙawa ko ƴar'uwa, duba da yadda rayuwar yanzun ya koma, amana yayi ƙaranci, ni dama tun lokacin da kika nuna mun bai kwanta miki ba sai na ƙara dagewa da addu'an neman alkhairi akai, kuma ko a yanzu ina ji a raina babu alkhairi a ciki shiyasa duk hakan ya faru", ummi tana rufe bakinta naji wani kuka yazo mun, Allah sarki uwa, gaskiya duk wanda ya rasa uwa dole ya koka *Aunty nice* domin ita wani abu ne na daban, nifa babu wani addu'a da nakeyi akan al'amarin amma kiji ita kuma tana mun, Allah sarki ummie nah, riƙo ta nayi sosai nace, "ummie amma duk da haka sai habiba ta so mutumin da yake sona? Kenan zata iya son mijin da nake aure ma kenan? Ummi ciwon ɗa nakeji a zuciyata bawai na rabuwa da shi bane, ina jin ciwon abun da ƴar'uwata da nafi so ta mun ne, yanzu dole danganta kar mu yaja baya" na faɗa ina share hawayen ido na, "babu komai sis insha Allahu tsakanin ku zai dai-dai ta, ke ae zuciyar ki mai kyau ce, kuma nasan zaki yafewa ƴar uwaki ki mata uzuri, insha Allah komai zai wuce" yayah mohd ya faɗa, sannan ya chanja topic ɗin, suka koma maganan haihuwar Aunty Bintu, inda yake gayawa ummie wai maiduguri take son zuwa haihuwa, amma shi gaskiya baya son hakan, itama ummie ta goyi bayan maganan shi akan gara ta haihu a ɗakin ta  don babu abunda zai gagara.


Tunda ga ranan da abun ya faru mamie ta samu abun habaici, babu garin Allah da zai fito ya faɗi bakaji ta tana surutun masu rashin farin jini ba, a haka Aunty Rakiya watarana ta shigo ta samu hakan na faruwa, ae ko ta sille mamie tass, harta habiba bata bari ba, don hajiya ummah ta gaya mata yanzu an hana habiba zuwa side ɗinta, ni kaɗai nake zuwa kwana a chan, aeko aka bar mamie da kame-kame tana bata haƙuri, tass ta zage habiba tana gaya mata indai cin amana da halin uwarta take so ta ɗauko wlh zata sha wahala, kuka habiba ta dinga yi, bayan mamah da Aunty Rakiya sun haɗu sun watse su, zuwa dare ina kwance a ɗakin mu na side ɗin ummah sai ga habiba ta shigo, yadda bata yi sallama ba ta shigo nima sai ban ɗaga kaina na dube ta ba, nidai ina riƙe da wayana muna chatting da jammy, haƙuri kullum take bani akan dukkan su basuji daɗin abinda ya faru ba, don mummy tayi rantsuwa ita dai babu yawun ta acikin maganan auren, don tun ranan tace babu jituwa tsakanin shi da mummy, shima Aliyun tace duk jikin shi yanzu a sanyaye yake, nidai ban tofah komai ba akai, don ummie nah taja mun kunne sosai akan al'amarin, saboda haka sai na chanja topic, na tambayeta yaushe zata fara karatunta? Tace sai bayan ta haihu,, so tanaga zai kai next year, haka mukayi sallama, ina kallon habiba ta gefen idon na tagama duk abinda zatayi na shirin kwanciya bata kulani ba, nima ganin hakan sai na rabu da ita, nayi shirin kwanciya na nima na kwanta.

Washe gari bayan mun idar da sallah na juya na kalleta nace, "sisto an tashi lpy"? A razane ta juyo ta kalle ni, amma abun mamaki sai bata iya ta amsa mun ba, kawai dai naga idon ta ya wani ciko da hawaye, ganin haka sai na koma kan gado na kwanta, na juya mata baya, ban farka ba sai wurin ƙarfe 8:00 shima hafsy ne ta shigo ta tashe ni, akan naje ummie tana nema na, dubawa gefen habiba nayi naga babu ita babu alaman ta, maida kallo na nayi kan hafsy nace, "da kika shigo kinga sisto ne?"  tsaki tayi ta fita a ɗakin tana faɗin " ke kika san wata sisto, ni dai naga habiba ta wuce side ɗinsu tun wurin 6:30am, idan zaki yiwa kanki faɗan ta nutsu gara ma kiyi", ta wuce tayi hanyar waje.


*AUNTY NICE*