An yanke wa wani ɗan dambe hukuncin rataya bayan ya kashe matarsa

An yanke wa wani ɗan dambe hukuncin rataya bayan ya kashe matarsa
 

Wata babbar kotu a jihar Adamawa da ke Najeriya, ta yanke wa wani dan damben gargajiya hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda ya kashe matarsa.

 
Thank-You Grim, fitaccen dan damben gargajiya ya fito ne daga yankin Silli a karamar hukumar Guyuk a jihar.
 
Jaridar Leadership ta rswaito cewa da yake yanke hukuncin mai shari'a Nathan Musa, ya ce masu shigar da kara sun gamsar da kotun cewa Grim ya aikata laifin don haka kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
 
Masu shigar da karar sun ce sai da mutumin da ake karar ya jefo matar kasa kafin ya yi amfani da tabarya ya doka mata aka abin da ya janyo mutuwarta a 2018.
 
Ma'auratan dama ba sa tare tun a farkon shekarar saboda sabanin da suka samu.
 
Kuma lamarin ya auku ne bayan da matar da samu wani da za ta aura a nan ne ta nemi takardar saki daga wajen tsohon mijin nata.
 
Amma maimakon ya aika mata takardar, sai ya gayyace ta gidansa a kan ta je ta karbi takardar sakin, ko da ta je sai ya nemi su sasanta amma ta ki.
 
Anan ne kuma rikici ya kaure tsakaninsu sai duka ya biyo baya daga nan kuma sai ya rarumo tabarya ya kwada mata a kanta.