An Samu Raguwar Aikata Fyaɗe Da Cin Zarafin Jinsi A Kano-- CITAD
Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al'umma CITAD ta ce duk da cewa ana samun jinkirin mayar da martani ga iyayen wadanda aka ci zarafi sakamakon nuna ƙyamar da al'umma ke yi da kuma rashin aiwatar da hukunci daga hukumomi, an samu raguwar aikata cin zarafin jinsi musamman Mata a cikin watanni uku a Kano,
CITAD ta ce an samu a cikin watan Satumba da Disamba an samu cin zarafin jinsi guda 61.
Jami'ar kula da jinsi ta cibiyar Zainab Aminu ce ta bayyana hakan, ya yin taron manema labarai da cibiyar ta kira a ranar Alhamis da ta gabata, a cewar Zainab Aminu an sami raguwar ayyukan cin zarafin jinci a watan Nuwamba idan aka kwatanta da watan Satumba da Oktoba na wannan shekarar, ta kara da cewa " mun lura cewa an samu raguwar fyade, cin zarafi na kafafen yada labarai da batanci da tursasawar Jima'i ta fuskar don haka muke kira da gwamanti da ta yi kokarin tabbatar da dokar nan ta cin zarafin kananan yara da za ta basu kariya"
Ta kuma ce duk da cigaban da aka samu wajen rage cin zarafi tsakanin jinci akwai bukatar gwamnati ta dauki tsauraran matakai domin kawo karshen matsalar,
Ya kara da cewa bai kamata al'umma su zuba wa gwamnati ido ita kadai ba, akwai bukatar kowa ya bada gudunmawa don kawo karshen cin zarafi a cikin al'umma
" Dolen dole sai iyaye da ƴan uwa sun fito sun hada kai da gwamnati da ragowar ƙungiyoyin da suke ya ƙi da cin zarafin mata domin a yi kokari a yaƙi cin zarafin mata domin mu kadai ba za mu iya ba, ita ma jiha ita kadai ba za ta iya ba, dole sai mun hada gwiwa mun hada kai domin mu ƴaki wannan al'amari" a cewar Zainab,
Sannan Cibiyar ta bukaci sarakunan gargajiya da malaman addini akan su hada kai da hukumomi wajen ɗakile cin zarafi a jihar Kano ba ki daya.
managarciya