An sake  Sace sama da mutum 17 a Sakkwato 

An sake  Sace sama da mutum 17 a Sakkwato 
An sake  Sace sama da mutum 17 a Sakkwato 

An wayi garin yau Laraba a garin Gatawa da mummanan labari domin barayi sun shiga garin Gatawa an sace sama da mutum 17 a garin dake cikin karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato.
Wata majiya ta sanar da Aminiya  hakan ta ce   daga cikin mutanen da aka sace an dauki Yahayan Tali, an je gidan dogon naira an tafi da iyalansa, haka sun tafi gidan kanen Hamza ciwo, abubuwa marar daɗi sun marar sun faru a garin.
"An ce mana ana aiki amma barayin nan suna yin yanda suka ga dama, an dauke mana layin sadarwa ba mu gaisawa da kowa a waje ga barayi na yi mana yanda suke so, ko yaushe matsalar nan karuwa take yi kusan soja 20 aka yi wa sallah a satin da ya wuce."
"Bayan sun shiga garin Gangara suka yi wa garin kacakaca ba mu san wannan tsarin da ake nufi ba ta'addanci na karuwa."
Tabbatar da faruwar lamarin dan majalisa mai wakiltar Sabon Birni ta Gabas Sa'idu Ibrahim ya ce Maharan suna neman jami'an tsaro a yankin
Suna neman sansanin jami'an tsaron ne tun bayan da suka samu karsashi bayan harin da suka kai garin Dama in da aka kashe sojoji da 'yan sanda da sibil defens.

Ya ce suna kai harin a wuraren da sojoji da 'yan sanda da sauran jami'an suke zaune.

Ya kara da cewar sun kai hari a garin Gangara da Gatawa tun bayan da suka kashe jami'an tsaro.