An Rufe Makarantun Boko A Birnin Abuja Don Kaucewa Harin ‘Yan Bindiga
Babban birnin tarayyar Najeriya na Abuja na fuskantar barazanar tsaro a halin yanzu, ‘yan ta’adda na shirin kai wasu munanan hare-hare. Rahoto na musamman da Daily Nigerian ta fitar a ranar Talata, 26 ga watan Yuli 2022 ya nuna ISWAP, Boko Haram da ‘yan bindiga su na shirya ta’adi a birnin na Abuja.
Miyagun za suyi yunkurin aukawa makarantar koyon aikin lauya da ke Bwari, sannan za su iya kai hare-hare a wuraren da ake ibada a Abuja.
Jaridar ta ce bayanin da aka samu ya nuna ‘yan ta’addan za su iya aukawa wurin aikin jami’an tsaro. Wannan ya biyo bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai a gidan gyaran hali da ke Kuje, suka yi nasarar kubutar da mutane sama da 600 da aka garkame.
Wata majiya ta shaidawa jaridar yaran Kachalla Ali Kawaje da Kachalla Dansadi suna neman yadda za su sace mutane daga makarantar lauyoyi.
Jami’an tsaro sun samu labari ‘Yan bindigan na kokarin shiga makarantar koyon aikin shari’an da nufin garkuwa da dalibai, malamai da ma’aikata.
Dan Bindiga Kawaje da mayakansa sun gagara a dajin Kuyambana da ya ratsa Zamfara, Kebbi, Kaduna da Neja. Yaransa ne suka harbo jirgin saman sojoji kwanaki.
Gwamnati ta bayar da sanarwar rufe makarantun boko a birnin Abuja daga gobe Laraba don kaucewa harin ‘yan bindigar da suke yi wa Abuja ga zaman lafiyar da an ka santa da shi.
managarciya