An Kwantar Da Dan Siyasa Asibiti Bayan Ya Sha Gurbatattun Ruwa Don Ya Burge Talakawa
An kwantar da dan siyasa a asibiti bayan ya sha gurbattacen ruwa don birge talakawa ya nuna masu shi da su daya ne.
Babban ministan Punjab na kasar Indiya, Bhagwant Mann, yana kwance a asibiti a wahalce bayan ya sha gurbataccen ruwa daga wani kogi domin tabbatarwa da jama'a cewa ruwan tsaftatacce ne.
A wani bidiyo, an ga Mann ya debi ruwan a kofin gilas daga kogin kuma da kwankwade shi yayin da magoya bayansa suke masa ihu da yabo.
Bayan nan ne ruwan suka tambaye shi domin sun shiga in da ba muhallinsu ba, nan take aka garzaya da shi assibiti.
Wannan salon yaudara na ‘yan siyasa haka suke a kasashe masu tasowa wurin yin kememe su nuna komi na tafiya yanda yakamata ba tare da kowace matsala ba.
managarciya