A ƙalla jami’an tsaron Nijeriya 11 ‘yan bindiga suka kashe a wani kwantan ɓauna suka yi masu a Giron Masa a ƙaramar hukumar Shanga jihar Kebbi.
Harin an yi shi ne a ranar Talata da dare da ya gabata in da jami’an suke sintiri a yanki.
Jami’an soja sun yi ƙoƙarin kare yankin aka yi masu kwantan ɓauna.
Sojoji da ‘yan sanda sun rasa rayukkansu da manyan motocin yaƙi guda biyu aka ƙona.
Gwamnan Kebbi Nasir Idris ya ziyarci wurin da kuma asibitin koyarwa ta gwamnatin tarayya dake birnin kebbi domin duba lafiyar waɗanda suka jikkata.
Gwamnan ya yi tir da rashin hankalin ya kuma ba da tabbacin gwamnati za ta kula da mutanen da suka samu rauni.






