An kama matar da ake zargi da kai wa Bello Turji makamai daji a Zamfara
Bataliyar rundunar sojin Najeriya mai yaƙi da yan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya da ake kira da Operation Fansar Yamma, ta samu nasarar cafke wata mata mai shekaru 25 da haihuwa dauke da alburusai 764 da kuma bindigogi guda shida, da ake zargin za ta kai sansanin madugun ƴan fashin dajin nan Bello urji
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar laftanal kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce an kama matar ne a ranar 28 ga watan Disamban 2024 da ake ciki, tare da wani abokin tafiyarta a yankin Badarawa da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Kamen dai ya biyo bayan wani rahoton sirri da aka samu game da safarar makaman ƴan bindigar a kan hanyar Kware zuwa Badarawa a karamar hukumar ta Shinkafi.
Bayan samun waɗannan bayanai ne dakarun rundunar ta Operation Fansar Yamma suka kafa wani shingen bincike wanda ya kai ga cafke wadanda ake zargin.
managarciya