An Kalubalanci Tambuwal Kan Yafi Kowa Cancanta A Zaɓen 2023

An Kalubalanci Tambuwal Kan Yafi Kowa Cancanta A Zaɓen 2023

Tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Sakkwato Honarabul Malami Muhammad Galadanchi wanda aka fi sani da Bajare ya ƙalubalanci Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal kan kalamansa na yafi dukkan 'yan takarar shugaban kasa da suka nuna sha'awarsu ta tsayawa zaɓe a 2023.

Honarabul Malami Bajare a zantawarsa da Managarciya ya ce Tambuwal ya so kansa da yawa a wannan maganar da ya yi domin akwai waɗanda suka fi shi cancanta a cikin dukkan manyan jam'iyyun biyun na siyasa APC da PDP, ta la'akari da yadda ya riƙe Sakkwato shekara bakwai ba wani abin a zo a gani.

 
"Tambuwal ya manta a wannan shekarar ya kasa biyan kuɗin jarabawar kammala sikandare da 'yan asalin Sakkwato suka rubuta, 12 ga Fabarairun nan za a yi jarabawar JAMB kuma duk wanda bai da sakamako a hannu bai zana ta, wanda yake wasa da makomar 'ya'yan talakawa dake son shiga jami'a shi ne yafi cancanta kan wasu.
"Sanata Wamakko a lokacin da yake gwamna ya samar da manyan makarantun gaba da sikandare ciki har da  makarantar koyon aikin unguwar zoma a garin Tambuwal da tsarin gina ta a mataki uku ya kammala mataki na farko a cikin wata 9, shi da ya zo ya mayar da ita kwalejin kiyon lafiya, a cikin shekara bakwai bai a ɗaura ko bulo ɗaya ba," a cewar Bajare.
 
Bajare ya ce yanda tattalin arzikin jiha da tsaronta suka samu ci baya kamata ya yi Tambuwal ya fara tunanin yin  wani abin a zo a gani a ɗan lokacin da ya rage masa ba wai ya koma wurin gwada tsayi da waɗanda suka fi shi kawo cigaba a jihojinsu lokuttan da suke riƙe da gwamnati.
"kowa ya san Tambuwal ya kafa tarihi kan rashin biyan kudin jarawabawar kammala sikandaren yara, ina kira gare shi da ya gaggauta shafe wannan tarihi a sauran lokacin da ya rage masa na mulki," in ji shi.