An hanunta mutane 11 da suka kubuta a hannun masu garkuwa ga mataimakin gwamnan Sakkwato 

An hanunta mutane 11 da suka kubuta a hannun masu garkuwa ga mataimakin gwamnan Sakkwato 
Mutane 11 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a kauyen Jaibaba mazabar Turba a karamar hukumar Isa sun samu 'yanci.
Jami'an tsaro dake aiki a dajin Zurmi dake Zamfara ne suka kubutar da su mace 7 da jarirai 3 da karamin yaro daya.
A lokacin da yake karbar mutanen mataimakin gwamnan Sakkwato Alhaji Idris Mohammad Gobir ya jinjinawa kokarin jami'an tsaro kan aikin da suka yi abin yabawa ne.
Alhaji Gobir ya sake jaddada kudirin gwamnatin Sakkwato kan magance matsalar tsaro.
Ya ce Gwamnatin Ahmad Aliyu ba ta taba wasa da harkar tsaro ba duk abin da ya taso na tsaro za a yi shi nan take.
Mataimakin gwamna ya ba da sanarwar tallafi dubu 100 da buhun gero da masara ga kowane daya daga cikin wadan da suka kubuta don su koma gida cikin farinciki.
Shugaban karamar hukumar Isa Alhaji Sharifu Abubakar Kamarawa ya godewa gwamnatin jiha ga karimcin da ta yi wa mutanen.
Ya ce wannan tallafin ya nuna yanda gwamnati ta damu da halin tsaro da walwalar jama'a.