An hana malaman Musulunci yin wa'azi sakamakon sukar juna
Hukumomin lardin Sindh na Pakistan sun haramta wa malaman addinin Musulunci fiye da 140 yin wa'azi har na tsawo wata biyu.
Hukumomin sun ce sun ɗauki matakin ne don kauce wa ɓarkewar rikici, sakamakon sukar juna da malaman ke yi musamman cikin watan Muharram wanda shi ne wata na farko a shekarar musulunci.
Pakistan ƙasa ce da mabiya mazhabar sunna suka fi yawa, kuma ƙasar ta sha fuskantar rikici tsakanin ɓangarorin addini a cikin watan Muharram, inda ake yawan sukar mabiya mazhabar Shi'a marasa rinjaye a ƙasar.
Wani jami'in gwamnatin ƙasar ya ce dokar ta haramta wa malaman tafiye-tafiye da yin wa'azi har na tsawon wata biyu don hana sukar mazhabobin juna.
Haka kuma gwamnatin lardin ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da wasu shafukan sada zumunta a kawanaki 10 na farkon watan.
managarciya