Daga Comrade Musa Garba Augie.
Kungiyar Plan International da ke zaman kanta a Najeriya, ta fitar da wani rahoton da ke nuna cewa akalla yara 1,409 aka yi garkuwa da su daga makarantun fadin kasar a shekara ta 2020, kuma cikin wannan adadi ɗalibai 16 sun rasu ko 'yan bindiga sun hallaka su.
Kungiyar ta ce yayinda aka bude makarantu firamare da sakandare a sassan Najeriya, akwai ɗalibai da dama da suka gaggara komawa makaranta saboda fargabar tsaro da garkuwa.
Ta yi kira ga gwamnatin Tarayya ta ɗau matakan da suka dace domin kawo karshen matsalar garkuwa da ɗalibai da tabbatar da cewa samun ilimi bai kasance cikin barazana ba, yayinda Najeriya ke shirin karbar nauyin taron ilimi kan tsaron dalibai a wannan watan.
Kungiyar ta yi wannan kiran ne a jiya a wani bangare na bikin cika Najeriya shekara 61 da samun 'yan ci.