An gurfanar da tsohon minista gaban kotu kan zargin yin lalata
Tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Kabiru Turaki (SAN), ya gurfana a gaban Kotun Majistare da ke shiyya ta biyu a Abuja, kan zarge-zarge da su ka shafi yin aure na karya da lalata da kuma wasu laifukan.
Sai dai kuma Turaki ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi lokacin da aka karanta takardar tuhumarsa a ranar Alhamis a gaban Mai Shari’a na Kotun Majistare ta Tara, Abubakar Jega.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa tsohon ministan ya bayyana cewa zarge-zargen da ake masa ba gaskiya ba ne.
A cewar takardar tuhuma, ana zargin tsohon ministan da aikata “yaudarar wata ta yarda cewa akwai aure na halal, yin lalata wanda ya saba wa sashe na 383, 387, da 389 na Kundin Laifuka.”
Masu gabatar da kara sun bayyana cewa binciken zargin ya biyo bayan wata takardar korafi da aka rubuta a ranar 9 ga watan Agusta, 2024, wacce aka mikawa Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda.
Haka kuma, sun ce bincike ya nuna cewa “kai Barrister Kabiru Taminu Turaki (SAN), tsakanin Disamba 2014 da Agusta 2016, ka yi zaman aure na karya tare da Ms. Hadiza Musa Bafta a wani otel mai suna Han’s Place.
“Ka kuma yi zaman tare da ita a Ideal Home Holiday, Asokoro, tsakanin Agusta 2016 da Nuwamba 2021.
“Ka kama mata wurin zama a No. 12, Clement Akpagbo Close, Gauzape daga Nuwamba 2021 kuma ka rudar da ita cewa ka aureta, har ka ci gaba da kwanciya da ita, wanda ya haifar da haihuwar wata yarinya.
“Ka bar Hadiza Musa Baffa tare da ɗiyarta ka kuma ƙi amincewa da cewa kai ne mahaifin yarinyar. Ka yi barazanar amfani da tasirin ka da matsayinka don kashe mahaifiya da yarinyar.
“Saboda haka, ana zargin ka da aikata wadannan laifuka.”
managarciya