Makomar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf na ƙara shiga duhu yayin da jagoransa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ke ci gaba da jan ƙafa kan jam’iyyar da zai koma — APC ko ADC. Rahotanni sun nuna cewa Kwankwaso bai gamsu da tsauraran sharuɗɗan APC ba, duk da tayin sassauci daga ADC.
Binciken Idon Mikiya ya tabbatar da cewa ganawar da Gwamna Yusuf ya yi da Shugaba Bola Tinubu ba ta haifar da wata matsaya ba. An ce shugaban ya buƙaci a fara warware saɓanin da ke tsakanin Yusuf da Kwankwaso kafin a yanke hukunci gaba ɗaya.
APC dai na kallon Kwankwaso a matsayin “babban ganima”, ba gwamnan ba. Daga cikin sharuɗɗan jam’iyyar akwai rashin ba Gwamna Yusuf tikitin tazarce kai tsaye a 2027, da kuma ƙin amincewa ya naɗa mutanensa a muƙaman jiha da tarayya.
Kwankwaso ya fito fili a Kano yana nuna rashin amincewa da APC, yana zargin jam’iyyar da karya alƙawura a baya. Ya ce ba zai shiga APC “a makance ba” sai an ba shi tabbacin makomar gwamnatinsa, ‘yan majalisa da magoya bayansa.
A APC Kano kuwa, manyan jiga-jigai sun nuna cewa amincewa da buƙatun Kwankwaso zai lalata tsarin jam’iyyar. Sanata Barau Jibrin da Abdullahi Ganduje na jagorantar manyan bangarori biyu, kuma kowanne na kare muradunsa gabanin 2027.






