An Bukaci Tambuwal Da Gyara Hanyar Mota A Gudu Da Ruwa Suka Lalata

An Bukaci Tambuwal Da Gyara Hanyar Mota A Gudu Da Ruwa Suka Lalata

 

Shugaban karamar hukumar Gudu Honarabul Bello Wakili Bachaka ya roki gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri  Tambuwal ya gyara masu hanyarsu da ta hada karamar hukumarsu da garin Tangaza wadda ruwan sama suka lalata a shekarar data gabata.

Shugaban karamar hukumar a lokacin da yake hira da manema labarai a garin Balle a rangadin da suka kai yankin ranar Alhamis data gabata ya ce akwai bukatar gwamnati ta bude masu sabuwar makarantar Sikandare da aka gina a yankin domin soma karatun 'ya'yansu.
Ya ce aikin babba ne dake da muhimmanci a gare su bai kamata a kyale shi, ba a fara cin amfaninsa ba, tsawon shekara uku da kammala aikin matsalar tsaro hana buda makarantar ya kamata a bude domin lamarin ya yi sauki a yankin.
Bachaka ya ce bayan hanyar mota da suke son gwamnati ta gyara masu har da karamin Dam da aka samar domin shi ne yake faccewa ruwan sama idan sun zo su mamaye titi sai ka ga lamarin ya zama matsala.
Ya godewa Tambuwal yanda yake kula da lamarin kananan hukumomi a jihar Sakkwato a kwanan baya ya ba su wasu kudi wanda suka gudanar da aiyukkan a dukkan mazabun karamar hukumar Gudu.