An bankaɗo yadda matar shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ta wawure sama da Biliyan 20 a Kano

An bankaɗo yadda matar shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ta wawure sama da Biliyan 20 a Kano

An baɲkaɗò yadda matar shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta wąwurê kuɗi sama da biliyaɲ 20 a asusun gwamnatiɲ Kano, kamar yadda  Ɗan Bello ya fitar da bayani.

Idan baku manta ba Dan Bello ya nemi APC a Kano da ta bashi haƙuri ko ya cigaba da fallasa irin satar da suka aikata, inda kuma suka gagara yin haka.

A cewar sa matar Ganduje Hajiya Hafsat Ganduje lokacin da suke kan mulki kai tsaye ake tura kudi a asusun bankunan ta da ta buɗe har guda 44, adadin ƙananan hukumnin Kano.

Ta rinka sanya ana tura miliyoyin kuɗi ba tare da ɓoye-ɓoye ba, a ƙarshe an gano kamfanin tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomin Kano Murtala Sule Garo ne ke fitar dasu.

Yanzu haka ana zargin ta da sace kuɗi sama da biliyan 20, daga asusun Gwamnatin jihar Kano.