An Bankaɗo Batun Kuɗaɗen Shiga a Jihar Sakkwato: Haƙiƙanin Yadda Alƙalumman Suke
Saɓanin abinda ke tafiya a yanzu, a lokacin gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal, sai da jahar Sokoto ta kai mataki na 17 a tsarin jahohi 36 dake Najeria ta fannin wadda tayi fice a ɓangaren samar da kuɗin shiga na cikin gida. In da a shekara ta 2021 da kuma 2022 aka tara kuɗin shiga kimanin naira biliyan 23.6. kuma wannan bayanin yana nan a rubuce ba shaci faɗi ba ne.

Marubuci Dr. Basit Yusuf Alkali (Masani kuma dan kishin ƙasa)
Kamar dai yadda mai magana da yawun Gwamnan Jihar Sakkwato Abubakar Bawa, ya fitar da takardar da aka rabawa manema labarai in da ya bayyana a cikin takardar cewa Gwamnatin da ta gabata a ƙarƙashin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal wai ba ta tabuka komai ba wajen ganin harkokin tattara kudin shiga sun inganta a Jihar.
A matsayi na masani kuma ɗan kishin kasa zanyi duba tare da yin tsokaci kan wannan bayani da maimagana da yawun gwanna ya fitar tare da duba yanayin tsarin tattara kuɗin shiga na gwannatin da ta gabata ƙarƙashin jagoranci RT. HON. Aminu Waziri Tambuwal.
A cikin takardar da aka rabawa manema labarai kamar yadda mai magana da yawun Gwamna Ahmed Aliyu Sakkwato ya fitar yana mai cewa ya ciro wannan bayanin ne a cikin bayanin da Gwamnan ya gabatar a wajen wani taron shekara- shekara na masu ruwa da tsaki a kan harkokin batutuwan haraji da cibiyar masana kan batun tattara kudin shiga wato (Chartered Institute of Taxation of Nigeria in Abuja). ta gudanar.
A cikin abin da aka gabatar a wajen taron, Gwamnan ya bayyana cewa Gwamnatinsa ta tarar da yanayi marar daɗi game da batun tattara kuɗin haraji da ke tattare da rashin gaskiya a harkar tattara wa da kuma yin amfani da kudin harajin cikin gida da ake tarawa a Jihar.
Yana mai bayanin cewa ya ɗaga darajar batun karɓar haraji a Jihar Sakkwato, daga batun; karɓar harajin a kowane watanni uku da ake samun naira biliyan 2.6 zuwa naira biliyan 3.8 a cikin watanni uku na shekarar 2024.
Haƙiƙa kamar yadda muka Sani kuma a bayanai na hakikanin gaskiya wannan magana ta saba wa gaskiya, kamar mutum mai matsayi irin na Gwamna ya dubi abokan aikinsa da kuma muhimman mutane masu ruwa da tsaki a kan batun tattara harajin cikin gida ya kuma saki baki ya riƙa fadin magana mai kama da zuƙi ta malle da ta saɓawa sahihan bayanan dake akwai a ƙasa.
A abin da ke akwai na haƙiƙa, a watan Fabrairu na shekarar 2017 Gwamnatin da ta gabata ƙarƙashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal sai da ta rushe hukumar gudanarwar tara kuɗin harajin cikin gida ta Jihar Sakkwato ta kuma maye gurbinta da wani ƙwaƙƙwaran kwamitin riƙo da aka ba su umarnin lallai su daga darajar batun karɓar harajin, su kuma tabbatar sun rufe tare da datse dukkan wuraren da ake amfani da su wajen zurarewar kuɗin harajin da gwamnati ya dace ta samu su kuma yi dukkan abin da ya dace domin ganin an inganta lamarin karɓar haraji a Jihar da zai dace da yanayin karɓa da tara haraji a cikin Najeriya da duniya baki ɗaya ke amfani da shi wajen karɓar haraji.
Ta hanyar yin amfani da hanyoyin daƙile dukkan hanyoyin da za a iya yin amfani da su wajen zurarewar kuɗin haraji ba bisa ƙa'ida ba, kwamitin ya samu nasarar ɗaga daraja da martabar hanyoyin karɓar kuɗin harajin Jihar daga naira biliyan 4.5 a shekarar 2016 zuwa sama da naira biliyan 9 a ƙarshen shekarar 2017, Kamar yadda hukumar haɗin Gwiwa domin karɓar kuɗin harajin suka bayyana.
Kuma kamar yadda kowa ya Sani domin ƙara inganta yanayin karɓar haraji a Jihar, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi ƙoƙarin canza Fasalin hukumar karɓar harajin musamman ta hanyar samar da doka da ta samar da sabuwar hukumar karbar haraji, wadda Gwamnatin jihar ce ta samar da dokar ta kuma aikewa majalisa inda majalisar dokokin Jihar ta amince da ita a shekarar 2019, sakamakon haka aka rushe batun karɓar haraji da hannu a waɗansu hukumomi waɗanda a can baya ba’a ma san da su ba wajen biyan harajin da ya dace su bayar.
Sabuwar dokar ta samar da yadda za a naɗa sabon shugaban hukumar karɓar harajin tare da daraktocin da za su ja ragamar hukumar. Tun daga wannan lokacin aka samu ingantacciyar hukumar da ta dace da yanayi na ƙasa da duniya baki ɗaya wajen batun karɓar haraji.
Haƙiƙa ya dace Gwamna Ahmed Aliyu ya shaidawa mahalarta taron da suka taho daga wurare daban –daban abin da suka fi son ji, wato abin da Gwamnatinsa take yi domin bunƙasa harkokin karɓar harajin cikin gida a Jihar Sakkwato, ba wai ƙin bayyana nasarar da Gwamnan da ya gada ya samu ba.
A zance na gaskiya dukkan mutanen da suka saurare shi a wajen wannan taron, a matsayinsu na masana suna da hanyoyin tantance bayanan nasa waɗanda ba gaskiya a cikinsu. Kuma hakan ya kasance rashin adalci da yawo da hankalin masana, kalaman da bai dace a ce sun fito daga bakin mutum mai matsayi irin na Gwamna ba, ya riƙa yin kalaman kushe na rashin gaskiya ga wata Gwamnati ba tare da ya bayyana gaskiyar inda aka aikata rashin gaskiyar ba.
Bari mu yi amfani da wannan dama domin bayyana irin kalamai na ƙage da zuƙi ta malle da suka fito daga bakin Gwanna a wurin wannan taro, ta hanyar yin bayanin irin yadda hukumar karɓar haraji a ƙarƙashin Aminu Waziri Tambuwal ta ɗaga darajar tsarin karbar haraji daga naira biliyan 9 a shekarar 2017, zuwa naira biliyan 18 a shekarar 2018, sai kuma naira biliyan 19 a shekarar 2020, amma saboda batun matsalar cutar Mashaƙo waton ( Covid - 19) duk da hakan a shekarar 2021 an samu nasarar ɗaga bataun karbar harajin zuwa naira biliyan 23 a shekara ta 2021 kuma da shekarar 2022.
Alƙalumman a bayyane suke cewa a ƙoƙarin ganin an sake Fasalin hukumar karɓar harajin cikin gida ta Jihar Salkwato, Tambuwal ya amince da a ɗauki waɗanda suka cancanta aiki ‘yan asalin Jihar da suka kammala karatun jami'a, a ƙalla mutum ɗaya daga kowace ƙaramar hukuma 23 dake Jiha, kuma an baiwa mata aƙalla kashi 30 wanda kuma an aikata hakan ta hanyar yin jarabawa domin kowa ya samu cike gurbin da aka ba shi, wanda bayan jarabawa an yi intabiyu ga duk wanda za’a ɗauka kamar dai yadda dokar ɗaukar aiki ta tanadar, an kuma bayar da ingantaccen horon sanin makamar aiki ga waɗanda suka yi nasarar samun aikin haɗi da mayyan jami’an hukumar da nufin kowa ya san irin abin da ke gabansa na aikin da zai yi a hukumar.
Kwamitin da ya jagoranci ɗaukar ma'aikatan na ƙarƙashin jagorancin Umar B Ahmad Tambuwal wanda shi ne babban akanta Janar na yanzu ƙarƙashin Gwamnatin Ahmed Aliyu.
Sai dai kuma abin takaici Umar Ahmed Tambuwal. Wanda shi ne shugaban kwamitin da ya gudanar da wancan aikin a lokacin gwannatin Aminu Waziri Tambuwal shi ne a yanzu aka zargi da ɗora Gwanna Ahmed Aliyu bisa keken ɓera ta hanyar zayyana masa irin wadancan kalaman da suka karkatar da shi har ya riƙa faɗin jawaban ƙarya a kan irin rawar da Gwannatin baya ta taka a kan harkar karɓar harajin cikin gida.
Dokar da Aminu Waziri Tambuwal ya kafa a lokacin ta kuma bayar da dama ga hukumar karɓar harajin ta karɓi haraji a madadin ƙananan hukumomi 23 a kuma miƙa masu ainihin abin da aka karba, amma hukumar ta karɓi kashi biyar na ladar aikin karɓar harajin da ta yi a madadin ƙananan hukumomin. A ƙarƙashin dokar an bayar da cikakkiyar dama ga hukumar ta cire dukkan waɗansu abubuwan da ka iya zama matsaloli ga yanayin aikin gwamnati.
Abin baƙin ciki kuma a nan shi ne Gwannatin Ahmed Aliyu duk da ta san wannan amma sai ta mayar da hannun agogo baya inda dokar ta zama ba ta da wani karsashi wanda hakan ya dagula aikin hukumar karɓar harajin baki ɗaya. Sai kawai ta koma tamkar wani mutum ne ke jan akalar hukumar wajen karɓa da aikin hukumar, ba tare da yin la'akari da tanadin da dokar hukumar ta yi ba.
Haƙiƙa ga duk wanda ya yi duba da kyau zai tabbatarwa da kansa cewa yanayin yadda hukumar karɓar harajin cikin gida ta Jihar Sakkwato take ciki bashi da kyau sam, idan aka yi la’akari da inda aka fito a lokacin gwannatin da ta shuɗe ta Aminu Waziri Tambuwal, domin kuwa a halin yanzu ana yin amfani har da karɓar tsabar kuɗi a hannu da sunan haraji a madadin tsarin da hukumar ke da shi tun da aka yi wa hukumar sahihin gyara a lokacin mulkin Aminu Waziri Tambuwal da nufin samun damar karɓa da tattara harajin tare da bin doka da dukkan ƙa'idar da dokar ta tanadar wanda hakan na haifarwa Jihar nasarorin da ba su da iyaka.
Babban abin da za a yi la'akari da shi a Jihar Sakkwato shi ne irin yadda Gwamnatin baya ta inganta yanayi da aikin hukumar karɓar harajin ta yadda aka yi wa hukumar Maida tsohuwa yarinya kuma ta zama ta zamani da ke gudanar da ayyukanta dai dai da zamani da ƙa'idojin duniya bayan da aka samar wa hukumar katafaren ofishi a gidan zuba jari na Jihar Sakkwato. Wanda ya kasance matsugunnin da ake amfani da shi sakamakon yadda matsugunnin din- din - din na hukumar ake kan aikin gina shi da nufin samar da wuri mai kyakkyawan yanayin aiki da ya dace, amma Gwamna Ahmed Aliyu ya yi watsi da aikin.
Sauran kuma ayyukan ci gaban Jihar da aka ƙirƙira wanda Gwamnatin da ta gabata ta yi, shi ne irin yadda aka samu gano waɗansu sababbin dabarun ingata su da a halin yanzu ke fuskantar shiga halin rushewa sun haɗa da:
Batun Samar da Albasa:- Kasancewar Jihar Sakkwato ce wadda ta fi kowace Jihar samar da albasa a Najeriya har ma da nahiyar Afirka, saboda akwai alƙalumman ƙididdiga da suka nuna ana samar da albasa da ke bayar da maƙudan kuɗi na naira biliyan ɗari biyu da Hamsin(250b) a shekara. Wanda sakamakon hakan ake yin aikin haɗin Gwiwa wajen karɓar harajin da suka haɗa da jiha da ƙananan hukumomi da ƙungiyoyi tare da sarakunan gargajiya ake kuma raba kuɗin harajin da aka samu kamar haka Gwamnatin Jiha kashi Arba'in (40), kashi 30 ƙaramar hukuma, kashi 20 ƙungiya, sai kaso 10 na masarautun gargajiya.
Baburan haya da ake kiransu da Kabu - Kabu da kuma Babura masu kafa uku: Nan ma yadda ake ƙarbar harajin su a kullum shi ne Kabu - Kabu da Babura masu ƙafa uku an samar da yadda ake ƙarbar harajin ne sakamakon tsarin da Gwamnatin Jiha ta yi da ƙungiyoyin su da kuma raba abin da aka samu kamar haka, kashi Sittin (60) zuwa ga Gwannatin jiha, sai kashi Arba'in (40) na ƙungiyoyin, an kuma samar da yadda ake karɓar kudin ta hanyar yin amfani da na'urar POS domin karɓar wannan harajin.
Kaɓar harajin Manyan makarantu da kuma sauran makarantu a Jihar Sakkwato:- dukkan kuɗin harajin da aka karɓa daga waɗannan wuraren ana Sanya su ne a cikin asusun ajiya na Banki zuwa ga wani asusun ajiyar da aka samar domin hakan, nan ma ana raba kuɗin ne kamar haka kashi Tamanin (80) na komawa ne ga makarantun sai kuma ana riƙe kashi Ashirin (20) a matsayin harajin Gwamnati. Haƙiƙa hakan ya kara bunƙasa irin yadda ake karɓar harajin makarantu da kuma na Jihar Sakkwato.
Waɗannan tsare - tsare masu inganci da tsohuwar Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta fito da su ya samar da ci gaban karɓar harajin naira biliyan 24 a shekara, a shekarar 2021 da kuma shekarar 2022 wanda idan aka yi lisaafi mai saukin ganewa za a gane cewa a duk watanni uku ana samun naira biliyan shidda (6) ba wai biliya biyu 2.6 ba a wata uku kamar yadda rahotannin Gwamna Ahmed Aliyu suka bayyana a wurin taron na Abuja.
Idan aka yi la'akari da alƙalumman, ta yaya za a ce harajin cikin gida na naira biliyan 3.8 a watanni uku a shekarar 2024 za a yi la'akari da shi a matsayin cigaba, a karkashin Gwamnatin Ahmed Aliyu?
In ma haka ne, ya kamata Gwamna Ahmed Aliyu ya fito fili yayi bayanin gaskiya a game da harajin da gwamnatinsa ta tara. Madadin kawai a riƙa shaci faɗin alƙalumma haka kawai, ya dace ya kawo wa masu sauraren sa sahihan alƙalumma da za su tabbatar da abin da yake faɗi, saboda batun kuɗin haraji ba siyasa ba ce kawai da ake iya yin shaci faɗi, abubuwa ne da suke a rubuce kuma suke buƙatar ƙwaƙƙwarar hujja.
Hakika gaskiyar lamari a nan shi ne Gwamnan Sakkwato na yanzu yana kallon batun maganar haraji a matsayin wani abu da ake gani a baibai a madadin yadda lamarin yake a haƙiƙanin gaskiya. Abin da ya kamata ya yi tun da farko shi ne ya tambayi shugabanni wato jagororin hukumar karɓar haraji ta Jihar Sakkwato, duk da abin da ke faruwa a fakaice a halin yanzu ya saɓawa ainihin yadda dokar hukumar harajin jihar ta ke, da ta yi bayanin yadda komai yake dalla dalla.
Saɓanin abinda ke tafiya a yanzu, a lokacin gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal, sai da jahar Sokoto ta kai mataki na 17 a tsarin jahohi 36 dake Najeria ta fannin wadda tayi fice a ɓangaren samar da kuɗin shiga na cikin gida. In da a shekara ta 2021 da kuma 2022 aka tara kuɗin shiga kimanin naira biliyan 23.6. kuma wannan bayanin yana nan a rubuce ba shaci faɗi ba ne.
Batun ayyana samun nasara a fannin tara kuɗin shiga na cikin gida batu ne dake buƙatar bayar da sahihan bayanai da alƙalumma ba wai shaci faɗi ba, A saboda haka idan Gwamna Ahmed Aliyu na son yin bugun gaba a wannan fannin kamata ya yi ya bayyana alƙalumma ba wai shafa labarin shuni ba.
Dr. Basit Yusuf Alkali
Unguwar Sama Road a Sakkwato Birnin Shehu.