Home Manyan Labaru Amurka ta dakatar da bada biza ga ‘yan Najeriya da wasu ƙasashe...

Amurka ta dakatar da bada biza ga ‘yan Najeriya da wasu ƙasashe 74

6
0

Amurka ta dakatar da bada biza ga ‘yan Najeriya da wasu ƙasashe 74

Gwamnatin Amurka ta dakatar da bayar da biza ga ‘yan ƙasashe 75, ciki har da Najeriya, lamarin da ya jefa masu neman biza cikin rashin tabbas.

Matakin, wanda ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta dauka, na daga cikin bitar hanyoyin tantance bakin haure, musamman tsaurara aiwatar da dokar “public charge”.

Dakatarwar ta shafi biza iri-iri, na bakin haure da waɗanda ba bakin haure ba, ciki har da na ziyara, karatu, aiki da haɗuwar iyali.

An umurci ofishin jakadancin Amurka a ƙasashen da abin ya shafa da su dakatar da bayar da biza na yau da kullum, ba tare da bayyana lokacin da za a dawo da bayarwa ba.

Ana sa ran matakin zai yi tasiri sosai ga ‘yan Najeriya, musamman dalibai, ‘yan kasuwa da iyalan da ke jiran biza.

Har yanzu ofishin Jakadancin Amurka a Abuja da karamin ofis ɗin na Legas ba su fitar da wata sanarwa kan yadda za a aiwatar da dakatarwar a cikin gida ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here