Amfanin Kitso ga 'ya mace

Amfanin Kitso ga 'ya mace

 

   Amfanin kitso ga mace: amfanin kitso ga mace ya na da yawa, har yanzu al’adar nan ta aikawa neman yardar makitsiya da samun lokacin yin kitson ta na nan. Magidanta mafi yawan su na baiwa kitson matan su muhimmanci, bayar da  kudin kitso na daga cikin abinda mace ke gane kaunar da mijin ta ya ke yi mata. Daga cikin amfanin kitso ga mace sun hada;

  1. i)                   Tsabta, kitso na  sa  mace ta zama cikin tsabta domin za ta zama cikin kamshin man da aka yi kitson da shi ba tare da wani warin kai ba.
  2. ii)                  Gyara kai, mace za ta samu gashin kanta zai yi tsawo da laushi kuma goshin ta zai fita sosai da sharpdin shi (da yawa maza na son ganin goshin mace ya fita sosai)

iii)               Qara kyau, za ta za ma  kyaun halittar ta ya fita sosai, wannan ke sa da yawa mata idan suka yi kitso za ki tarar ba su cika daura dan kwali ba idan su na a cikin gida, musamman in ya na sabo, domin jan hankalin mazajen su.

  1. iv)              Karadankon so ga mazaje, kitso na kara sa kauna ga mata daga wurin mazajen su (akwai sirri sosai a cikin wannan)

Me rashin yin kitso ke sanyawa ga mata; da zarar mace ba ta kitso ai daga nan matsala ta fara, gashin kai na daga cikin sassan jiki masu bayyana wari ga mutum, musamman mata (ki lura ko samarin yanzu masu tara sumar nan sosai, ai za ki ga kowane lokaci cikin gyaran ta su ke yi) to, ina ga mace. Rashin yin kitso na haddasa matsaloli kamar haka;

  1. i)                  Kyama daga mai gida, domin wannan na kawo bayyanar warin kai.
  2. ii)                 Lalacewar kai, kamar tsinkewar gashi, amosanin kai, kurarraje da sauransu.

Tsawon lokacin da ya kamata ayi kitso: ya zama tsakanin kwana goma zuwa sati biyu, in son samu ne kar ya wuce haka.

  Yadda ya kamata mace ta tanadi kitson ta: wanke kai bayan an kwance kitso na daga cikin abin da ke sa gashi ya lalace, ya zama ko da an yi kitson ba zai kwanta sosai  ba, ko ya ki kyau. Kamata ya yi kwana uku kamin ranar kitso, ki wanke kanki sosai da sabulu ko man wankin gashi a cikin wadannan kwanakin uku. A ranar kitson, bayan wanke kitson sai ki shafa mai sosai da sauran sanyin wanke kan, bayan ya bushe sosai sai ki kwance kitson tare da tsefi gashin sosai kamin ki je gidan kitso. To, ina tabbatar miki, idan ki ka yi haka za ki ga kitson ya fita sosai ya yi kyau.

    Me ke sa mata son yin kitson Sallah: Duk Bahaushiyar mace na son yin kitso domin bukin sallah, kin san lokaci ne na kawa da nuna sutura, watakila shi ya sanya ake karin maganar cewa “Ba’a neman mata ranar sallah” domin kowace mace ta yi kawa. In kin duba ai ko mabiya sauran addinai na baiwa kitso muhimmancin gaske, misali lokacin kirsimeti za ki ga kowace mace na son ganin sai ta yi kitso fiye da komai.

    Kitso sana’a ne ko sha’awa ne: ‘gaskiya kitso sana’a ne a wuri na, domin ni dai na yi duk ‘yan abubawa da nike son in yi da kitso. Za ki san mutane daban-daban, kama daga ‘yan mata da ma’aurata da ma’aikatan gwamnati kai har da wadan da ba ki yi tsammani ba. Idan kuma ba ki yi hankali ba akwai ‘yan matsaloli domin za ki hadu da matsalolin mata daban-daban, wani lokaci zai kasance kishiyoyi biyu ko sama da haka duk a wurin ki suke kitso, matukar ba ki yi hankali ba akwai kura, domin kowace za ta zo miki da na ta sirri.’ A tabakin wata makitsiya.

     Ta yaya ake koyon kitso: To, gaskiya ban tunanin ana koyon kitso, ni, dai a fahimta ta wannan baiwa ce daga Allah, ban taba ganin an aje da wasu da sunan ana koya masu kitso ba, ko ace ga wani lokaci da aka kiba domin koyon sa. Abin da na sani yawan kallon yadda ake yi zai kara sa ki kware, domin za ki  ga nau’o’in kitson daban-daban.

    A wajen gyaran gashi na zamani watu (saloon) akan dau lokaci mace na ganin yadda ake wanke gashi da sanya shi bushewa kamin ayi kitson kawai.

    A yini mace nawa ake iya yiwa kitso: ya danganta daga wane iri kitso za’a yi ko ya yawan gashin wacce za’a yiwa kitson. Misali idan amarya ce, dole kitson zai dau lokaci domin dole a fito da ita sosai.

   Matsaloli: ba za a rasa ‘yan matsaloli a harakar kitso ba, kamar yadda na fada a sama ya na da kyau, a jiye sirrin kowa daban. Duk wacce ki ka rika kanta sai ta zo maki da na ta magana ko dai don neman shawara ko don gulmar abokiyar zaman ta ko wata fira ta daban. Yana da wuya ba’a samu wannan ba. Abu na biyu, kasancewar halin da muke ciki a yanzu na bazuwar cuta a cikin al’umma, mafi yawan masu zuwa kitso sun fi son zuwa da tsinke da matajen(comb) kan su, domin kiyayewa da amfani da na wani (Allah Ya karemu).