Ambaliyar ruwa: Mutane 41 sun rasu a Nijar
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 41 a daminar bana.
Ambaliyar na faruwa ne sanadiyyar ruwan sama mai ƙarfi da ake samu a wasu sassan ƙasar.
BBC Hausa ta rawaito cewa rahoton da ofishin kare haƙiƙin jama'a na ƙasar ya fitar ya nuna cewar wasu daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu sun nutse ne a kogi ko rafuka yayin da wasu kuma gine-gine ne suka danne su.
Rahoton ya kuma ƙara da cewa yankin Tahoua ne ya fi fama da matsalar inda mutum 15 suka rasa rayukansu.
Sai Maradi inda mutum 11 suka mutu, yayin da mutum shidda suka rasa rayukansu a yankin Zinder.
Tuni dai hukumomin kasar suka dauki matakai na taimaka wa waɗanda suka shiga mummunan hali sanadiyyar ambaliyar.
Latsa hoton da ke ƙasa don sauraron rahoto kan ambaliyar ruwa a Nijar.
managarciya