Ambaliyar Ruwa: Gidauniyar Matawalle Orphan ta tallafa wa mutum 300 a Gasma
Daga Muhammad Maitela, Damaturu.
Gidauniyar 'Matawalle Orphan' a karkashin dan Majalisa mai wakiltar karamar hukumar Karasuwa a jihar Yobe, Hon. Adamu Dala Dogo (Matawallen Nguru), ta tallafa wa magidanta 300 wadanda ibtila'in ambaliyar ruwa ya shafa a garin Gasma da ke karamar hukumar, ranar Asabar.
Sa'ilin da yake kaddamar da bayar da tallafin ga al'ummar garin, Manajan Daraktan Gidauniyar Matawalle Orphan, Mohammed Musa Gasma ya ce kimanin mutum 300 ne suka ci gajiyar tallafin kudin. Inda ya kara da cewa, "Wadanda gidajen su ya rushe baki daya mun tallafa musu da 10,000, yayin da wadanda gidajensu rabi ko kuma ambaliyar ta shafi wani bangare na gidajensu mun taimaka musu da gudummar 5000."
"Sannan kamar yadda muka saba, ayyukan wannan gidauniyar ya shafi taimaka wa marayu ne da maras galihu a cikin al'umma. Wanda idan mun lura jama'ar wannan yanki sun fuskanci kalubalen ambaliyar ruwan da ya jefa daruruwan mutane cikin tsananin rayuwa, kuma bisa hakan muka ga ya dace mu tallafa musu da dan abin da ba a rasa ba."
Mohammed Musa ya kara da cewa, ta la'akari da gidauniyar su ta yi, wanda ko shakka babu jama'a suna bukatar kowane irin tallafi ne, saboda yadda ambaliyar ruwan ta lalata gidaje da amfanin gonakin jama'a. Ya kara da cewa, "Saboda haka a matsayin mu na gidauniyar da ba ta gwamnati ba, kuma muna da ayyukan jinkai da dama da muke a fannin tallafa wa marayu da masu karamin karfi, shi ne muka ga ya dace mu taimaka wa wadanda suka fuskanci ibtila'in ambaliyar ruwan."
"Abu na biyu- kuma, wadannan ayyukan jinkan suna gudana ne daga aljihun Hon. Adamu Dala Dogo (Matawallen Nguru), kana dan majalisar dokokin jihar Yobe, mai wakiltar karamar hukumar Karasuwa. Ya kafa wannan gidauniyar ne domin taimaka wa marayu da masu karamin karfi a cikin al'umma." In ji shi.
Har wala yau, Shugaban gidauniyar, ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin kudin da cewa su ci gaba da addu'o'in Allah ya kawowa jihar Yobe da Nijeriya baki daya dawamamen zaman lafiya. Haka kuma ya yi wa al'ummar fatan alheri da samun cikakken zarafin sake gina gidajensu tare da mayar da gurbin abubuwan da suka yi asara ta dalilin ambaliyar ruwan.
A hannu guda kuma, wadanda suka samu tallafin; maza da mata sun bayyana matikar godiya tare da yaba wa gidauniyar bisa duba da yanayin da suke ciki da basu tallafin inda suka roki Allah ya saka wa wanda ya assasa gidauniyar da masu gudanar da ita da mafificin alheri.
managarciya