Ambaliya: An Gano Adadin Wadanda Su ka Mutu da Rasa Muhallansu a Jihohin Arewa 3 

Ambaliya: An Gano Adadin Wadanda Su ka Mutu da Rasa Muhallansu a Jihohin Arewa 3 


Gwamnatin tarayya ta ce mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa ya kashe akalla mutane 49 a Arewa maso Gabas.
Haka kuma an samu jihar Arewa maso Yamma ɗaya - Jigawa, da ta fuskanci matsanancin ambaliya a damunar ba. 
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta ce aƙalla mutane 41,344 sun rasa muhallansu. 
Jihohin da iftila'in ya fi shafa a wannan lissafin sun hada da Taraba da Adamawa da ke Arewa maso Gabas, sai Jigawa da ke Arewa maso Yamma. 
Jami'in hulda da jama'a na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ta bayyana cewa yanzu aka fara shiga lokacin ambaliya, musamman a Arewa. Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Manzo Ezekiel a shekarar 2023 ne aka samu ambaliya mafi muni a kasar nan. Channels Television ta wallafa cewa akalla mutane 600 ne su ka mutu, yayin da wasu miliyan 1.4 million su ka rasa gidajensu, an rasa gonaki 440,000 a 2023.
Hukumar bayar da agaji a Jigawa (SEMA) ta ce an rasa kadada 11,560 na gonaki a Jigawa. Shugaban hukumar SEMA a Jigawa, Dr. Haruna Mairiga ya shaidawa Legit cewa an kuma rasa gidaje akalla 7,060. 
Dr. Mairiga ya bayyana fargaba kan karuwar ambaliya ganin cewa har yanzu ana cikin mamakon ruwan sama. 
A baya mun ruwaito cewa ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar rushewar gidaje akalla guda 100 a jihar Jigawa, inda mutane su ka fara neman mafaka.
Hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC ta bayyana cewa su na agazawa wadanda lamarin ya shafa, sannan ana tsare kayansu saboda kar ɓata-gari su yi masu sata.