Amaechi Ya Nuna Fushinsa  Kan Rashin Saurin Aikin Jirgin ƙasan Kaduna Zuwa Kano 

 Amaechi Ya Nuna Fushinsa  Kan Rashin Saurin Aikin Jirgin ƙasan Kaduna Zuwa Kano 

 

Ministan harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi, ya nuna ɓacin ransa ga Kamfanin Fasahar Gine-gine na China, CCECC bisa yadda aikin layin dogo na Kaduna-Kano ya ke tafiyar wahainiya.

 
Amaechi ya baiyana ɓacin ran nasa ne a yayin ziyarar duba yadda aikin ke tafiya da kuma na Tashar Sauke Kayayyaki ta Dala, wato 'Dala Dry Port's tare da wasu masu ruwa da tsaki a jiya Asabar a Kano.
 
A cewar Amaechi, aikin ba ya sauri kwata-kwata, inda ya ƙara da cewa kayan aiki 2000 ya kamata a kawo, amma an ɓuge da kawo guda 541.
 
"Sun ce sun kai kayan aiki sama da 300 a Kaduna kuma an tafi anje a tabbatar. To in ma hakan ne, ya zama 800 kenan idan a ka kwatanta da 2000 da ya kamata a kawo. Sabo da haka akwai matsala," in ji shi.
 
Haka-zalika Ministan ya nuna rashin jin daɗin bisa yadda CCECC ɗin ko fara aikin tashar ma ba su yi ba.
 
Ya ƙara da cewa kamata ya yi a ce CCECC sun yi wa Ma'aikatar sa bayani sabo da an riga an basu wasu da ga cikin kuɗaɗen da za a basu, inda ya ce ya kamata a ce an an fara aiki a wajen.