Alkalin Kotun Zabe Ta Ki Karbar Cin Hanci Ta Kuma Fallasa Wanda Ya Ba Ta

Alkalin Kotun Zabe Ta Ki Karbar Cin Hanci Ta Kuma Fallasa Wanda Ya Ba Ta

Alƙaliyar Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe A Kano Ta Koka Bisa Yunƙurin Wani Babban Lauya Na Bata Cin Hanci.

Shugabar kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta majalisar tarayya da ta dokoki a jihar Kano, Mai shari’a Flora Ngozi Azinge, ta bayyana fushinta kan yunƙurin wani babban Lauya mai muƙamin SAN, na neman ya ba ta cin hanci.
Da ta ke jawabi gabanin fara zaman sauraron ƙararraki a jiya Talata a Kano, Alƙaliyar ta koka kan yadda manyan lauyoyi musamman ke aikata wannan mummunar ɗabi’a.
Ko da ya ke ba ta bayyana sunan babban lauyan ba, Ms Azinge ta ce SAN ɗin da ake magana a kai na da shari’a a gaban kotun.
“Babban Lauyan Nijeriya da ke da shari’a a gabana ya na ƙoƙarin ba ni cin hanci. Tun jiya kuɗi ke yawo a wannan kotun. Duk wanda ya karɓi kuɗi a madadina, Allah zai hukunta shi da shi da zuri’arsa baki ɗaya."
“Suna ci gaba da zagin alkalai, suna zagin mu kullum a cikin jaridu, a kafafen yaɗa labarai – cewa muna karɓar rashawa."
“Bari in sake jaddada muku cewa kada kowa ya sake tunkara ta da cin hanci. Na gamsu da abin da Allah ya ba ni, kuma ina da rufin asiri na.” In ji ta.
Sai dai Eyitayo Fatogun, SAN, wanda ya kasance a gaban kotun, ya tsaya a madadin dukkan lauyoyin da suka halarta, kuma ya buƙaci Alƙaliyar da ta kai ƙorafi ga hukumomin da suka dace.
Domin ƙarfafa hujjar sa, babban lauyan ya ce ya ga inda shari’o’in da ake tuhumar Alƙalan da suka kasa gabatar da ƙararraki na irin wannan ɗabi’a ta cin hanci.