Alamomi 7 da za ku gane ƙoda ta fara samun matsala

Masana harkar lafiya sun bayyana cewar koshin lafiyar koda na daga cikin sirrukan dadewa a duniya ba tare da gajiyawar jiki ba,
Masana harkar lafiya sun bayyana cewar koshin lafiyar ƙoda na daga cikin sirrukan dadewa a duniya ba tare da gajiyawar jiki ba,
Ƙoda na taka muhimmiyar rawa wajen tace wa da cire sinadarai ma su guba daga abubuwan da mutum ya sha. Ƙoda na da alaƙa da sarrafa yanayin jinin jikin ta mutum,
Bisa la'akari da muhimmanci ƙoda a jikin mutum ne yasa muka bunciko muku wasu daga cikin alamomi 7 da ke nuna cewar ƙoda ta samu matsala, kamar yadda masana su ka tabbatar.
1. Kumburi da taruwar ruwa a sassan jiki: Daya daga cikin alamomi na sahun farko da ke nuna cewar ƙoda ta fara samun matsala akwai taruwar ruwa a cikin jiki da kale haifar da kumburi. Sassan jiki da wannan matsala ta fi bayyana su ne; sahun kafa, hannaye, kafafu, ciki, da fuska.
2. Sukurkucewar mafitsara: Yayin da mutun ya fuskanci ba ya iya rike fitsari kamar yadda ya saba a baya, ya gaggauta zuwa asibiti domin gudanar da bincike a kan yanayin aikin ƙodar sa.
3. Gagarumin canji a launin fitsari: Launi, kala, da zarnin fitsari na daga cikin abubuwan da ake amfani da su wajen fahimtar aikin ƙoda.
Idan fitsari yana kumfa ko tsananin zarni ko wari ko mutum ya ke jin zafi yayin fitar fitsari ko ganin jini a fitsari alamu ne da ke nuni cewar aikin ƙoda ba ya tafiya yadda ya kamata.
4. Kuraje a fata: Duk da akwai abubuwa da yawa da kan iya haddasa fitowar kuraje a jikin mutum, gazawar koda wajen tace wasu sinadarai ma su guba kan iya haddasa fesowar kuraje a jiki.
6. Hawan jini: Masana lafiya sun bawa ma su matsalar ƙoda shawarar su ke yawan ziyarar asibiti domin duba yanayin jininsu, saboda ƙoda na taka rawa wajen daidaita sinadaran fatashiyom da sodiyom, sindaran da ke da alhakin da alhakin daidaita yanayin jini a jiki.
7. Yawan gajiya da kasala: Yayin da ƙoda ta fara samun matsala, mutum kan tsinci kansa cikin yawan samun kasalar jiki da gajiya, wasu lokutan mutum har jiri ya kan ji da rashin samun natsuwa.
Lafiya uwar jiki.