ALALAN WAKE DA DOYA
Girki domin inganta zamantakewa a tsakanin ma'aurata, musamman Hausawa a Nijerriya da nahiyar Afirika gaba ɗaya.
BASAKKWACE'Z KITCHEN
Kayan Haɗi:
Wake
Doya
Magi
Manja
Mangyaɗa
Kayan ƙamshi
Albasa
Attarugu
Tafarnuwa
Yanda za ki samar da Alalan:
Dafarko za ki gyara wake ki yanka doya ƴanana ki zuba akai kisa tarugu albasa Tafarnuwa, akai maki nika, idan aka kawo ƙullun seki sa su Maggi gishiri da kayan ƙamshi, kisa Mangyaɗa da Dan Manja, maimakon ruwa dazakisa kiyi kwaɓin sekiyi da ruwan zafi, kitsaidata daidai kaurin ƙullun alale, seki kulla kidafa, karki cika mata wuta ,anfiso adafata ahankali don doyan ya dahu.
08167151176
MRSBASAKKWACE
managarciya