Akwai Yiyuwar PDP Za Ta Kashe Karba-Karba A Wurin Zaben Shugaban Kasa

An samu labarin gwamnonin PDP a yankin Kudu sun tafi gidan Atiku Abubakar a boye domin su yi masa bayanin hujjarsu ta goyon bayan shugaban jam'iya na kasa ya fito daga Arewa.

Akwai Yiyuwar PDP Za Ta Kashe Karba-Karba A Wurin Zaben Shugaban Kasa
Akwai Yiyuwar PDP Za Ta Kashe Karba-Karba A Wurin Zaben Shugaban Kasa

Jam'iyar PDP mai adawa a Nijeriya da alamu ba za ta yi karba-karba a wurin fitar da dan takarar shugaban kasa ba duk da matsayar da kwamitin karba-karba na Gwamna Ugwanyi  ya cimma ta mika shugaban jam'iyya na kasa a Kudu.

Manyan jagorori a PDP sun sanarda jaridar The Nation  cewa fitar da sanarwar ta kwamitin ta tayar da kura a jam'iyar da ke barazana a hadin kan jam'iya.

 Maganar karba-karba za ta sha wuya a zaben 2023 duk kwamitin ya ba da sanarwa karba-karba a tsakanin Arewa da Kudu za ta soma aiki daga watan Okotoban wannan shekara.

Hakan ke nuna mika kujerar shugaban jam'iya na kasa a yankin Arewa, za a mika kujerar shugaban kasa a yankin Kudu bisa ga tsarin babban taron jam'iya kan rabon muamai.

Shugabannin jam'iya sun ce wannan tunani kuskure ne, suna ganin matukar dan takarar shugaban kasa ya zo daga yankin Arewa ana iya karbar mulki hannun APC.

Sun ce Atiku Abubakar, Gwamna Tambuwal da Rabi'u Musa Kwankwaso da Sule Lamido da Bukola Saraki dukkansu daga Arewa suke kuma suna saon yin takarar shugaban kasa, ina za a iya jingine takararsu.

An samu labarin gwamnonin PDP a yankin Kudu sun tafi gidan Atiku Abubakar a boye domin su yi masa bayanin hujjarsu ta goyon bayan shugaban jam'iya na kasa ya fito daga Arewa.

Gwamnonin sun tafi da dare a gidan kuma an ce sun samu fahimta da Atiku.

Akwai bayanin da aka samu cewa masu goyon bayan 'yan takarar shugaban kasa daga Arewa za su yaki wannan matsayar a taron majalisar zartarwar PDP wanda ake sa ran gudanarwa kowane lokaci daga wani  sati mai zuwa.

Bayanai na kara fitowa PDP za ta bar kofar neman takarar shugaban kasa a bude a tsakanin yankin Arewa da Kudu kowa zai iya fitowa ya nema.